Complete

2.8K 125 11
                                    

*SANGARTA*


©
_*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*LAST*

_*Masha Allah! AlhamduLillah Ina matuk'ar godiya ga Allah da ya nuna min wannan rana da na kammala wannan littafi, ina cikin farin ciki mara misaltuwa*_

GODIYA

*GODIYA MAI TARIN YAWA GA*
*My Besty Khadija S Muhammad, hakika ina alfaharin samun ki a matsayin amintacciya, domin kuwa duk wani abu da aka gani cikin wannan labari ke ce silar shigarsa banza gaji da gode maki ba, Allah ta'ala Ya saka maki da mafificin Alhairi Ya bar mana zumunci har ya'ya da jikoki Allahumma amin.*

'''JINJINA GA
Ummyn Yusrah fan's group
Bilkisu Bilyamin Novel's
3 Star Hausa Novel's
Surbajo Hausa Novel's group
Láifin wa? And sangarta fan's
Khalisat Haydar Hausa Novel's
Zama na amana 2
Hassan ATK
Hussain ATK
Umar Dalhat
Kamala Minna
Khadijah S Muhammad
Fa'eeza S Muhammad
Ummu Sayyid
Ummyn Yusrah
Amrah Auwal mashi (Princess Amrah)
Ramlat Ar Manga (My me Dambu)
Nafeesa Musa Ankerh'''

Da sauran wanda ban lissafo ba.

'''I hearttttt you my daughter Badeeyar Adam (beauty queen)'''


*51*

Ɗaukarta ya yi ba tare da ya ce komai ba ya nufi motarsa, ciki ya sanya su suna ci gaba da wasa da Littel Ameesha kai tsaye gidansu ya kai ta, Rufaida kanta ta yi mamakin ganin Miemie har ta kasa haƙuri ta ce "Honey wannan kamar yarinyar da ake cigiya ko?"
"Eh! Ya amsa mata a takaice. "Please ki yi mata wanka ki canza mata kaya sai mu kai ta gidansu."
"Gidansu Honey baka tsoro ace kai ka saceta?"
"Ai gara ace ni ne na saceta akan aka ma wanda ya saceta ɗin, amma duk da haka ya zama dole iyayenta su san wanda ya saceta." Ya gama magana yana ɗage kai wanda ke tsananin yi masa ciwo, tir yake da halin mahaifinsa na son abin duniya, 'wato ashe Abba zai iya haɗa kai a yi kidnapped ɗin jikar amininsa? Lallai duniya ta zo ƙarshe Allah Ya rabamu da son zuciya.'

Cikin ƙananun lokaci har Rufaida ta tsaftace Miemie ta shiryata cikin wata kyakkyawan doguwar riga mai kyau da tsada sosai yarinyar ta yi kyau da yake har kitson kanta ta canza mata sai ta fito fes, suna riƙe da hannun juna ita da Littel suka shiga mota, sai da suka biya suka ɗauki Mommy sannan suka ɗauki hanya a tsanaki yake tuƙi har suka isa unguwar.
Horn ya yi a ƙofar gidan mai gadi ya buɗe masa, ya yi parking a gefe yana hamdala da ganin motar Abban Ameesha a gidan, hakan ya nuna cewa yana cikin gidan ke nan, bayan ya faka motar bai fita ba sai ya ce "Littel da Miemie su fita, sai da yaga sun yi nisa har sun kai ƙofar falon Aneesa sannan suka fito daga cikin motar, kowa ya ga fuskar Najeeb ya san akwai damuwa "Ka ga Najeeb ka cire wannan damuwar kar wani cutar ta shigeka." Mommy ta yi maganar cikin sigar lallashi. "To mommy ya amsa yana ƙaƙalo murmushi iri wanda iyakarsa laɓɓa. Suna kallon yaran suka fito daga ɗaya ɓangaren suka nufi ɗayan.

Duk suna zaune sai gani suka yi Miemie ta shigo riƙe da hannun Littel, da mamaki suke kallonta sun kasa motsi, kallo ɗaya zaka masu ka tabbatar suna cikin farincikin ganinta, babu ma kamar Aneesa har rige-rigen zuwa ɗaukarta ake wani irin miƙewa Aneesa ta yi da gudu ta nufi Miemie wacce ta saki hannun Littel ta nufi Aneesa tana faɗin "Oyo-yo Momma."
"Oyo-yo 2 My baby I Miss You, daga ina kike? Wa Ye suka ɗauke mini ke Miemie?" Aneesa ta jero mata tambayoyin cikin sauri. "Watu mutane tuka ta ni a motarsu wai za su kai ni wajen Daddy shi ke nan na tena ka nin ku." Cikin maganarta wacce ba ta fita sosai ta yi maganar.
Kafin ta yi wata magana sai jin sallamar su Najeeb suka yi. Gabaɗaya suka ɗago da mamaki suna amsawa.

Ciki suka shiga aka gaisa Ameesha cike da ɓacin rai tana shirin yi wa Najeeb rashin mutunci, wato shi ya ɗauke mata yarinya ya barsu cikin matsala da tashin hankali, shi ma a ɓangaren Dr haka abin yake hanya yake nema da zai nuna wa Najeeb kurensa, sai yanzu ya tuna shi wannan saurayin Ameesha ne na da wanda suka yi zaman asbiti lokacin, maganar Najeeb ce ta dawo da su hankalinsu "Abba a yi haƙuri ga Miemie nan ɗazun Allah Ya sanya muka ganta, bana son kowa ya ce komai sai kun je gidan da muka samu Miemie daga nan sai ku san matakin da za ku ɗauka, amma ina roƙon alfarma Abba kar ka ji kunyar wanda ya aikata maka hakan.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 31, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now