page ...44...

168 27 2
                                    


*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...44....

Wajen karfe shabiyu Ahmad ya dawo gidan ba yadda ya saba dawowa ba,dan ya kira wayar maryam yafi a kirga amma bata amsa ba,abin yayi masa ba yanda yasaba ba sam.
Da sauri ya shiga gidan yana zuwa yayi turrruss a bakin kofar falon saboda mungun ganin dayayi arba dashi a bakin kofar.
Mai zai gani maryam ce a kwance cikin jini ko numfashi batayi bare motsi.
Wani uban salati yasaka tareda tsugunnawa a wajen.
Salati yake ta maimaitawa da wani abumma da bakinsa baya tantance mai nene.
Kinkimarta yayi duk da yanda jikinsa yake rawa cikin jarumta yayi hanyar waje da ita.
A bakin kofar fitar mai ganin ya matso da sauri yana tambayar mai ya faru,Ahmad bai amsa masa amma ganin yanda maryam din take yasa yace,
"Shikenan ta kasheta wato,yanzu dam rashin tausayi shine tayi mata haka"
"Mai tayi mata wacece itah"
"D'aya madam din ogah ta shigo dazu da sauri,dana je kaiwa aikan madam din sainaga tarike mata wuyah suna kokuwa,daga baya kuma sainaga tafito da sauri ta bar gidan,kaman akwai abinda ta aikata"
"Sumayyah kake nufi?"
"Eh ba shakkaah ogah ita fah"
Daga haka Ahmad yashiga motar da sauri tareda nufar asibiti mafi kusa
Yana zuwa cikin gaggawa suka karbeta zuwa emergency room,dan tana bukatar taimakon gaggawa.
Kiran wayah yayi yafadawa yah mu'azzam halin da ake ciki,dakuma abinda maigadi yafada masa na abinda sumayyah ta aikata maryam din
Budar bakimsa yace
"Innalillah zata aikata kam,dama biri yayi kama da mutum,taya za'ace wani bayan duk tsiyar datayi da ace wai tasanja,ai hali zanen dutsene baya sanjwa,ai bari kaga yanzu zan dau mataki karka damu "
"Ahah ina nan zuwa,yakamata mufara sanar da abbah abinda ake ciki,kardaga baya ya ji"
Bari yanzu zanzo asibitin,tabbb wannan wace irin zuciya ce da itah,abin harda kisa."
Kashe wayar yayi yana kallon humairah wacce take jijjiga dan ta yana kuka,
"Kinji kuwa koh,waccen yarijyar mai zuciyar arna ta kashe maryam,wai da tsohon ciki ta tureta yanxu haka suna asibiti"
"Lahaulah saka kuwwata,sumayyan ce tayi hak"
Tashi yah mu'azzam yayi cikin bacin rai yafita daga gidan zuwa asibitin,a hanya ya kira yah naseer yake fada masa abinda yafaru,shima ba karamin haushi da takaici abin ya bashi ba.
Ita kuwa humairah yah mu'azzam yana fita ta kira anty Maimuna ta fada mata abinda ake ciki,tana kashewa kuwa ta kira anty nafi ma.
"Hello anty nafi kinji mai yafaru kuwa"
"Mai ya faru, humairah babu ko gaisuwa"
"Hmm wayake ta gaisuwa,yanzu yayanku suke wayah da Ahmad wai yana asibiti,sumayya ta ture maryam akan cikinta,yanzu haka babu tsammanin zata rayu ma nake fadamiki"
"Inna lillah,amma abin da mamaki Anya kuwa hakane zancen"
"Oh karya zan miki,kema dama ai kinsan halinta da kuncin zuciya,dama ta dade tanajin haushin cikin maryam dakuma kulawar da maryma take samu,yanzu haka suna asibiti ana kokarin ceto rayuwarta,ita kuwa sumayyah ba'asan inda take bama"
Kashe wayar anty nafi tayi idonta yana zubar da hawaye,dan bazata iyah cigaba dajin kalmomin ba

"Wayyo sumayyah mai kika aikata haka,keda baki gama samun yardar mutane ba kuma kisake baro wannan danyen aiki"
Duk wannan abin da'akeyi sumayyah batasan da zance ba,tanacan tana kokarin gama yiwa sabin daliban Interview.
Bata ankara ba tana tsaye sai shigowar yan sanda tayi sun tsaya a gabanta,daya daga cikinsu ne ya dauko id card dinsa ya nuna mata tareda cewa,
"Am sorry kece Sumayyah Abudulkadir Gobir?"
"Eh nice mai ya faru?"
"You are under arrest for attempting murder"
"Murder what!? Nidin yaushe a ina "
Babu wanda ya amsa mata sai ma fisgarta dasukayi zuwa cikin mota sai office dinsu.
A gaban shugabannasu aka zaunar da ita da ankwa a hannunta,babu abinda take sai binsu da ido,dan ko kalma daya ta gagara furtawa.
Dago ido yayi ya kalleta cikin rashin tausayi yace,
"Kece Wacce ta yi yunkurin kashe kishuyarta da tsohon ciki koh,wace irin zuciya ce dake,da har zaki aikata hakan iye"
"Wace kishiyar tawa na kashe,bangane mai kuke nufiba,anya kuwa kun kama wanda kuke nema kuwa?"
"Kehhh karki raina mana hankali,gwanda ma ki karb laifinki tun kafin jikinki yayi tsami,kece kika tureta ko bake bace"
"Nibansan wane laifi kuke tuhuma ta da shiba"
"Zakuwa kiyi bayani,dan mijinki da kansa ya bamu damar ladabtaki idan baki fadi gaskiya bah,ku kaita cell har sai ta fadi gaskiya tukunna"
Jan sumayyah sukayi zuwa cikin cell din da karfi sai tambayar su take akan mai tayi.
Tun daga bakin kofar cell din kanajin karar ihunta kan cewa babu abinda tayi amma basu bar dukanta ba,a dole sai ta fadi laifinta.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now