BABI NA BIYAR

2.7K 137 0
                                    


*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

5

"Heeee." Ya daka mata wata irin tsawa, da yasa Meena rugawa waje, don Meena fa akwai tsoro.

"Get out side."

"Sorry Sir! Wallahi makara muka yi."

Ameesha ta yi maganar ta na ci gaba da tafiya.

"Baki ji abinda na ce ba ne? Ki fitar min a lab, tun kafin na shigo ai na faɗa maku dokata, don haka yi waje ba karatun kike so ba, da har zaki ce wai makara ku ka yi nonsense kawai." Cikin daure fuska ya ke maganar, in ba kana cikin lab ɗin ba, sai ka rantse da Allah ka ce ba shi ya ke maganar ba, don ko kallon inda take bai yi ba.

Cikin sauri Ameesha ta ɗago da kai, jin yadda ya zageta karaf suka haɗa ido da shi, don dama duk maganar da su ke yi ba ta kalle shi ba tana ganin shi, sai ta saki wani malalacin tsaki tare da juyawa. Gaba ɗaya yana lab ɗin sakin baki suka yi tare da bin ta da kallo.

Daidai lokacin da za ta fita ta ji ya na faɗa masu sunansa.

"Asmad Abubakar ɗan Fullo, Ya ce amma an fi saninsa da. Dr ɗan Fullo"

Maimaita sunan Ameesha ta yi a zuciyarta wato 'Asmad Abubakar ɗan Fullo lallai zaka gane kuranka.' Ta ƙarasa maganar tana fita daga lab ɗin.

In da Meena ke zaune ta nufa ranta a matuƙar ɓace, kallonta Meena ta yi tare da fashewa da dariya ta ce

"Kai! Meesha wannan irin abu haka, kinga yadda kika yi kuwa kamar fulawar da ta samu yis da rana?" Meena ta kai ƙarshen maganar tana ci gaba da dariyar ta.

Wani malalacin kallo Meesha ta watsawa Meena ta ce

"Ke fa Meena baki da kirki me na yi da har kike cewa mini wai kamar fulawar da ta sami yis da rana? Ke bama wannan ba wai tsoron mutumin can kika ji ne?"

"Sosai ma kina jin irin tsawar da ya zabga mana, kamar an busa algaita taf ai wallahi ya firgita ni, amma ke naga ko a Jikinki ?"

"Ƙwarai kuwa ko a jikina, dama ina nemansa, kuma ga shi yau Allah Ya haɗa ni da shi, don haka wallahi sai na rama marin da ya yi mini jiya." Ta kai ƙarshen maganar tana huci.

Cikin rashin fahimta Meena ta ce "Ban gane ba Meesha dama kin san shi ne?"

Sweet ta ɗauko cikin jakarta tare da jefawa cikin baki ta ce

"Jiya muka haɗu a Sahad na je yin shopping, shi ne fa ya yi min crossing hanya don na yi masa magana sai ya mare ni."

Mamaki ya kama Meena, don haka sai kawai ta zubawa Ameesha ido tana kallonta, zuwa can ta ce

"Amma Meesha da zaki yarda in na baki shawara, wallahi ki bar mutumin nan, don babu ta yadda za ki iya rama..."

Hararar da Ameesha ta jefeta da ita, shi ne ya hanata karasa maganar da take yi.

"Meena kenan kin manta halina ne hala?"

"A'a shawara dai na ke baki."

"To ba ni son shawarar riƙe kayan ki, amma ramuwa kuwa babu fashi."

Meena ta buɗe baki da niyyar magana, Ameesha ta yi saurin katse ta ta ce

"Please karki ce min komai, tashi mu je na yi break don ban yi ba na fito, wallahi da nasan wannan nonsense ɗin mutumin ne, to ba zan fito ba sai na yi break ɗina."

Tashi Meena ta yi suka kama hanyar inda Rastaurants ɗin da Ameesha ke cin abinci yake. Daidai lokacin da suka dawo shi kuma ya ke fitowa daga lab ɗin, harara Ameesha ta cilla masa, sai ko aka yi sa'a ya gani, girgiza kai kawai ya yi ya nufi inda motarsa take, hannunsa riƙe da bag din laptop ɗinsa.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now