BABI NA SHA DAYA

2.2K 139 0
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

''' ina matukar taya ki murna my sweet sister BILKISU BILYAMIN Ubangiji Allah yasa kifi haka Allah ya kara baiwar fasaha da kaifin brain'''

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

                      *11*

A hankali cikin mutuwar jiki ta kai hannu ta amsa.

" Na gode"

Ameesha ta yi maganar cikin wani irin voice.

Murmushin nan ne dai kwance a fuskar sa

" no need "

Ya bata amsa, yana juya kai, bai wani bata lokaci ba ya tada motarsa don dama jiranta ya tsaya yi, kuma tunda ta dawo har ta amshi abin ta mai zai tsaya yi.

Fuskar nan tata yake gani kota ina,  yanayin da ta shiga dazun yake mamaki, da wannan tunanin ya kama hanyar gidan su.

Ameesha kuwa bayan wucewar sa, da kallo ta raka motar har sai da ya kulewa ganin ta sannan ta saki wani sansanyan ajiyar zuciya a fili ta furta

" Allah na gode maka."

Motarta ta koma, zuciyar ta cike da tunanin Dr dan fullo, da irin taimakon da ya mata a wannan rana, da wannan tunanin ta isa gida.

Parking ta yi tare da zaro hand back din ta, cikin rashin kwarin jiki ta nufi hanyar shiga falo, dan juyowar da zata yi sai ko idonta ya sauka kan motar Najeeb dake aje a parking space, siririn tsaki taja ranta ya dan sosu da ganin motar.

Falo ta shiga ko sallama bata samu ikon yi ba sai ma zubewa da ta yi a kujeran falon ta furta

" Wash! "

Ummi dake fitowa daga kicin ta zubawa Ameesha ido, da mamaki ta ke kallonta don duk wanda ya ga Ameesha yasan ba a cikin nutsuwa take ba.

"  Lafiya kuwa Auta? "

Ummi ta karasa tambayar tana nufa inda Ameesha ta ke.

Wani murmushi ta k'ak'alo wanda iya karsa lebe, don tun kallon da Asmad ya mata Jikinta ke mace.

" Ummi lafiya lau fa, kawai gajiya ce."

Ta bata amsa tare da maida hankali kan Ummi.

Zama Hajiya Halima tayi tare da riko hannun Ameesha, don ko kadan bata kaunar damuwar Ameesha.

" Anya kuwa Ameesha? Jifa yadda kika koma kodai baki da lafiya ne? "

Girgiza kai tayi alamar a'a. 
" Are your sure?"

"Sure Ummi."

" OK tashi kije kiyi wanka, sai ki ci abinci, ga Najeeb can yana jiran ki."

"To " kawai ta amsa tana mikewa.

A toilet ma dai da Ameesha ta shiga, duk tunanin Asmad din ne a zuciyar ta, ruwa ta watsa tana fitowa ta shirya, Yau simple dress tayi, don riga da siket ta sanya na atamfa, powder ta mursa sai lipstick da ta shafa, ya zuwa wannan lokacin miss call a wayarta sun haurawa ashirin, a fusace ta dauki wayar

" Hello." ta fada bayan ta Kara wayar a kunne.

Banji mai aka ce mata ba Sai ce wa ta yi, ai nasan da zuwan ka amma yau sai dai ka daga min Kafa don ina da bukatar in samu nutsuwa."

Fadin haka keda wuya ta yanke kiran, tare da jifa da wayar rai a bace,  tafiya ta soma yi don sauka falo, domin tasan matukar bata sauka falon ba to Ummi sai ta daga hankalin ta.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now