Page......18......

174 15 0
                                    

   🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...18....

Kukansu suka cigaba da sha yaya da kanwar babu wanda ya samu kwarin gwiwar tunkararsu bare ya hanasu,yaya mu'azzam ne ya shigo gidan,tun daga bakin kofa yayi turus ganin abinda yake faruwa,karisawa wajensu yayi tareda janye Muhibba daga jikin sumayyah,ganin hakanne yasa sumayyah sake rungume yar uwartata da ake shirin rabasu,koda a baya basu wani yi shiri ba amma kuma jini daya da kuma kwana da tashi is something else.
"Wai menene yake faruwane,su sunata kuka ku kuma kun tsaya kuna kallonsu,wanine ya mutu,sannan itakuma wannan mai take a gidannan yanzu?"
Duk tambayar dayake yi yana yinta ne yana kallon hajiya mama wacce itama tunda ta fito daga dakinta kallone nata,dan bata ce komai ba.
Maida idonsa yayi kan sumayyah wacce take durkushe,dan yasan koda wani zai san mai yake faruwa to bazai kaita sani ba.
"Ke bakyajin ina magana ne,me kikeyi anan gidan yanxu?"
Bude baki sumayyah tayi zata yiwa yah mu'azzam magana,saidai babu abinda yafito daga bskinnata face wani kukan wanda yafi na da karfi.
Ganin hakan da salma tayine yasa tafara basu labarin abinda yake faruwa kafin ta kara dacewa,
"Yasaketa Saki uku,shiyasa kuka ganmu a yanzu na rakota gida,sannan baban abin takaicin shine yayi mata lahani sanadiyyar zubar mata da ciki da yayi da kwayoyi masu matukar karfi,sanann kuma wanann cikin ma ta kasa haihuwa da kanta,inda tayi ta nakuda har na kwana uku ba aka kaita asibiti ba,Hakanne yasa dan cikin jikinta ya mutu har yakara affected din mahaifarta,yanzu dai suj bada magugunna sannan sun ce dole saidia ta hakuri da sanjin dazata gani,kuma daukar ciki a gareta nan gaba babban hadari ne"
"Cikin wadin ake magana akai,waye ya samu matsala?"
Shine maganar da sukaji daga bakin kofa wanda hakan yasa salma yin shiru da bayanin da takeyi.
Abbane ya kariso cikin gidan wanda dawowarsa kenan daga dakin baki yayi bako.
Idonsa ne ya sauka akan sumayyah wacce take durkushe a inda take,annurin fuskarsa ne yafara sanjawa zuwa bakin ciki lokaci daya,nuna sumayyah yayi da hannu kafin yaka fara magana cikin bacin rai,
"Me wannan baiwar allah take yi a cikin gidana,mai ya kawota inda nake?"
Kowa tsitt yayi yasha jinin jikinsa babu mai cewa kala.
"Ba magana nake miki ba bazaki amsa minba,idan bakinki ciwo yake kin zama kurma to ki kalli hannuna da abinda zan nuna miki,ina nufin ki tashi ki barmin gida yan zunnan banason sake kara idona na ganki a cikin gidana,dunta gidan badake muka hada gumi mukayi shi ba,gidanane sai wanda naga dama yazauna a cikinsa,ke kuwa na dade da haramta miki takashi"
Duk maganar dayake cikin daga murya yakeyi tareda nunawa sumayyah hanyar waje.
Ita kuma hakan da yayi ne yasake kara volume din kukanta tareda saka jikinta karkarwa kaman an dorata akan spring.
"Abba.........na rokeka ka yafemin abinda na aikata,tabbas naga darasi a rayuwata sosai,sanann Allah kadai yasan halin dana shiga a dalilin bijiremaka,kayi hakuri abba dama dukkan sauran yan uwana,dan Allah ku yafemin,idan har ban samu yafiyarku rayuwar duniya da shakar numfashi ma zai kin wahala a rayuwar nan"
"Wannan daga baya kenan,sanda nace karkiyi kika toshe kunnuwanki kika sakawa kanki kunnen kashi kikayi abinda yafi miki baki tuna da wanann ranar zatazo ba,sai yanzu data zo zaki saukar dakai ki nuna nadamarki,daman nasan wanann ranar zata zo,kuma ina mai fadamiki bakiga komai ba indai wanann duniyar ce da abinda yake cikinta,dan haka tun kafin raina yafi haka baci ki tashi ki bar gidannan ki bacemin da gani yanzunnan"
Cikin rawar jiki da karfin hali sumayya da yunkura ta mike jikinta yana rawa harda fatar bakinta,kallon idon hajiya mama tayi wacce idonta ya ciko da kwallah saura kiris take jira ta zubo,,ganin sumayyah tana kallonta tareda san gano mai yake cikin zuciyarta ne yasata saurin juyawa ta daina kallon mai yake faruwa.
Tafiya sumayyah ta fara harta karisa inda abba yake tsaye,tsugunnawa tayi tareda kankame gwiwonsa,duk da rashin karfin jikinta da kuma azabar ciwon dayake addabarta,hakan bai kai kwatan kwacin abinda takeji ba lokacin da furucin korata daga gidan yake fita daga bakin mahaifinnata ba.
"Abba kayimin rai narokeka dan rahamar allah,koda ba a matsayin yar ka ba ka kalleni a matsayin baiwar Allah da take neman taimako a gareka,abba bazan takura da sai ka yafemin ba amma ka taimakeni da inda zan zauna,dan banida wani wajen zuwa a duniyar nan dayawuce nan,hakika nasan na zakunci kaina iya zalunci wanda hakan yasa bazanga lafin duk wanda ya nuna kyamarsa a gareni ba,dan a yanxu nikaina kyamar kaina nakeyi"
A zuciye abba ya ture sumayyah wacce take rike da kafafuwansa ta fadi a kasa tana dafe cikinta wanda yake cikeda rauni cikin runtsewar ido,hakan ko kadan bai dameshi ba saima magana daya cigaba dayi,
"Duk maganar ki bazasuyi tasiri akai na ba,saima su kara hura hutar takaicinki a zuciyata,kaman yanda nafada da farko zan sake maimaitawa,ki tashi ki barmin gidana yanzu nan"
Duk wanda yake wajen har sumayyah ya cire tsammanin da cewar abba zai sanja maganar sa,hakan yasa sumayyah babu yanda ta iya cikin dauriya ta mike tsaye ta nufi kofar fita daga falon,har sanann idanuwanta a jikie suke da hawaye sharkaf.
Takawa daya biyu tayi ana ukun taji wani jiri ya debeta kafin tasa kafa ta fita daga falon,saurin kaiwa hannunta tayi ta dafe bakin kofar tareda niyyar saka kafarta zuwa waje.
Shiru tayi nadan sakanni domin sauraron saukar jirin amma maimakon saka sai ma kara hawa dayakeyi.
Duk abinda takeyi idon kowa na kallonta amma kowa yana shakkar taimaka mata saboda fushin abba,har zuwa lokacin da idonta ya rude kirif ta fadi warwas a kasa tamkar matacciya.

    ___________________________

Da kadan kadan idonta yake budewa,amma saita mayar dashi ta rufe kaman mai tsoron budewa, taga haske,saida ta wadatu da hasken wajen kafin ta dora idonta akan fankar datake wainawa a dakin,gefenta ta kallah inda Muhibba ke zaune tana danne danne a waya,abinne ya fadomata rabonta da waya tun sanda mutari ya karba wai zayyi amfani da ita bada sake kallonta,ta dade tana kallon Muhibba wacce take da danne dannen waya,da alama chatting takeyi
Saida tari ya kamata kafin Muhibba ta dago da kulada tashin sumayyan,saurin ajiye wayar tayi tareda matsowa kusada ita tana murmushi.
"Lah aunty sumayya kin tashi,ya jikinnaki,bari na kira aunty nafi,yanzu nan kuwa ta fita itada salma,zasu dauko wasu kayan a gida,ganin baki tashi ba sunyi zaton kwana zamuyi"
Duk maganar da Muhibba take da murnar tashin sumayyah duk ita kadai takeyi,dan sumayyah a ranta jitakeyi ina ma tacan wuce zuwa mutuwarta data huta da wannan rayuwar da takeyi,tambayar kanta tafa ra a ranta kan cewa,meyasa duk abinda yake faruwa da ita yaci ya dauki ranta amma har yanzu bata mutu ba tana nan da ranta.
Saurin tuba tayi a ranta taresa maida hankalinta kan Muhibba,dan duk abinda ya samu bawa bai kamata yayi wanann tunanin ba inda baso take ta kama hanyar tabewa ba.
"Muhibba tun yaushe nake kwance?x"
"Eh awa biyar dai kikayi a kwance"
"Waye yakawoni asibiti,mai abba yace? Ina hajiya mama?"
"Aunty sumayyah wannan tambayoyi kiyi shiru dasu,bai kamata a halin yanzu ki tayar da hankalin ki ba,kina bukatar hutu,sannan inshaallah babu inda zakije a gida zaki zauna,ki kwantar da hankalin ki"
Daga kai sumayyah tayi akan taji abinda Muhibba ta fada,duk da acikin zuciyarta ba haka bane.
Suna cikin magana ne sai ga anty nafi ta shigo da buta da kuma flask s hannunta,itama mamakin tashin nata tayi har saida ta nuna a fuskarta.
"Sumayyah kin ta shi ya jikin to?"
"Da sauki ya gida"
"Lafiya kalau,amma yanzun babu inda yake miki ciwo ko,dazu likita sun miki gwaje gwaje,yanda wancan likitan ya fada suma haka sukace, kuma abin yadan kara yawane saboda bakiyi amfani da ruwan zafi ba,saiki dage da kula da jikinki sosai,dan abba yana nan akan bakarsa na yanke alkarki damu,yanzi ma hajiya mama ce takirani tace nazo naga ya yanayin jikinnaki,dan ita kam babu dama ta zo.
Naji dai yah naseer yana cewa wai zaki zauna a gida,amma akwai sharudan daya gindaya wanda bansan menene ba sai kinje gidan zaki ji.
Shiru sumayyah tayi tana sauraron anty nafi,zuciyarta tana cigaba da bugawa,dan bata san mai abbannasu zai ce da ita ba.
Hawayene ya gangaro daga fuskarta kana ta kalli anty nafin,
"Nagode sosai anty nafi,koba komai naji dadin ganinki,dan allah kuyafemin abinda nayi muku a baya,nasan idan ban nemi yafiyarki yanzu ba basake magana zamuyi ba"
"Haba sumayyah karki ce haka mana,komai zai zo da sauki ki cigaba da addu'a kedai"
"Inshaallah kullum cikin yinta nakeyi"
Daga haka suna nan zaune har bacci ya dauke sumayyah,Muhibba ce ta kalli anty nafi tareda cewa,
"Wlh tausayin anty sumayyah nakeji,lokacin da salma take bani labarin abinda yafaru da ita a gidan aurenta saida abin ya girgizani,gani nake kaman a mafarki,ki kalli fah yanda ta rame tayi baki,ko jinya iyakacin haka"
"Hmm kezaki fadi haka koni,kwanakin baya taje wajena lokacinda ya zubar mata da cikin farko,haka tayi tamin kuka da magangsnu masu karyar da zuciya,lokacin data tafi nadade inayiwa abbansu Nabeel kukan halin da take ciki,harfah wajen baffah Usman naje a Zaria amma yacemin wai bazai iya tunkarar abba a yanzu ba da zancen sumayyah,tunda ga yanda abu yakasance ranar auren"
"Hmm saidai muce ALLAH ya kiyaye kawai,ALLAH kuma yasa abba yabarta a gida,dan korarta daga gida a wannan yanayin babban hatsarine sosai"
"Hakane kam ba'asan wane hali zata shiga,hakan zai iya zefata mummunan hali"
A Daren basu kwana ba likatan dayazo yaga jikin sumayyah ya basu sallama akan su tafi gida,lokacin iyah Muhibba ce a wajenta anty nafi ta tafi gidanta.
Kekasa kasa sumayyah tayi akan bazata tafi gida a ranar ba,har cewa ma tayi wai zazzabi takeji,kallonta Muhibba tayi dan tasan karya take babu wani zazzabi a jikinta,kawai dai ta kula gidanne take tsoron komawa.
"Anty sumayyah ki kwantar da hankalin inshaallah abba bazai korekiba zaki zauna a gida"
"Bawai ban yards dake bane,kawai dai banajin hakan a cikin zuciyata ne,gani nake kamam abbah zai koreni,idan ya koreni bansan inda zanje ba,dan nasan ko gidan baffah Usman naje bazai yarda ba"
"Kidaina fad an haka,yakamata ki zatawa kanki alkhairi a koda yaushe,ki tashi mutafi gida anty sumayyah babu abinda zai faru,kinga yanzu darene babu wanda zai kula amma gobe da safe abin sai yafi haka"
Shiru sumayyah tayi tana nazari,zancen da Muhibba ta fada gaskiya ne,gwanda shigar dare da ta safe.
Da haka dai Muhibba ta yaneta suka hada kayansu driver yazo ya dauke su zuwa gida.
Kasancewar darene baby kowa a masu aiki duk sun tafi gida,hajiya mama ma tana dakinta,muhibba ce suka shigo itada sumayyah wacce take dafe da kafadar muhibban,
"Anty sumayyah na fadawa hajiyah mama mun dawo koh"
"Ahah kibarta sai gobe,a halin yanzu banida karfin halin yin arba da ita,muwuce dakina kawai,idan kuma abbah yazo da daddare ma ya koreni shikenan"
"Kidaina fadar haka mana,muje kiyi wanka ki kwanta,idan har kina bukatar wani abuma mu to"
Dakin Muhibba suka nufah,don nata dakin a rufe yake tun sanda ta tafi,kwanakine ma hajiya mama take cewa zata budewa su farouq shi su dunga kwana (yaran su yah naseer wanda suke wajen hajiya mama).

......toh watakila mai daki ta dawo abinta.....


🏵_*sadi-sakhna*_🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now