Page ...51...

143 4 0
                                    

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

       

  🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵

  ..............*KAICO NAH*.............

 Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵

...51....




Hasken ranane ya haska cikin dakin da safe,wanda hakanne yasa Ahmad dole murtsike baccin safen ya tashi.

Ya dan dade bai sauka daga kan gadonba yana kallon saman dakin,da alama abinda ya faru tsakaninsu shida sumayyah yake tunawa.

Fitowa yayi daga dakin yana leka kitchen jin yadda Gidan ya dauki kamshin abinci.

Bayanta yake gani tana aiki ko kula dashi batayiba,har saida ya karisa inda take ya leka abinda take ta gefen wuyanta tukunna.

"Mekike dafawane da safennan uhm"

"Abinda zamu saka a cikinmu mana,ko bazaka ci ba kai irinna nada"

Dariya yayi tareda mitsininta a gefen ciki,

"Na isa ma,a bayama tsiyace kawai,amma inason dandanawa"

Tare suka karisa abincin suka kawo dining din.

"Idan kingama zamuje ki dauko kayanki a gida,duj da nasan ma bakya bukatarsu wani yanzu,

Sannan akwai abinda nake son fada miki,barina je daki na dawo"

Wata waya karama a yadauko a dakin,inda ya sakawa sumayyah abinda yake ciki bayan sun gama cin abincin.

Zaro ido tayi idonta na zubar da jawaye jin maganar da maryam takeyiwa Ahmad lokacin dazata bar duniya,shuru tayi tana sauraron amanar da maryam din ta bata har ta gama,

"Allah ya sarki maryam,wlh nina yafemiki abinda kikayimin,kece ma nake farinciki danaji kin yafemin,dan ki kuwa ko bake kika hafeshi ba zan rike,koba dan Ahmad bane ni mai rike dankine bare nima da nane,zan daukeshi tamkar da na,wannan alkawari nayi inshaallah"

Ahmad ne yafara rarrashinta yana bata baki,ganin yanda tasaka abin a zuciyarta,

"Ahmad mufara bi tagidan su maryam mudauko abeeh tukunna"

"Sumayyah tun yanzu zamu daukoshi"

"Yanzu yaakamata mu daukoshi,so nake nayi rainonsa tunda ga kankanta,kaman yanda maryam ke son na bashi tarbiyyata inaso na fara daga yanxu,mu daukoshi na shirya karabarsa"

Rungumeta Ahmad yayi tareda zuba mata kalmomin dashi kansa baya tantancesu,dariyah tayi tareda kankameshi tana fadin alllah ya barmu tare.

Shiryawa sukayi cikin kaya masu kyau gwanin sha'awa,gidan su maryam din suka fara shiga,dayake da hantsine tana zaune tana bawa abeeh din madara.

Maraba tayi musu tareda basu wajen zama,nan aka danyi hira kafin sumayyah tace,

"Mama dama munzo tafiyane da abeeh idan bazaki damu ba"

Jugum tayi tareda cewa,

"Wai sumayyah anya kuwa baiyi kankanta ba,kar a doramiki wahala fah"

"Babu wahala mama,nice nace zan daukeshi,inason cika burin mahaifiyarsa ne naya tashi a wajena,inason na reneshi daga yanzu ,dan ma banananne da tun yana jinjiri zan karbeshi.

KAICO NAHWhere stories live. Discover now