Page...24....

174 17 0
                                    


     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...24....

To kawai sumayyah tace daga haka ta Muhibba ta mika mata riga ta saka suka fita zuwa dakin hajiya mama n.
Duk taku daya a kafar benin sumayyah ji take kaman kayan cikinta zasu zubo,inda ta cije a fatar bakinta na kasa saida ya fashe dan wahala.
Lokacin dasuka zo kasam benin har haki takeyi,kama hannunta Muhibba tayi cikin tausayawa suka shiga dakin hajiyah maman.
A bakin gadon Muhibba ta taimaka mata ta zauna ,dan ma tagyara jikinta sosai yanda bazata batawa hajiyah mama gadonta ba kaman yadda ta bata nata.
Lokacin da suka shigo bata dakin,saidaga baya ne tashigo dauke da kofi a hannunta.
Mikawa sumayyan tayi,saida ta karba kafin taga ashe kunun gyadane wanda akeyiwa abbah,bakin sumayyah har motsi yake takai shi bakinta,sai a sannan ta tuna ashe ta dade rabonta da abinci.
Saida tasha kusan rabin kofin kafin hajiyah mama ta mika mata kwayoyin magani kala kala guda uku,kallonsu take sai a sannan ta tuna ashe maganinta ne da likita yace ta dunga sha,tun sanda aka bata maganin ta ajiyeshi a dakin Muhibba bata sake bi takansa ba,ah she zaiyi mata Rana.
Zubasu tayi a bakinta takara binsa da kunun gyadan dayake hannunta.
Duk abinda take hajiya mama tasaka ta a gaba tana kallonta,Muhibba kuma tana kam kujerar dakin tana kallon abinda yake faruwa.
"Tun yaushe cikinnaki yafara ciwo amma baki fadawa kowa ba,idam ma bazaki fadawa kowa ba meyasa baxaki ajiye maganin a inda zaki gani ba,tunda kinga kece uwar kanki da uban kamki zaki iya kulada kanki batareda wani ya saniba"
"Ahah hajiyah mama wlh bansan ciwon zai kamani ba,ina bacci naki yafara,sannan wayata kuma babu kati,nayi niyyar kiran Muhibba sai naga wayar babu kudi a ciki"
"Meyasa dakika san bakida katin baki fadaminba,ko idan kika fadamin bazan saka miki,yanzu da bamu kulaba haka zaki kasance a yanayin har sai al'amarin ya cakude,da irin lokacin bayane babu Wanda zaije dubaki,saboda ansan halinki ne na koyaushe idan aka miki fada kinyi badaidai ba ki kulle kanki a daki ke daya,dan dai yamzu ansan kin daina hakanne shiyasa nace Muhibba ta duboki.
Bakya cikin ran mutane da dama kaman yanda sauran mutane suke,saboda dama an saba yin komai batareda ke ba,bakya shiga cikin mutane,a ganinki babu abinda suke dashi dazasu miki,abinda nake ta fadamiki kenan.
Yamzu gashi lokacin dakike bukatar shiga cikin mutanen suma sunnuna miki sun sana harkarsu babu ke,na tabbata da Muhibba ce akace kar kowa da ya kulata da tuni dokar ta karye,amma dayake kece babu wanda ya kula,dan dama da babu dokar duk dayane"
Shuru sumayyah tayi tanajin fadan hajiyah mama,ta inda tashiga ba taanan take fita ba har tayi ya isheta,kuma ita kanta tasan gaskiya hajiya maman take fada mata.
Saida tayi fadanta son ranta kafin ta mike zuwa waje da taji muryar drivern su.
Wani abu takarbo a leda tareda bawa Muhibba ta tafasa mata ruwansa.
Sumayyah tana nan zaune a dakin hajiya mama har aka gama tafashen ta karba ta shiga bandaki dashi .
Ta dade a ciki kafin ta leko ta kalli sumayyah wacce take zaune,da alama ciwon ta sauta saboda maganin data sha.
"Saiki shi go bandaki ai "
Tashi sumayyah tayi kaman kwai yafashe mata a ciki tanufi bandakin hajiya maman.
Ruwa tagani a cikin bahon wankan,yayi kala da alama tafashasshshen abinne a ciki.
Tsayawa tayi tai shiru bata motsa ba,ganin kallon da hajiyan take mata ne yasata cire rigar jikinta ta shiga cikin ruwan.
Haka da zafi da komai ta danna ta cikin ruwan har saida yayi sanyi,zubar dsshi tayi tasake hada wani ta zuba ruwan maganin sumayyah takara shiga.
Haka sukayi tayi har sau uku,sumayyah jitake kamna kunkuminta ta dafu da ruwan zafi.
Bayan sun fito din ma wani uban kasko aka kawo mai dauke da garwashi a ciki,wani maganin hajiyah mama tasake barbadawa a cikin kaskon tareda turawa sumayyah gabanta.
Jatayi ta tsugunna akai,saida shima yakare kafin ta tashi.
Saida tagama tukunna hajiyah mama ta mika mata kayanta da Muhibba ta daukomata a dakinta tasaka,ita kuma Muhibba takawomata farfesun kifi.
Jan kwanon tayi gabanta taci iya cinta kafin ta ture,ruwan sanyi ma hajiyah mama hanata sha tayi,saidai ruwan tea mai zafi.
Haka babu yanda zatayi ta karbi tea din tasha.

A haka saida sumayyah tayi kwana uku hajiya mama tana jinyarta a dakinta,dan kwana ma ana suke kwana tareda ita,koyaushe tana cikin hadamata wasu abubuwan ta bata.
Tun dawowar sumayyah gidan bata yi wasu kwanakin farincikiba kaman yamda tayi kwana ukun a dakin hajiya mama,gashi kuma sosai takejin sanji a jikinta na maganin da mahaifiyar ta tayimata.

Bikin yan mu'azzam ya matso sosai,gida ya cika da mutane sai shiri akeyi,dan ranar itayo ake shirin ganin daurin aure idan allah ya kaimu.
Duk shirye shiryen da akeyi wanda sumayyah tafi shiga shine wajen hidimar abinci,dan yanzu allaj ya hada jininta da madafar abinci abinda koda wasa da bai dameta ba,ita kanta mamakin sanjawarta takeyi,har tambayar kanta take shin dama mutum yana sanjawa haka a rayuwarsa.
Kaman yanda yah mu'azzam yafada kuwa yacika alkawarinsa na yimusu dinki itada Muhibba,dan shigowar Muhibba kenan dakin sumayyah suna zaune itada salma,sai tadinsu sukeyi suna dariya.
Wajen sumayyan taje ta zauna tana dariya tareda fitar da kayan tana nunawa mata.
"Anty sumayyah kallifah kayan kigani,dama cewa nayi bazan nuna mikiba sai an gama dinkawa,anty salma style din yayi kyau koh?
Murmushi salma tayi tareda cewa
"Yayi kyau sosai,inaga idan mundawo bikinki ma wata shekarar irinsa zamuyi,dan naji wani zance anayi a wajen su anty nafi"
Rufe fuskarta Muhibba tayi tana dariya,
"Lah lallai kam,ai bazanyi aureba sai anty sumayyah tayi nata tukunna,hankalina bazai kwanta ba idan ina gidan miji ita tana gida"
"Lallai jimin yarinya,har danni saiki fasa aure,to ki bar wannan zancen,aurenki bazai fasuba danni Muhibba,kuma ni ai nayi da farko,ke yakamata yanzu kiyi sai hankali na yafi kwamciya,musamman idan naga kinfi haka kiba kina juyi"
Dukka dariya suka sa,yayinda Muhibba ta dauki kayan tayi waje da gudu kaman wata yarinya karama.
Salma ce takalli sumayyah tareda cewa,
"Ke nina manta ban fadamiki bama,kwanaki kinjini Shiru ko waya,matsala fah aka samu,bakijj zancen aurena shiru ba?"
"Lahh salma gaskiya ban kyauta ba,kumafah yakamata ace na kula,dan tun lokacin dakika fadamin da yanzu anyi auren"
"Hmm kedai bari kawai,waifah saida aka zo daurin aure ashe wai HIV ne dashi,munje anyi gwaji tun sanda kika ganni nan babu matsalar komai,ashe wai wani magani suke sha sai taki nunawa a jikinsu,daga baya idam maganin yasake su shikenan.
Toh fah wancan watan na daurin auren har an fara shirye shirye musamman ma ummah har tayi siyayyar kayan kitchen,sai naga bakuwar lamba,kaman bazan daga ba sai dai na dauka,ashe abokinsa ne yadau lambata ya kirani.
Nan yake fedemin biri har wutsiya kan tabargazar da Brr Isma'il yake shirin yimin.
Inajin bayanin naje na fadawa ummah halin da ake ciki,da farko bamu yadda ba saida ya turomata medical report dinsa muka je har asibitin.
Da farko basu bamu bayanin ba,dan kinsan basa bada bayanin marar lafiyarsu,saida muka shaida musu halin da ake ciki kafin suka amince muka ga report din.
Karki ga kukan danayi sumayyah,dan wlh ina sonsa sosai,ban taba zaton zaimin zagon kasa irin wannan ba,sai gashi nagani a gunsa"
Tunda tafara bawa sumayyah labarin tabude baki a bude tana saurarenta harta gama kafin tasaki wani numfashi da ta rike tun daxu.
"Waii bala'i,wai nikam wannan rayuwar ina zata damune,hmmm da bada yardar iyayenki za'ayi ba da tuni ya aureki ya gogamiki dafi,Allah yasa kemai hankalice da biyayya ba kamar niba salma.
Ainikam nadauki darasin y'ay'a maza dakuma illar sabawa iyaye,dam mutum bakaramim zafa'i sai shiga ba idan ya sabawa Allah da kuma iyayensa,ita kanta sallahr ka Allah ba karba zayyi ba idan iyayenka na fushi dakai,Allah ya taimakeki salma,saida muce allah yakare na gaba kuma"
"Hmm nima haka nace sumayyah,Allah  yakawo nagari kuma,duk ni yanzu tsoron auren ma nakeyi,gani nake kaman irin su mutarine da kuma Isma'il dukka,bayan kuma ba haka bane"
"Ke kenan ma idan kika koma aiki bakida matsala,zaki yi rayuwarki har Allah  yakawomiki wani,nikuwa fah,salma karki ji fargabar datake tattare a cikin raina idan na tuna saura na wata daya iddah ta takare,gsshi munyi da abbah ina gama idddah zan daura aure na bar masa gida,nikuma bansan wazan aura ba salma,dan babu wanda nakeso a raina yanzu,kowane namiji har yayuna kallonsu kawai nakeyi,shiyasa kika ga ko gargajigar auren yah mu'azzam banayi,dan yanda kika san an ciremin son biki da aure kona waye haka nake ji"
"Karki ce sumayyah,Allah zai kawomiki mafita inshaallah,kedai bukata Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya"
Haka su sumayyah da salma suka cigaba da tattaunawarsu,yayinda sukuma yan biki suka cigaba da hidimar bikinsu.
Daga baya fitowa sukayi harabar gidan aka cigaba da yin aiki dasu,har sai yamma likis wajen magriba kafin salma tayiwa sumayyah sallama ta tafi,hajiyah mama harda turare ta bata,dan dama tasansu da sumayyah tun tana secondary.
Har bakin get tarakata ta shiga motarta,saboda harabar gidan ana ta ayyuka yasa salma barin ta a kofar gida.
"Toh salma sai anjima ki gaida ummah,kice mata ina nan zuwa yini idan aka gama biki"
"To shikenan zan fada mata kuwa,dan dazan taho ma saida tace baki bullomana ba"
.,........kuyi manage da wannan,chapter gaba ta biki ce kowa ya sako ankonsa yazo asha bikin yah mu'azzam da amaryarsa AISHA HUMAIRAH.
🤩🤩🤩🤩🤩🤩🤩💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now