ARBA'IN DA DAYA

2.3K 123 1
                                    

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

*Wow gaskiya ina godiya sosai masoya, bani da bakin da zan iya kwatanta farin ciki da nake ciki, sai dai nace Allah ya saka da mafificin Alhairi, ina alfahari da ku😍😍*

'''Khadija S Muhammad
         &
Badeeyar Adam (beauty queen) hakika ku ɗin na daban ne, babu abin da zance akan ku, sai Allah ya saka maku da Alhairin sa ya bar mana zumunci har karshen rayuwa. (Aneesa tana gaisuwa lol)'''

_*Sorry sister SHAMSHIYA SALIS wallahi na yi missing contact naki, na yi ta jira ko zan ga maganar ki na ji shiru, amma jiya nasa mu Number insha Allah zaki ganni yau*_
       
 
                  *41*
Ya yi kusan minti biyar a zaune, rungume da Ameesha wacce ke ta sakin ajiyar zuciya, kallonta ya yi cikin tausayawa ya kaima goshinta sumba, tabbas ya jinjina mata don sosai ta yi kokarin amsan lalurar sa, bai so tun yanzu ya nuna mata haka ba so ya yi sai ta ɗan kwana biyu amma sam a daren jiya kasa control ɗin kansa ya yi, gyara mata zama a jikinsa ya yi yana faɗin

"Allah ya maki albarka Maryerm hakika kin cika yar halas."  Jin Dr ya yi sama da ita yasa ta kuma rintse ido don bata son su yi ido hudu, bai zame ko ina da ita ba sai toilet inda ya haɗa mata ruwa masu dan karen zafi, Ameesha batai aune ba sai jinta ta yi cikin wannan ruwan, ai da karfi ta saki k'ara saboda yadda ta ji shigar ruwan jikinta, sam Dr bai damu ba sai ma ci gaba da buɗe mata kafa yadda ruwan zai shiga da kyau yake yi, tun tana mugun jin zafi har ta soma jin dadin sa.

Sai da ya sanya ta cikin ruwan zafi sau uku, sannan ya barta.

"Heartbeat ki yi wankan tsarki ina zuwa." Dr ya yi maganar yana fita.

"To." Ameesha ta amsa idonta a rufe don taki yadda su hada ido.

Fita ya yi ya cire zanen gado ya canza wani, sannan ya koma toilet ya ɗauko Ameesha akan gado ya yi mata masauki, fita falo ya yi bai wani jima ba ya dawo hannunsa dauke da cup din shayi.

"A'a wai har kin kwanta?"

"Dr bacci nake ji."

"Ok tashi ki sha tea sai ki sha magani kin ji ko?"

"To." Ta amsa tana tashi zaune.

"A'a wai lafiya kuwa, shi idon yau an daina buɗe shi ne?" Yana maganar ne yana mik'a mata cup.

Turo baki ta yi cikin shagwaɓa, bata ce komai ba haka ya shiga bata tea a baki ido na rufe kamar makauniya, bata wani sha da yawa ba ta ce ta koshi, magani ya balla ya bata yana shafa mata gadon baya ya ji ta saki gyatsa, babu jimawa bacci ya yi gaba da ita. Gyara mata kwanciya ya yi ya rufe ta da blanket, kafin ya nufi toilet ya tsarkake jikinsa, lokacin karfe uku na dare sallaya ya shimfida ya shiga nunawa Allah farin cikin sa tare da gode ma Allah da ya ba shi Ameesha matsayin mata, yana mai addu'a da babban murya Allah yasa kwallonsa ya shiga raga.

Ya daɗe zaune yana addu'oi kafin ya kwanta rungume da ita a jikinsa, bacci mai dadi ya ɗauke shi, yadda jikin Ameesha ke kadawa ne ya farkar da shi a gigice a lokacin  karfe shida an dade da isar da asbah, kallon ta ya yi a dimauce jikinta babu inda baya rawa  haƙora ta sai haduwa suke da juna, saboda zafin zazzaɓi, magani ya ballo ya bata da kyar ta iya hadiyewa, sannan ya goge mata jiki da ruwan sanyi da towel, sosai zafin jikin ya ragu har bacci ya dauketa, sai lokacin ya samu nutsuwa har ya yi sallar asuba.

Bai koma bacci ba sai zama da ya yi yana jiran ya ga tashin ta,  yana ta zaune har ya soma gyangyadi bai sannan lokacin da wani nannauyan bacci ya dauke shi ba, sun sha bacci inda Ameesha ta soma farkawa karfe tara, yanzu kam jikin da sauki sai dai jinta take fayau da ita kamar iska zai dauketa. Shiga toilet ta yi tare da haɗa ruwa, sai da ta kuma zama cikin sa ta yi wanka hadi da alwala, har zuwa lokacin Dr bai farka ba sallah ta yi, sannan ta tsantsara kwalliya cikin wata jar atamfa dikin riga da siket, sosai kayan suka amshi jikinta, feshe ko ina na jikinta ta yi da daddaɗar turarenta mai sanyin kamshi ta yi, har ta zauna sai kawai ta tashi ta nufi bedroom ɗinta, don tasan Dr ba barinta zai yi ba.

SANGARTA COMPLETETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang