TALATIN DA UKU

2.1K 116 1
                                    

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                      *33*

"Dr ka kula da menene a wajen ca." Ya yi tambayar idon akan Asmad.

Dr Asmad bai kalli Dr Ansar ba idonsa yana kan computer yana nazarin abin dake k'wak'walwar  Ameesha, kusan minti biyu tukun ya sauke a jiyar zuciya ya ce

      "Dr duk iya nazari na ban gane ko menene ba." Har a lokacin yana kallon computer.

Murmushi kawai Dr Ansar ya yi yana zomming na pic na photo, sai ga wajen ya fito fes, zaro ido Dr Asmad ya yi cike da mamaki ya ce

     "Da fatan yanzu ka ga komai?" Ya yi maganar yana ci gaba da daddana wa.

       "Yes! Dr na ga komai har na gane abin da ke wajen."

       "Me ka gani kenan?"

        "Jini ne kwance a wajen, ga shi nan." Dr ya yi maganar yana nuna cikin computer.

         "Tabbas jini ne ka duba da kyau yana motsa wa daf yake da gangarawa cikin k'wak'walwar ta, kuma da zarar ya ida shiga babu tantama haukace wa zata yi."

     "What! Dr ya faɗa da karfi.

     "Yes! Abin da na faɗa ma gaskiya ne, domin wannan ciwon da kake gani ba karamin illa garshi ba, AMNESIA babban cuta kenan sosai yake mai da mutane mahaukata  amma ita nata da sauki kawai manta baya ta yi sakamakon wannan jinin dake cikin k'wak'walwar ta, amma da zarar an cire shi tunaninta zai dawo, sai na yi mamaki da  duk fayal din da ka kawo babu mai makamancin irin wannan, mu kuma a binciken farko mun gano asalin inda matsalar ta ɓullo."

   Jinjina kai Dr ya yi yana kara yadda da kudurar Ubangiji, ya yadda da ci gaban kasashen duniya wanda har zuwa yanzu Nigeria bata da kashi biyu bisa uku cikin masu ci gaba ba, cikin lokaci ƙalilan har an gano ciwon da aka yi kusan wata uku ana fama, ya tabbata da kudi na sayan lafiya da Abban Ameesha ko nawa zai iya sawa ya saya mata, sai dai shi lafiya wani kyauta ne daga Allah madaukakin sarki, yau ga shi cikin karfin ikonsa ya kawo su idan zata samu waraka   _(Allah ka kara mana imani da tsoronka, Ubangiji kara mana son Annabi Muhammad.)_

         "To Dr yanzu yaushe za'a shiga da ita don wanke jinin, bana son ya gangara gaskiya."

         "Kar ka damu bari mu shiga office sai mu tattauna maganar, yanzu bari mu ci gaba da bincike ko zamu gano wani abun." Yana maganar ne yana bubbuga kafadar Dr Asmad.

   Dr Asmad bai kuma magana ba, sai ci gaba da kallon computer,
Sun dauki time cikin wajen kafin Dr Ansar yasa suka koma office don ba suga komai ba, wani daki yasa a kai Ameesha allura ya umurci nuser su kuma suka fita.

Dr ne zaune shi da Dr Ansar wanda keta rubuce rubuce, kusan minti biyar sannan ya ɗago da kai yana kallon Dr Asmad
 
       "Tunda an yi saurin gano matsalar zuwa gobe sai a yi mata aiki ma'ana a wanke jinin dake cikin k'wak'walwar ta."

       "Eh! Haka ma ya yi don burina da na iyayenta bai wuce ganin ta dawo normal ba."

        "In sha Allah zata koma dai dai duk da aikin babban ne, dole sai an hada da addu'a." Cikin karfafa masa gwiwa Dr Ansar ya dire maganar.

       "Kullum addu'a ana yin sa sai dai akara."

      "Nan zata zauna gobe da karfe biyar na yamma za'a shiga da ita tiyata."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now