BABI NA GOMA

2.2K 129 3
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
                  
                      *10*
"Abba gaskiya abin da kake son aikatawa bashi da kyau, ka dubi girman amintar dake tsakanin ku da Abban Ameesha, amma Abba yau har kai kake son yin amfani da ɗiyar sa don cimma wani buri na..."

Wata muguwar tsawa ya daka masa, ransa a matuk'ar ɓace ya katse Najeeb cikin sauri.

"Kai Najeeb har ka kai matsayin da zaka zauna kana min wa'azi? To bari ka ji Allah yasa Masallaci ne kai ,ba malami ba tashi kabani waje tun ban tsinka maka mari ba."

Tashi Najeeb ɗin ya yi yana faɗin

" Allah ya huci zuciyar ka Abbana."

Dogon tsaki  Alhaji Mansur ya ja tare da shigewa bedroom ɗinsa.

Najeeb na fita bangaren Mominsa ya shiga, zama ya yi a falon tare da dafe kai, don kwata kwata tunanin sa ya kulle ,da yana da yadda zai yi tofa lallai da ya hana mahaifinsa aiwatar da wannan mummunan aikin.

Sai dai bashi da wannan damar don mahaifinsa ya kasance mutum ne mai mugun ra'ayi, duk abin da ya yi niyya tofa sai ya cimma biyan buk'atar sa.

Haka Najeeb ya kasance cikin tunane tunanen yadda zata kaya, shi dai yasan a wannan gaɓar tabbas ya kamu da don Ameesha so kuma na gaskiya, bawai na yaudara ba.

**************************************

(" Asmad noi haa jotta minanai ad'on wolwa hala yahugo Adamawa da yald'e bangal d'on badita lutti burai sati tatii.") " Asmad har yanzu ban ji kana maganar zuwa Adamawa ba, ga lokaci nata gabatowa yaufa kwata kwata bai fi sati uku bikin ba amma, baka ko maganar zuwa."

(Nanne wii Asmad binni.)  ce kewa Asmad maganar.

(O wo'ini jode mako dendenta o lorni hakkilo mako do Nenne owii.) Gyara zama ya yi tare da maida hankalinsa kacokan kan Nanne yace

(" To Nenne jotta saito miyahi Adamawa? Minna mi anda tomi andino da miyahino miwarti.")  Yo Nanne wai a haka har Adamawa zanje, ni ai ban yi wannan tunanin ba, da tuni naje ai."

(Nenne d'oiliti moo) Harara ta yi masa cikin wasa,ta ce

( "Nananam 6ingel, jotta ad'on numa na saito a yahi ha Aneesa maan? To dei on narrata be mako?" )" Kuji min yaro , yanzu kai kana tunanin ba sai kaje wajen Aneesa ba? To kenan ta ya zaku fahimci juna?"

(" Allah Nenne sina gam awolwi mii tammai saito miyahi,  amma jotta de a hirliti aam der satii do miyahan.") " Allah Nanne ban da yanzu da kika yi maganar ban san sai naje ba, amma tunda haka ne insha Allah cikin satin nan zan yi k'ok'arin shiga."

(" Yawwa barkantejo yahu Allah wanne barka.")   Yawwa ɗan kirki ka k'ok'arta ka shiga ɗin Allah ya yi albarka."

("Amin") "Amin Nanne."

(Asmad noti d'on lara agogo jungo mako.)  ya amsa yana kallon agogon hannunsa.

("Nanne hami yaha Asibiti gammi d'on momi wanni *CS* o badeke fintugo.") "Nanne bari na tafi asibiti don akwai wacce nayi wa *CS* to ta kusa farkawa."

("Allah wallu Nenne wii.") "Allah ya taimaka."

Nanne ta faɗa.

Mintina goma suka kai shi asibitin, a parking space ya paka motar sa, wasu takaddu ya kai hannu zai ɗauko kamar ance ya ɗago kai, sai kuwa idon sa ya sauka akan su.

Kara buɗe ido ya yi sosai, tabbas itan ce suke hira da saurayi da alama tana jin daɗin hiran musamman yadda take ta sakin murmushi, kana kallon su zaka gane su ɗin masoya ne, shi duk gani ganin da yake mata bai taɓa koda ganin tayi murmushi ba, amma gashi yau har dariya take, ji ya yi ransa ya sosu da ganin da ya mata haka.

_*( A'a ikon Allah, kuji shiga uku takabar suruki, inji Kamala Minna, in ba shiga uku ba ina ruwan Asmad da Ameesha? To ko dai ko dai..... bari nayi shiru don ban tabbatar ba.)*_

A fusace ya fita daga motar cikin zuciyarsa yana dana sanin zuwan sa asibiti a dai dai wannan lokacin, tabbas da yasan irin wannan gamon zai yi gaskiya babu abin da zai kawo shi.

Office ɗin sa ya shiga, sam bai samu sukuni ba a wannan rana, don hoton su kawai yake gani kota ina, tsaki kam har ya yi babu adadi.

Haka dai ya yi ta duba majinyatan nashi, duk don ya manta dasu amma ina kamar ma yanzu suke zaunen haka yake gani.

Su kam bama su san ya na yi ba, don hiran su suke sha irin ta masoya, Najeeb ne ya kawowa Ameesha ziyara har asibitin, karkashin wata bishiya suka zauna sai hira suke zubawa, sosai Ameesha ta kamu da yawa, bata k'aunar abin da zai raba ta da Najeeb don tana masa wani irin so ne.

Sun daɗe suna hiran kafin su ka yi sallama, shi ma badon sun so rabuwa da juna ba, Najeeb ya soma wucewa ita kuma ta kuma shiga ciki inda Meena ke jiranta

"Kai Meesha hala da ba zaku rabu da juna ba ne ? Kin shanyani Bros Abdul sai kirana yake."

"Ki bari kawai Meena wallahi in Ina tare da Najeeb bana k'aunar abin da zai gifta da sunan katse mana jin daɗin mu."

" Yana da kyau haka, yanzu dai tashi muje lokaci kan ya tafi sosai."

Meena ta k'arasa maganar tana ɗaukar jakarta, Meesha ma jakarta ta ɗauka sannan suka nufi inda motar Ameesha ya ke, suna zuwa shima Asmad na zuwa don shi ɗin ma gida zashi ya gaji da takaicin da yake tunawa

" Dr sai gobe."

Meena ce mai maganar,ita Madam ko kallon sa bata yi ba tayi shigewarta mota.

Murmushi ya yi ya ce

" Allah ya kaimu."

Tsaki taja tare da bama motar wuta ta juyo ta kalli Meena ta ce

"Ke kam kin fiye cusa kai ba k'warjini, wannan miskilin kikewa magana?"

" Babu wani cusa kai, yanzu ke fisbilillah ya da ce mu wuce ba tare da munyi sallama da shi ba?"

" Yo Ina ruwan biri da gada?"

Tayi maganar tana watsa hannu irin ko a jikina

Gyada kai Meena tayi cikin zuciyarta ta ce

"Allah ya shirya min ke."

Meesha kam bata kuma magana ba,don wayarta ta ɗauko ta kunna wak'a ,ita ma shiru ta yi har suka iso kofar gidan su Meena , buɗe kofa Meena ta yi ta ce

" To ta Najeeb! jikam sai gobe in Allah ya kaimu."

" Allah ya kaimu, don Allah ki zomin da han out ɗin nan na Chemistry, don gobe school zamu shiga kuma test jibi."

" Ok zan fito maki da shi ɗin."

Meena ta kai karshen maganar tana nufa get ɗin gidan su.

Meena tana wu ce wa, sai ta soma duba wasu takaddun ta ,duk ta duba motar babu ,da sauri ta kira Meena ta ce bata gansu ba, fitowa Meena ta yi ta ce "ki koma asibiti, muje ina raka ki."

"No Meena koma gida kawai bari na koma asibitin."

Ta ida maganar tana juya kan motar ,gudu take yi kai tsaye  asibitin ta shiga don babu tantama a cen ta zubar, addu'a takeyi Allah yasa ta gani.

Tana shiga ta faka motar cikin sauri sauri ta fita , cikin ta shiga ta dudduba amma bata gani ba,  bayan ta gama duba duk inda take saran ganin takaddun amma bata gani ba. Sai kawai ta dawo gurin motar jiki a mace, ji take kamar ta kwanta ta yi ta birgima da ƙafafuwanta kamar dai yadda yara suke yi idan abu ya ɓata masu rai sosai. Ta kai hannu jiki a mace da niyyar buɗe motar sai ta ji magana kamar daga sama.

" Lafiya ki ka dawo?"

Ta juyo kamar ta k'wala ihu, rasa abin da zata ce ta yi,sai ta zuba ma sa ido game da langaɓar da kai gefe hawayen da ta ke ɓoyewa , suka ziraro.

Mamaki ya kama Asmad,duk irin tsiwarta,yau kuma ita ce ta koma haka. Sai kawai ya  yi murmushin da yake k'arawa fuskarsa kyau , buɗe wani file ya yi ya zaro takardun tare da mik'a mata.

_*Yar Mutan Rano*_

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now