ARBA'IN

2.5K 129 0
                                    

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

 
                  *40*

Bedroom ɗinsa ya nufa, sai da ya soma rage kayan jikinsa sannan ya faɗa toilet ruwa ya watsawa jikinsa, bayan ya fito ya gabatar da sallah, jikinsa ya shafe da mai tare da feshe ko ina da turarr, kayan bacci ya sanya sai ya bi lafin gado bakin sa dauke da addu'a, bai wani dade ba bacci ya yi a won gaba da shi, mai cike da mafarkin Ameesha. Kiran sallar asuba ya  farkar da shi, mika ya yi tare da addu'a kana ya nufi toilet ya dauro alwala, bai ta yar da sallah ba sai da ya je dakin Ameesha wacce ke sharar bacci, a hankali ya matsa inda take tare da kai lallausan hannunsa  fuskarta yana mata waiwayi.

Buɗe idonta ta yi mai cike da bacci, ta zuba su bisa fuskar Dr.

"Lokacin sallah ya yi tashi ki yi."

Mika ta yi tare da hamma alamar dai bacci bai isheta ba, ta amsa da

"To."

Yana zaune har ta  shiga ta fito, sannan ya jasu sallah suna idarwa Ameesha ta sanyaya murya ta ce

"Ina kwana Dr!"

"Lafiya lau Heartbeat fatan kin tashi lafiya ya sabon waje?"

Murmushi ta yi kanta a kasa ta ce "Alhamdulillah!"

"Madallah! Yanzu dai nasan kina da buk'atar hutu, je ki kwanta ki huta zuwa anjima."

Mik'ewa ta yi ta nufi gadon, shima Dr gadon ya nufa ya kwanta cikin hikima ya jawota jikinsa tare da rungumota, kamar zai mai da ta ciki duk da son jiki irin na  Ameesha amma ganin yadda Dr ya cusata jikinsa sai ta fara k'ok'ari janye jikinta, shi kuma ya ki barinta, gajiya ta yi ta barshi  a haka bacci ya kwashe su.

Basu farka ba sai karfe tara, Dr ne ya soma tashi sannan Ameesha bed ɗinsa ya nufa don yin wanka, shaf shaf Dr ya yi wanka ya fita, kai tsaye bangaren Aneesa ya nufa.

A hakimce ya ganta zaune kan kujera, ko sallamar da ya yi kin amsa masa ta yi

"Kin tashi lafiya?"

Banza ta kuma masa, bai yi zuciya ba ya kuma faɗin

"Kin yi break ne?"

Mtsss ta ja tsaki ta ce

"Ina ruwanka da break ɗin na? Kai dai ba kana can tare da matarka ba, kaga kenan rashin yin break na ba matsalar ka ba ce." Tana dire maganar ta yi shigewarta bedroom.

Tsayawa kawai Dr ya yi yana kallon Aneesa, tun yana mamakin halinta zuwa yanzu har ya daina, nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da kaɗa kai ya fita.

Mota ya ɗauka ya fita, don nemo masu abin da za su ci, bai ta de ba ya dawo, wannan karon ma falonta ya shiga, mika mata tek away din ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fita, yana jin lokacin da ja tsaki.

A bangaren Ameesha bayan Dr ya fita itama toilet ta shiga wanka ta sillo daure da towel gaban madubi ta yi masauki, duk ilahirin jikinta ta shafe da mai kafin ta nufi wordrop da niyyar dauko kayanta, sai jin sallamar Dr ta yi take wani irin kunya ta kamata, motsi ma kasawa ta yi don kunya.

"Heartbeat baki gama shiryawa ba?" Shiru ta yi ta kasa ko da ɗago kai.

Ganin taki magana yasa ya karasa inda take yana faɗin

"Kinga Wallahi yunwa nake ji fa kuma nasan kema haka Please bari na shirya ki." Ya yi maganar yana sa hannu cikin wordrop ɗin, kaya ya dauko mata riga da siket da pant and bra, aje su ya yi kan gado tare da riko hannunta.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now