HAMSIN

2K 109 4
                                    

*SANGARTA*

®
_*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*50*

Haka ta wuni sukuku har su Aneesa suka dawo, a falo suka sameta kwance Miemie da sauri ta faɗa kanta tana faɗin "Mami min dawo." "Sannu da dawowa 'yar Momma ya Nenne?" "Lafiya lau tana gaidaki." Aneesa ta bata amsa. "Ina amsawa." Ta amsa a takaice "Wai har yanzu ciwon kan ne?" "A'a me kika gani?" "Babu komai kawai na ga kamar ba ki cikin nutsuwa?" "Ki bar kawai wallahi ɗazun bayan fitar ku Dr ya tabbatar min ina da ciki har tsawon wata biyu." "Shi ne abin tashin hankalin?" "Eh mana duka shekarar Miemie daya fa gaskiya ba haka na so ba." "Hmmm! Yar'uwa kenan wallahi wannan ba abin damuwa ba ne ki bar tada hankali ki yi addu'a Allah ya sauke ki lafiya, idan ta Miemie ne ba abin damuwa ba ne saboda Miemie tana cin komai tana tafiya kuma bata damu da nono ba."

"To ya zan yi dole ai na hakura Allah ya bamu masu albarka, Miemie kuma yanzu zan hado mata sauran kayanta dake dakina ku karata can, dama kun saba Allah ya raya maki ita." "Yar'uwa kina nufin kin yaye Miemie kenan?" "Eh, ta koma dakin Momman ta dama tun da ta zo duniya take ɗiyar Momma to yau Allah to yau Allah ya tabbatar." Ameesha ta gama maganar tana mik'ewa tsaye. Rasa abin da zata faɗa Aneesa ta yi don sosai abin ya bata mamaki, wato kyautar da Ameesha ta yi mata na Miemie tun ranar da ta fado duniya gaske ne? Lallai ta jinjina da karamci irin nata da zallar farin ciki da murna ta ce "Na gode sosai Ameesha Ubangiji Allah ya baki abin da kike nema duniya da lahira, wallahi da ana samun kishiya irin ki da ko wacce mace zata so a yi mata kishiya hakika ke kin bambanta da sauran mata, na cutar da ke Ameesha na mugunawa rayuwar ki amma duk da haka ke kullum da Alhairi kike nufina, a zatona tun da kin kasance shagwaɓaɓɓa idan kika auri Hamman za ki iya raba ni da shi ko dan salon SANGARTAR ki ashe abin ba haka ba ne, ki yafe min don Allah." "Na yafe maki Allah ya yafe mana baki daya." Ameesha ta faɗa fuska sake.

"Na gode Allah ya saka da mafificin Alhairi, Ubangiji ya biya maki buk'atar ki ya sauke ki lafiya." Murmushi kawai Ameesha ta yi ta amsa amin "Allah ya ci gaba da bamu hak'urin zama da juna da zuciya daya." "Amin" suka amsa tare. Sannan ta nufi bedroom kaf kayan Miemie ta kwashe ta kai bangaren Aneesa, farin cikin da Aneesa ta shiga a ranar baya misaltuwa. Ko da Dr ya dawo ya samu labari dariya kawai ya yi ya ce "Allah ya taya ta riko, Ameesha na lura dama kamar baki damu da Miemie ba?" "Haba beby wannan wacce irin magana ce? Miemie fa 'yata ce bana jin duk duniya akwai wanda ya kaini sonta, amma ka duba hidimar da Aneesa ke yi wa Miemie wallahi ta cancanci kyautar Miemie, na bata da zuciya daya Allah ya kara haɗe kanmu."

Rungumota jikinsa ya yi yana jin wani sabon soyayyar ta a zuciyarsa, bai taɓa ganin mai sanyin hali irin ta Ameesha ba, wallahi a time ɗin da suka fara haɗuwa da Ameesha a sahad bai taɓa tunanin tana da sanyin hali da tunani ba sai da ya mallaketa, kara matseta ya yi jikinsa ya ce "ina sonki matata so irin wanda bazai misaltu ba Allah ya yi maki albarka." "Nima ina sonka Dr Asmad Abubakar My fullo, Ina jinka har cikin zuciyata uban 'yayana, kullum fatana shi ne in faranta maka." Daɗi sosai ya rufe Dr jin kalaman da take faɗa masa, shi sai ya ji a duniya ya fi kowa sa'a. Sun daɗe a haka rungume da juna kafin Ameesha ta lankwashe murya tana faɗin "Beby wankan fa kalli time ga yi baka lek'a Aneesa da Miemie ba." "Oh! Wallahi har na manta, idan ina tare da ke manta kowa nake yi mu je ki yi min My wife." "An gama mijin mace biyu." Ta gama maganar da dariya. "Baki karya na autar Ummi ni ne mijin mace biyu Aneesa da Ameesha Baban Fatimah (Miemie)." Dariya sosai maganar Dr ya ba Ameesha don haka har suka shiga toilet din tana dariya.

Sun ci gaba da gudanar da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har Allah ya sanya Ameesha ta shiga watan haihuwar ta, ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ga shi Dr baya gida, Aneesa ce ke ta taimaka mata amma fa sosai ta sha wahala fiye ma da haihuwar Miemie sannan ta haifi lafiyayyun yaranta biyu mace da namiji, tsaf Aneesa ta wanke yaran tare da shirya su cikin kayan sanyi masu taushi da kyau.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now