ARBA'IN DA BIYU

2.1K 122 3
                                    

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

*Ku taya ni murna ranar asabar bikin k'awata Yar'uwa kuma Aminiya, ina farin cikin zuwan lokacin bikin ki MARYERM IMAM RANO Allah ya baki zaman lafiya a gidan aurenki, Ubangiji ya albarkace ki da ya'ya nagari Amin Allah kuma yasa mijinki ne bokin arzikin ki*
 
                  *42*

Da taimakon ma'aikatan gidan ya shirya kulolin a mota, sannan ya yiwa Nenne sallama, kai tsaye gida ya nufa a lokacin karfe biyu saura mintina. Bayan ya yi fakin ya kwashe kayan zuwa bangaren Ameesha, yana buɗe kofar Ameesha da ke zaune a falon ta yi saurin tashi tana amsar kayan da ya shigo da su.

"Sannu da dawowa baby."

Ta yi maganar tana shirya kayan a kan dining.

"Yawwa Cutie na barki ke kaɗai ko?"  Dr ya yi tambayar yana kai hannunsa kugunta. Bata yi magana ba har sai da ta gama abin da take sannan ta juyo.

"Baby na yi kewarka sosai." A shagwaɓe ta yi maganar tana rungumeshi.

"Na fiki kewarki Cutie na na kosa na dawo gida na yi arba da kyakkyawar fuskarki." Yana maganar ne yana sinsinar wuyar ta.

"An ya kuwa baby?"

"Sosai kuwa." Ya tabbatar mata da haka. Ko kafin ta yi magana ya yi saurin faɗin

"Mu je ki ci abinci sai ki bani labarin missing dina da kika yi." Zaunar da ita ya yi a dining din sannan ya ɗauki plet ya cika da abinci

"Ina zuwa Cutie zan kaima Aneesa abinci, karki fara ci fa don tare za mu ci." Yana maganar yana tafiya.

"To! Kawai Ameesha ta amsa.

Kamar ko da yaushe yanzu ma kofar ta abude take shiga cikin  falon kawai Dr ya yi bakinsa dauke da sallama, ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba sai ma ɗaukar remote control ta yi tana kara maganar t.v

Murmushi kawai ya yi lamarin Aneesa sai dai addu'a, kullum abin gaba yake ba ya sauki kusa da ita ya isa tare da aje plet ɗin ya ce "Ga abinci nan ki ci my Anee don nasan kina tare da yunwa." Yana gama faɗa ya sa kai zai fice.

Cak! Dr ya tsaya jin maganar da Aneesa ke yi.

"Zo ka ɗauki abincin ka bana ci, ko an ce ma ni mayunwaciya ce?" Ta kai karshen maganar tana watsa masa harara.

Takowa ya yi a hankali har inda take zaune ya sassauta murya ya ce

"Look Aneesa ya kamata kisan da wa kike magana, domin na fi kowa sanin  ke ba mayunwaciya ba ce, amma hakkin ciyar da ke yana kaina don haka ga abinci nan na kawo maki, ko kici ko ki  zubar ruwanki." Gama maganar sa ya yi dai dai da soma tafiyarsa.

Mtsww! Aneesa ta ja tsaki bayan fitar Dr daga falon, gaba daya haushinsa take ji, ko birgeta ba ya yi yanzu.

Yana takaicin halin Aneesa sam bata da halin kwarai ita kenan kullum cikin masifa, kai Allah ya kyauta, sai da ya daidaita nutsuwarsa kafin ya shiga falon, inda ya bar Ameesha zaune a nan ya sameta tana aikin Game a wayarsa.

"Sorry Cutie na barki ke kaɗai ko?"

A je wayar ta yi tana sakar masa murmushi bata iya cewa komai ba, saboda wani irin kallo da Dr ke aika mata, take wani irin kasala ta saukar mata, zama Dr ya yi bayan ya zuba masu abinci kan cinyarsa ya yi mata mazauni da kan sa ya rika bata har sai da ta koshi, sannan ita ma ta shiga ba shi, suna yi suna zuba soyayyar su har suka kammala, kwashe kayan Meesha ta yi ta kai kicin, sannan ta gyara inda ya ɓaci Dr kallonta kawai yake cikin wani irin shaukin soyayya, ya yadda yana son Ameesha so irin wanda bai taɓa yiwa wata ba, bai san time da ta iso wajensa ba sai jinta ya yi ta shige jikinsa.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now