BABI NA SHA BAKWAI

2.1K 136 0
                                    

*SANGARTA*

                        ©
       *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Besty*

_*Ina taya dukkan Musulmai murnar sallah, Allah ya amsa ibadunmu Ubangiji ya sa muna cikin yantattu da wadinda aka yiwa gafara Allahumma amin*_

_ina cigiyar Baseera Sabo Nadabo! Please baiwar Allah ina kika shiga haka?_

*My Besty ke kam dama ta dabance, a lokuta da dama har rasa kalmar da zanyi amfani da ita yayin nuna maki  zallar farin ciki da kulawar da kike min nake yi, amma duk da haka ina maki fatan alheri, Allah ya baki miji na gari Ubangiji ya nuna min auran ki muzo mu kwashi shokiiii*

''' Happy sallah Uncle HASSAN ATK & Uncle HUSSAIN ATK''' inji Sweet *SAFWAN* fatan kunyi sallah lafiya Allah ya maimaita mana na baɗinbaɗaɗa

                 *17*
Zuru Ameesha ta yi tana kallon sa.

Shima Asmad ɗin zuba mata ido ya yi cikin wani irin yanayi.

A hankali ya girgiza kai, a zuciyar sa  yace " *Lossing memory?* " Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un. Ashe maganar a bayyane ya yi ta sai jin muryar Meena ya yi ta ce

"What Dr Meesha tayi lossing memory? Hasbinallahu wani'imal walkil, Inna lillahi!

Haɗa rai ya yi yace " Please Meena kiyi shiru domin ban tabbatar ba."

Faɗin haka ke da wuya, sai ya nufi kofa da niyyar fita, zuciyar sa cike da tausayin halin da ta tsinci kanta a cikin.

Bai ko kalli su Abba ba, ya ce

" Alhaji bari na ɗauko wani abu a office."

Ita ma Ameesha maimaitawa ta yi, tana mik'ewa tsaye da sauri ta isa inda Asmad yake tayi saurin rik'o hannunsa  ta kankame, sai kuma ta bata fuska.

"Cike da mamaki, haɗe da mutuwar jiki, Alhaji ya bi Ameesha da kallo, saboda yadda yaga ta kamkame hannayen likitan. Wannan bakon al'amari ne a rayuwar."

A hankali Dr ɗan fullo ya zame hannayen sa daga rikon da ta yi masa, ya zaunar da ita bisa gadon ya kalleta zuciyar sa  a karye kamar zai zubar mata da hawaye "Zauna ina zuwa kin ji ko? Ya faɗa a hankali cikin dakin fuka. Ita dai kallon da ta yi wannan karon bata yi magana ba.

Wani murmushi ya saki, aiko sai ita dinma ta yi murmushin, kallon su Abba ya yi ya kuma maida kallon sa kanta, in har ya fahimta dai dai to Ameesha yunwa take ji, don haka sai ya ce

"Meena taimaka mana da tea please! Dr Asmad ya faɗa.

To kawai Meena ta amsa sannan ta soma haɗawa, cikin kankanin lokaci ta mika masa, shi kuma ya mikawa Meesha, ita dai Ameesha zubawa cup din ido tayi tana kallo don bata san ya zata yi da shi ba. Kamo hannunta ya yi yasa mata cup din ya ce

"Princess sha tea kina jin yunwa ko?

Cup din ta rike sannan ta maimaita abin da ya faɗa ɗin. Ita bata sha ba kuma bata aje ba.

Wani tunanin ya yi sai ya ce "Meena haɗa wani tea din ki zauna kusa da ita, sannan ki fara sha."

Yadda ya ce kuwa haka ta yi tana sanya cup din sai itama Ameesha ta kai baki, ta kurba sai ta aje shi a baki ta kasa haɗiyewa, don bata masan haɗiyewar ake yi ba.

"Meena ki kuma kurba sai ki hadiye ta gani." Dr ɗan fullo ya yi maganar.

Cikin ikon Allah kuwa sai Ameesha ta yi yadda Meena ta yi har saida ta shanye tas ta saki gyatsa. Sai ga zufa ya soma keto mata.

Murmushi ya yi irin mai nuna farin ciki.

Ji yowa ya yi ga su Ummi wanda suka yi jugum, suna kallon ikon Allah.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now