part 1

8.8K 376 15
                                    

SANGARTA

            ©
ZULAIHEART HARUNA RANO

Allah ina roƙonka don ƙarfin ikonka, kaba ni iko kamar yadda na fara rubuta littafin nan lafiya Allah Ka sa in kammala rubuta shi lafiya.

Kacokan! Wannan littafin sadaukarwa ce ga KHADIJAH S MOH'D, Allah Ya bar ƙauna haƙiƙa ke ɗin ta dabance, kin wuce duk wani kalma da nake son yin amfani da ita don yabonki, sai dai na yi maki addu'a da fatan ganawa da wannan duniya lafiya, Ya ƙara kauna tsakaninki da Babyn Baby, Ya kawo zuri'a ɗayyaba, na san kin daɗe da sanin ZULAIHAT HARUNA RANO mai ƙaunarki ce.

Bismillahir Rahmanir Rahim!

             1

      Zaune yake cikin ƙasaitaccen falonsa wanda aka tsara su da manya-manyan kujeru na alfarma. Kallo ɗaya zaka yi wa falon ka san ba ƙaramin dukiya aka narka ba. shi kansa kafet ɗin falon ba duka gidaje ake samun irinsa ba sai gidan wane da wane.

Hannunsa ya miƙa tare da ɗauko jaridar Leadership daga kan wani kyakykyawan teburin dake kusa da shi, ya buɗe tare da soma karantawa.  Cikin wata irin tafiya take taka steps ɗin tana saukowa fuskarta ɗauke da murmushi, jikinta sanye da wata rigar bacci wandda bata gama rufe mata cinyoyi ba, kanta ko ɗankwali babu. Kai tsaye wajensa ta nufa. Shi ma tun da ya hangota fara'ar fuskarsa ta ƙaru. Ba ta zame ko ina ba sai inda yake zaune, zama ta yi kusa da shi tare da ɗora kanta saman kafaɗarsa, cikin shagwab'a ta ce
“ Barka da safiya Abbana.”
Murmushi ya yi ya ce “Barkanki dai Uwata, fatan kin tashi lafiya?”
Dariya ta saki tana faɗin, “Lafiya lau Abbana.”
“Madallah, fatan babu wata matsala?” Ya yi tambayar yana kallonta.

“Innalillahi..! Ni Halimatu!! Ke kam don Allah Ameesha kina ɗaukar maganata kuwa? sau nawa ina maki maganar ki daina fitowa a haka?” Maganarta da suka ji kamar daga sama ne ya hana ta ba Abban nata amsar tambayarsa, duk suka juyo ga mai maganar.

    Turo baki ta yi tare da ƙunƙunai “To ni Ummiee wai shi kenan mutum ba zai sake ba shi da gidannsu?”
Daƙuwa Ummiee ta watsa mata tare da ɗaure fuska ta ce, “Za ki tashi ki je ki suturta jikinki ko sai na ɓata maki rai?”

     Ganin fuskar Ummiee ba wasa ya sa ta miƙewa cikin takaici. Abbanta ya ce “Haba Hajiya! Mene ne ya sa kullum sai kin riƙa takurawa yarinyar nan ne? Ko baki san har yanzu ƙaramar yarinya take ba?”

    Wani takaici ya rufe Ummiee ta ji kamar ta gaurawa mijin nata mari “Haba Alhaji, ta yaya zaka ce kar na yi wa Ameesha faɗa in ta yi ba daidai ba? Yarinyar nan fa kullum ƙara girma take yi amma babu hankali a tare da ita. Ji fa irin kayan da take fitowa falo da su, by mistake a yi ɓako ta fito haka ai kunya zamu ji...”

     Ya dakatar da ita da hannu “Look! Hajiya ban son dogon turanci, gida dai nawa ne kuma Ameesha gidan ubanta take, don haka babu mai takura mata. Ke kullum baki da abokiyar faɗa sai yar cikinnki? wallahi wani in ya shigo sai ya yi tunanin bake kika haifeta ba, musamman da kullum faɗa ne ke tsakaninku da ita. Kuma kina maganar ɓako, ai ba mai shigowa falon nan sai da izini. Gidan nan duk muharramanta ne, ba sai ta riƙa sa kaya masu nauyi ba.”

    Takaici ya rufe Hajiya, wanda har ta kasa furta komai, sai aje masa Cup ɗin coffee ɗin ta yi tare da nufi bedroom ɗinta. Tabbas ta san duk wani abu da Ameesha takyeyi da izinin mahaifinta, don shi ne baya ƙaunar a faɗi laifin yarinyar. ‘Allah ya sani ina iya bakin ƙoƙarina wajen ba wannan yarinyar tarbiyya, amma taki ɗaukan duk wani nasiha tawa.’ Ta faɗa a ranta.

   Ameesha tana shiga bedroom ɗinta toilet ta zarce ta sallo wanka. Tana fitowa ta zauna gaban dressing mirror ta soma tsantsara kwalliya. Tana gamawa ta shirya cikin wata baƙar doguwar riga, mai masifar kyau, ta yi rolling ɗankwalin rigar a kanta. Iya kyau dai kam Ameesha ta yi, kamar a sace a  gudu. Kyakykyawa ce sosai mai kimanin shekaru goma sha takwas. fara ce amma ba sosai ba. Ta samo asali da kyau ne wajen mahaifiyarta, komai nata irin na mahaifiyar ne. Maryam Tahir kenan inkiya kuma Ameesha yarinya 'yar gatan Abbanta.

    Wayoyinta ta kwasa daga kan gado ta sanya takalminta mai kyau, sannan ta fita falon don yunwa take ji sosai. wani murmushi ta saki ganin har a lokacin Abbanta na zaune a falon
“Wow! Babyna kin yi kyau.”
Abban ya faɗa yana nuna farin ciki.
Ɗan turo baki ta yi ta ce “Na gode Abban Ameesha. Abba so nake yi na je Saloon saboda kaina yana yi mini nauyi.” Cike da shagwaɓa ta ƙarasa maganar.

“Ok babu damuwa my baby. Yanzu dai je ki fara yin break don na san kina jin yunwa. In kin gama sai ki tafi.”

   “Abba nifa ba kudi a hannuna, kai za ka ban kuɗin da zan yi amfani da shi.”

    “Sai dai ki je da ATM Card don ba ni da wasu kudi masu yawa a gida.” Ya bata amsa a lokacin da yake ƙoƙarin mayar da hankalinsa ga jaridar da ke hannunsa.

“No Abba, Gaskiya ba zan iya bin layin ATM ba, mutum ya je ya yi ta tsayuwa.” Ta yi maganar kamar zata yi kuka a daidai lokacin da Hajiya Halima mahaifiyar Ameesha ta iso inda suke.

      “Yawwa Hajiya muna da buƙatar kuɗi in kina da su a hannu.” Alhaji Tahir ya faɗa, yana rufe jaridar.

     “Wani irin kuɗi kuma Alhaji?" Hajiya ta tambaya cikin nuna rashin fahimta "Baby ce zata je Saloon kuma wajena babu kuɗi a gida, ki bata 30 thousand naira ƙila su isheta.”

     Zaro ido Ummiee ta yi ta ce “Alhaji dubu talatin fa kace! Da su zata je wajen Saloon ɗin?”

    “E, saboda zata biya ta yi wo shopping. ko kuma dai bata fifty zai fi.”

      Jinjina kai ta yi tare da ba shi amsa a takaice “Ai ba ni da su.”

     “Zan mai da maki kuɗinki Hajiya.”

   Juyawa ta yi ta nufi bedroom ɗinta, tana ƙara mamakin halin mijin nata.

    Ameesha kam sai da ta kammala break ɗin ta tsaf, kana ta baro dining table ɗin. Wajen Abban ta nu fo ta faɗin “Abbana na gama.”

     “Ok je ki amshi kuɗin wajen Umminki, 50k ne ai za su isheki ko? Sai ki siyo yan abubuwan buƙata da abinda ya rage.”

Daga kai ta yi kafin ta nufi bedroom ɗin Ummin. Ta yi Sallama ta shiga. Hajiya Halima dake zaune ta amsa. “Ummiee ki ba ni kuɗi in ji Abba.” Ameesha ta faɗa tana turo baki, ita a dole tana jin haushin faɗan da Ummiee ta yi mata ɗasu. 

Girgiza kai Ummiee ta yi ta ce “Allah ya shirya mini ke Ameesha, wai yaushe za ki yi hankali ne?” Ta ƙarasa maganar tana miƙa mata kuɗin.

Amsa ta yi tare da yin waje. tana zuwa ta aje masa kuɗin a kusa da shi. Cikin muryar kuka ta ce “Abbana ba na son kuɗin nan.”

    Hankalin sa ya tashi da ganin hawayen tilon ɗiyarsa mace, ya ce “Uwata me ya faru?”

     Jikinsa har wani rawa yake.  “Ba Ummiee ba ce bayan ta ba ni kuɗin sai ta ce wai Allah Ya shirya ni...”

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now