🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵
🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......DEDICATED TO MY MOTHER& UNKNOWN OLD WRITER
Wattpad:SAKHNA03
🏵🏵🏵
...23....Shirye shirye ya kankama na bikin yah Mu'azzam,dan yanzu saura bai fi wata ba a rangada aure.
Gidan su sumayyah har an fara cika da mutane na shirim biki,gsshi gidan su yarinyar mai suna Balkisu suma manyan mutanene sosai,saidai akwai dattako.
Rike sumayyah take da mopa tana goge falon bayan takai kwanukan da aka ci abinci kitshen,ladidi tana wankewa.
Dan yanzu tare suke aikin sun tsarashi yanda zasu ji dadin yinsa,tun su fatsima suna dar dar da sumayyah har su ware,jinta suke yanzu a cikin ransu tamkar yar uwarsu,itama kuma yanzu bata danganta kanta da yan gidan,dan yanzu sai ayi abu dayawa a gidann ma bata saniba,koyaushe tana harkar gabanta tareda kokarin rungumar sabuwar rayuwar data tsinci kanta a ciki,dan yanzu ta yadda da zancen inna ramma,dolene tafara karbar kanta ta kuma koyi son kanta da mutunta kanta kafin wani ya sota koya mutunta ta,ta hakane zata samo amsar maganar da iyah tafada mata kan cewa ta inda aka wargaza ta nan ake gyarawa.
Tana cikin mopping din yayinda hankalinta kuma ya tafi wata uwa duniya wajen tunani,tazo daidai bakin kofah tana gogewa sai ji tayi ta bugi mutum a bakin kofar.
Saurin matsawa tayi da baya dan karewa waye ta buge a bakin kofar,gashi tun kafin ta daga kai kamshin tuarensa har yayi mata yawa a hancinta.
Ware do tayi kaman zasu fado ganin mutumin da bata taba tunanin ganinsa a lokacin ba.
Shima kallon cikin idonnata yake babu alamar wani yanayi a cikinsu,duk da akwai yanayin kawai yana kokarin boye sune.
Muhibba ce ta katse kallon da sukeyi lokacin data kira suanan Ahmad din tana sakkowa daga kan beni.
"Yah Ahmad Har ka iso,yanzu fah mukayi waya da yah mu'azzam yacemin zakazo ka karbi sako"
"Eh dama banada nisa daga nan din lokacin da yayimin magana ai,je ki karbomin zan koma shagone"
Daga haka ta gyada kai tareda yin hanyar dakin hajiya mama,gyaran murya yayi bayan Muhibba ta bar wajen tareda nufar kujerar dake falon ya zauna yana jiranta.
Sauke ajiyar zuciya sumayyah tayi tareda gyara earpiece dake kunnenta tacigaba da goge gogenta.
Dayake dama tazo bakin kofa sai ta dauki kayan aikinta takai inda ake ajiyewa.
A hanya ne suka hadu da ladidi ta dauko faro a kan plate da kuma Five alive,tareta sumayyah tayi tareda tambayarta tana dora hannu akan kunkuminta.
"Ina zaki kuma da wannan ruwan a cikin plate"
"Ahmad ne nazo wucewa yace na kawomasa zai sha"
"Bani nan yau aikina ne banaki ba ai,ki koma kawai zan kaimasa"
"To shikenan,amma kina ganin ba matsala"
"Babu komai karki damu ladidi aikina nake,danshi bazan bari wata tayimin ba tunda da lafiyata"
Daga haka sumayyah ta nufi falon da plate din a hannunta,tana zuwa durkusawa tayi ta ajiye akan table din gabansa tareda gaisheshi,abinda batayiba lokacin da ya shigo gidan.
Shiru kawai yayi bai kalleta ba sannan bai amsa mata gaisuwar ba,abin ya tabata hakan yasa ta tashi zata bar wajen.
"Tsaya!! Ki tafi da ruwan dakika kawo bana bukata,sannan kicewa wacce nasa takawomin mai yasa bata kawo ba,....yar aiki nasaka ta kawomin bake ba mai yasa zaki kawomin ruwa,sannan naji labarin kinje wajen su inna kina kalallamesu,to kisani kinayine a banza don aikinki bazai tasiri a kaina ba,dan haka tun wuri gwara ko farfado daga mafarkin dakikeyi"
Zuwa yanzu abinda yake fada yayi mata ciwo,dukkuwa da cewar bata ga laifinsa ba hakan bashi zao hana taji ciwon abunba.
"Batun kawomaka ruwa bazata kawo ruwa ba saboda yau ba aikinta bane nawane,dan haka ba iya kai kadai ba duk wanda yazo gidannan nizan kawomasa ruwa,koda kuwa karene,sannan kana magana da mai aikin gidanne ba yar gidan ba,dan haka batun kawo maka ruwa a cikin aikina yake ba a wani dalilin daban ba.
Yafiya kuma na nema ne a wajenka badan kara dagula rayuwarka,saidan nakara mantawa da rayuwarka,kuma bazan daina rokon kayafemin kura kuraina ba,sannan bazan ji haushinka ba dan kaki yafemin ko ka fadamin maganganu,domin na cancanci hakan a gun duk wanda nabatawa rai a baya,ka fadawa maryam itama ta yafemin abinda nayi mata,duk da nasan ba lallai ka fada mata amma kaji abinda nace"
Zuwa lokacin hawaye ya wanke fuskarta shaff,saboda ta juya masa baya bai kula da halin datake cikiba sai rawar muryata dayaji alamun abin har zuciyarta yake tabawa.
Share hawayen fuskarta tayi tabar wajen batareda ta juyo inda yake ba saboda kar yaga halin datake ciki.
Dakinta ta nufah da sauri tareda fadawa kan gadonta,kukan tadake rikewa ne yadamu damar kwacewa da karfi.
Saida takai kusan miniti talatin tana kuka kafin allah yabata ikon yin shiru,kanta har yafara ciwo.
Tashi tayi takalli madubi ganin yanda fuskarta ta kumbura fulu fulu kaman mai ciwon kumburi.
Tunani yafara akan shin yaushe wannan abin zai wucene ta samu saukin abinda yake damunta,lallai abinda ake cewa hakane,kayi daya ayimaka goma.
Har ta mike zata tashi saikuma taji kasan cikinta yadanyi suka kadan,dafa wajen tayi yayinda maganar abinda yafaru da ita matsala ya dawo cikin kanta.
Komawa kan gadon tayi ta kwanta kawai maimaikon fitar da take shirin yi.

YOU ARE READING
KAICO NAH
ActionShin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bare na fada musu cewa duniya tayimin zafi..........?😓😓😓 Ina ganin na fita a wannan chakwakiyar ashe...