BABI NA BIYU

4K 199 5
                                    

2

    Zaro ido ya yi ya ce “Me Hajiya take nufi da wannan kalmar? Tana nufin ke ba shiryayya ba ce?” A zafafe yake maganar.

     “To ni ma fa Abba abin da ya ban haushi kenan, ita Ummiee kullum bata son ta ga ina farin ciki, sai ta yi dalilin sanya ni cikin damuwa"

       Ameesha ta yi maganar tana cigaba da matsar ƙwallar ta. “Yi hakuri 'yar Abba tashi ki je zan sami Hajiyar yanzu, sai ta faɗa min dalilin ce maki hakan, oya je ki wanke fuskarki.”

     Ummiee ce ta fito daga bedroom ɗinta, ganin Ameesha na kuka ya sa ta mamaki, har ta kasa ɓoye mamakinta ta hanyar yi mata magana “Ke lafiyarki kuwa, kin fasa tafiya Saloon ɗin ne?”

    “Wani irin tambaya ce haka Hajiya, ke fa kika sa yarinyar nan kuka, amma yanzu ki zo kina tambayarta” Cikin faɗa ya ƙarasa maganar.

     Ɗan murmushi Ummiee ta yi ta ce “Haba Alhaji ka daina saurin ɗaukar fushi a kan lamarin Ameesha, in ban da kai ma kana biye mata, har yaushe za ta ce na sakata kuka ka yarda? Kodayake tun da Sangarta na damunta, dole ne ta yi kuka don na yi mata addu'ar Allah Ya shiryeta ita.”

     “Yawwa kin ji ba, me kalmar Allah Ya shirya ta yake nufi? Gaskiya ni ban son haka, duk mai son zaman lafiya to kar ya taɓa mini Uwata.” Ya gama maganar cikin fushi.

     Jinjina kai Ummiee ta yi ta ce “Allah Ya baka haƙuri Alhaji, amma maganar nemar wa  Ameesha shiriya wajen Allah yanzu na fara, don ta fi buƙatar irin wannan addu'a fiye da komai.” Tana gama faɗi haka ta yi shigewarta kicin.

    “ 'Yar Abba tashi ki je ki wanke fuskarki, sai ki zo ki tafi ko?”

    “Ni fa Abba ina jin na fasa zuwa.”

     Ameesha ta yi maganar tana cigaba da latsa wayarta. Don dama duk maganar da Abbanta da Ummiee suke yi tana jin su, ko kallon su bata yi ba har suka gama.

   "Haba 'yarlelen Abbantq mai zai sa ki fasa? Tashi maza ki je ko kina son na kaiki da kaina ne?”

    “A'a Abba da kaina zan je.”

   “Ok to tashi, da wacce motar za ki fita da ita?”

    “Abba sabuwar motar ka zan hau yau, wannan wanda aka kawo last week, Bugatti Veyron ɗinka.” Ta ba shi amsa tana taka step, don hawa sama.

   Faɗaɗa fara'arsa ya yi ya ce “To maza ki fito ki zo ki dauko key, sai ki tafi 'yar Abbanta.”  Ya ƙarasa maganar yana girgiza kai.

    Cike da nutsuwa ya shigo falon bakinsa ɗauke da sallama, ganin Abba yana zaune a kan kujera sai shi ya tsuguna, sannan ya soma gaida mahaifin na shi cikin ladabi, fuskar Abba sake ya amsa da “Lafiya Lau Jaheed ya ka tashi?” Duƙar da kai kasa ya yi yana amsawa. Hajiya Halima ce ta fito daga kicin fuska ɗauke da fara'a tana faɗin “Lallai Jaheed yau ka yi nannauyan barci, har shaɗaya ta gota fa sannan ka fito?”
  “Wallahi Ummiee jiya da zazzaɓi na kwana yanzu ma da ƙyar na tashi” Ya ba ta amsa.

     “Ayya sannu Allah Ya kawo sauƙi, tashi ka yi break sai kasha magani, kuma shi ne ba ka kira waya an kawo maka break ba, ga shi kuma da aiki, amma dai ba za ka fita ba ko?” Cikin tausayawa ɗan nata take maganar.

    “Abba na ɗauko key din sai na dawo.” Muryar Ameesha ya katse masu maganar.

    “Ok 'yar Abba a dawo lafiya.” Abban ya faɗa cike da kulawa.

     “Ke ina za ki je yanzu a wannan lokacin har da ɗaukar mota?” Jaheed ya tambaya ransa a ɓace

“La! Yaya kai ne, ina kwana? Saloon zan je fa daga nan zan biya na yi Shopping.” Cikin shagwaɓa ta gama maganar.

Harara Alhaji Tahir ya zabga Ya Jaheed ya fara magana cikin masifa “kai jama'a ni kam ban son fi'ili, yanzu kai ina ruwanka da inda zata je, kawai kowa ya saka idon shi a kan yarinya.” Mtswwww! Ya saki tsaki.

“Allah ya baku haƙuri dama ba da wata manufa na yi mata tambayar ba.”

    “Ku dai kuka sani kuma, ku yi ku gama ita dai Uwata dashen Allah ce.”

     Jinjina kai kawai Ummiee ta yi cikin ranta tana faɗin “Lallai lamarin Alhaji ƙara gaba yake.”

     Matsawa kusa da Abbanta ta yi tare da manna masa kiss a kumatu ta ce “Abbana ina sonka sosai, sai na dawo.” Murmushi ya saki yana ce mata “To a dawo lafiya Uwata Allah ya tsare ki riƙa kula da kanki, kin san akwai wanda suka sa maki ido.”

    “In Sha Allah Abba.” Ta yi maganar tana fita daga falon.

   Mamaki sosai ya rufe Ummiee, da irin maganar Alhaji Tahir ɗin, Jaheed ya buɗe baki zai yi magana suka haɗa ido da Ummiee, yana ganin kallon da Ummiee ta yi masa ya gane nufinta, don haka sai ya ja bakinsa ya yi shiru, ita kam Ameesha tuni ta yi tafiyarta.

         ASALIN LABARI

    Maryam Tahir Ameesha ɗiya ce ga Alhaji Tahir da Hajiya Halima, yarinya ce 'yar gata wajen mahaifinta, Alhaji Tahir haifaffan garin kano ne, cikin ƙaramar hukumar Bicci, yana da matar aure d'aya da ya'yan sa biyar, Hajiya Halima ita ce matarsa ta lalle, daga ita har yanzu bai ƙara aure ba. Kuma ita ce ta haifa masa duk 'ya'yansa, suna zaune ne cikin garin Kano a unguwar Tudun Yola Alhaji Tahir babban ɗan kasuwa ne Allah ya ba shi tarin dukiya. Yana da manya manyan shaguna a kantin-kwari da Singa duk dake cikin garin Kanon Dabo, Babban ɗansa shi ne Muh'd Mujahideen, wanda suke kira Jaheed, sai AbdulMalik, Umar Faruk, sai Aliyu Haidar, 'yar autarsu kuma mace ɗaya ita ce Maryam,  wacce suke yi wa laƙabi da Ameesha domin ta ci sunan kakanta ne wacce ta haifi Alhaji Tahir, Allah Ya ɗaurawa Alhaji Tahir son Ameesha ko da wasa ba ya ƙaunar ganin ɓacin ranta, tun lokacin da take ƙarama duk rashin kunyar da ta yi maka, baka isa ko kallon banza ka yi mata ba, ballantana a kai ga maganar duka ko zagi, to a ranar ba zaman lafiya don an taɓa masa 'yar lelensa, haka yasha zuwa makarantar su Ameesha ya zabgawa malaman rashin mutunci. Don kawai ta yi laifin an yi mata hukunci, shi ya sa tun tana ƙarama abin da ta yi niyya shi take yi, babu daman wani ya yi magana sai Alhaji Tahir ya soma faɗa yana cewa an sawa yarsa ido, ko da kuwa Ummiee ce da yayyinta su ka yi mata magana a kan wani abu da take haka yake rufe ido ya yi ta zuba ruwan masifa, shi ya sa Sangarta kala-kala Ameesha ta iyi, babu mai magana. wannan abu yana yi wa Hajiya Halima takaici, sai dai bata da yadda zata yi da ya wuce Addu'a. Har zuwa lokacin da ta girman ta bata rage ko abu ɗaya daga Halayyarta ba, sai ma rashin mutuncinta da yake ƙaruwa a kulluyaumin.

                 ***

    Fitowar ta kenan daga cikin Shahad store, inda ta yo Shopping ɗin duk wani abu bu da take so, idonta sanye da wani kwamemen glashi, kallo ɗaya zaka yi mata kasan babu mutunci a tattare da ita. Musamman yadda take wani irin taku cikin isa da taƙama. Hannu tasa tare da zame glashin din idonta, tana kallon motar da aka faka kusa da tata motar. Jinjina kai ta yi tana mamakin wanda ya faka motar don ya tare mata hanyar fita, tsayawa ta yi jikin motar tana jiran ganin fitowar ko ma waye mai motar, don ta nuna masa ba a yi mata haka, yau zata nuna ma duk wanda ya yi mata wannan aikin rashin mutunci. Tafiya yake cikin nutsuwa, wayar sa maƙale a kunnen sa, da gani kasan waya yake yi, isa ya yi wajen motar sa tare da buɗewa, zai shiga ciki kenan maganarta ta dakatar da shi.

    “Kai Malam dame kake ji da shi da har zaka yi mini crossing ɗin hanya, sannan ka zo ka wuce ba tare da ka ba ni haƙuri ba?”

    Ɗago da kyakykyawar fuskarsa ya yi, ya sauke idon shi a kan fuskarta, take ya ji wani yanayi ya shige shi wanda bai taɓa jin irin shi ba. Kallon beauty face ɗinta yake babu ƙaƙƙautawa. Ran Ameesha ya ɓaci matuƙa da irin kallon da yake mata, sannan ta yi magana bai amsa mata ba, ba ta jira komai ba ta ɗaga hannunta tare da kai wa fuskarsa mari. Saurin gocewa ya yi bata same shi ba, ransa ne ya ɓaci har shi ma bai san lokacin da ya ɗaga na shi hannun ba tare da zabga mata wani lafiyayyen mari. Cikin kausasa murya ya fara magana “Ke wacce iriyar mahaukaciya ce da har zaki ɗaga hannu da sunan marin fuskata?”

    Buɗe ido ta yi cike da tsananin mamakin marin da ta ji saukarsa ba tare da zato ba, a iya saninta rabon da wani ya ɗaga hannu da sunan dukanta ballantana a kai ga a mareta tun tana primary 3, shi ma malamin sanadiyyar dukan da ya mata ya bar koyarwa a school ɗin, cikin sauri ta zaro wayar ta tare da dailing numbers ɗin Abbanta cikin kuka ta soma zayyane masa abin da ya faru...

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now