TALATIN DA TARA

1.9K 114 2
                                    

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                      *38*

    "Au dama Dr Asmad ne ya yi maki wannan walak'ancin?"

     "Eh! Abbana." Meesha ta bashi tabbaci.

     "Ai ko sai na nuna masa kurakuransa tunda ya taɓa min uwata."

    "Yawwa Abba wallahi ka nuna masa kurakuransa, har yau idan na tuna marin raina yakan ɓaci, kuma fa shi ne sanadin da na daina zuwa sahad yanzu."

      "Yi hakuri 'yar Abbanta tabbas Dr bai kyauta ba, don haka zan dau mataki, tashi ki ci abinci."

     "Bari na je na yi wanka tashina daga bacci kenan ko wanke baki ban yi ba."

    "A fito lafiya, amma don Allah Mamina a daina baccin yamma."

Dariya sosai Ameesha ta yi jin yadda Abba ya yi maganar, kamar wani marayan yaro

      "Na daina in sha Allah."

    "Allah ya yi albarka, je ki fito ina nan tare za mu yi dinner."

Amsawa ta yi tana tattaka matakalar benen. A jiyar zuciya Ummi ta saki, domin tun ɗazun ta suma da jin maganganun Abba da 'yarsa, gyara zama ta yi tare da maida hankali kan Alhaji Taheer ta ce

    "Alhaji da gaske mataki zaka ɗauka kan Dr Asmad?"

   "Me kika gani?"

   "Na ji  kana tabbatarwa da Auta ne, to wallahi Allah tun wuri ka sake tunani, wannan SANGARTAR da kake nunawa Auta sam ba abin arziki ba, kai yanzu ko shawara aka baka sai ka ɗauka Alhaji?" Cikin sanyi take maganar.

Murmushi ya yi irin tasu ta manya ya ce

    "Haba Halima! Ai karen hauka bai cijeni ba, da har zan ce zan ɗauki mataki akan Dr Asmad, ba Dr ba wallahi ko wanine babu abin da zan masa, kin san menene hikimar amsa mata zan dau mataki?"

Girgiza kai Ummi ta yi idonta na kan fuskar Alhaji Taheer.

    "Saboda yanzu uwata ta zama hukuma sai da lallashi, yanzu da ace ba haka na ce mata sanin kanki ne da yanzu bata bar kuka ba, to kin ji dalilin amsa mata, ai  kaf duniya uwata bata da wani miji sama da Dr Asmad."

Murmushin nasara Ummi ta yi ta ce

     "Madallah! Da maigidana abin alfahari na, tunanin ka abin sone ga kowa, Allah ya tabbatar da Alhairi."

     "Hhhhhhhhh! Tunanina? Ko tunaninki? Ai yanzu duk wani abu da nake aiwatarwa ke ce SILAH, a da bana gane karatun da ki ke min amma yanzu Alhamdulillah! Allah ya maki albarka."

    "Amin." Ummi ta amsa sannan suka ci gaba da hira, a haka Meesha ta same su, kai tsaye dining suka nufa domin yin dinner, sai a time ɗin Haydar ya dawo gida.

Bayan sun gama cin abinci, Ameesha suka ci gaba da hira ita da Abba rabi duk nusiha ne, ta yadda zata kula da Dr, domin cikin hikima da basira Abba ya tabbatar mata da aurenta da Dr babu fashi, domin dai Dr Alhairi ne a gare su.

Bayan duk ta gama jin bayanin Abba, sai ta mik'e cikin zallar SANGARTAR ta fashe da kuka,  harda bubbuga kafa kamar dai wata karamar yarinya, da gudu ta kwasa ta yi sama cikin fushi.

Duk yadda Abba yaso ya shawo kanta abin ya gagara sai kawai ya barta.

Da niyyar da safe zai lallasheta

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now