TALATIN DA HUDU

1.9K 123 2
                                    

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*  
    
'''Har abada bazan manta da Alhairin ku a gareni ba, tabbas ba dan kuba wallahi da yanzu babu sauran maganar labarin SANGARTA, amma kasancewar ku a wajena yasa ku ku ka assasani har labarin ya kawo yanzu, ina kara godiya a gareku Allah ya saka maku da mafificin Alhairin sa ameen da ku nake

KHADIJAH S MUHAMMAD ( Bestyna)
           &
BADEEYAR ADAM (Beauty Queen) Allah ya barmu da k'aunar juna'''

*Dedicated to LAIFIN WA & SANGARTA FANS* ina son ki sosai😍😍😍

                      *34*

Da sauri Nenne ta kara damke hannun, cikin zuciyarta tana tasbihi ga Allah a haka duk jikin Ameesha suka fara motsi

      "Alhamdulillah!" Nenne tafa murya a bayyane.

Ummi da sai a lokacin ta kula da sauri ta matso tana faɗin

"Kamar tana motsi ko?"

"Eh! Bari a kira Dr." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa.

    "A'a zauna kawai bari na kira shi." Ummi ta dire maganar tana fita daga dakin ranta fes.
               
Lokacin da Ummi ta  sanar masu duk sun ji dadi, suna addu'ar Allah yasa ta warke kenan, babu kamar Dr da ya ji maganar kamar anyi masa bushara da aljanna, sujada ya yiwa Allah don nuna jin dadin sa, ji ya yi kamar ya ri ga kowa ganin Ameeshar sa, sai  dai yana kunyar su Ummi, lokacin da ya dawo tunaninsa wayam yaga wajen ma'ana har su Abba sun tafi ganin Ameesha kenan? Ya yi maganar shi ma yana nufa dakin.

Su kam su Abba kusan a tare suka shiga, kan gadon duk suka nufa tare da zuba mata ido,

        "Dr ashe ta farka?" Abba ya tambaya.

       "Eh! Ta farka yanzu, sai dai akwai buk'ata ta samu hutu."

     "Ku yi hakuri ku dan bani waje." Dr ya yi maganar yana nufa wajen gadon, ya soma duba ta ganin numfashin ta ya dawo normal,   sai dai bata buɗe ido ba, ganin haka da Dr Ansar ya yi sai  ya ce

     "Kin farka?"

A hankali ta soma buɗe ido har ta bude su duka, ta daura idonta akan na Dr Ansar tana masa wani irin kallo na mamaki, sam Dr bai damu da haka ba.

farin  ciki ne ya kama Abba da su Nenne ai da sauri suka shiga ɗakin, ganin an turo kofar yasa Ameesha saurin daga kai tana kallon masu shigowa bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi

     "Alhamdulillah! Autar Ummi." Ummi ta yi maganar cikin farin ciki.

     A karo na biyu ta kuma buɗe ido  ta zuba su kan fuskar Ummi, ko kadan bakinta bai motsa da sunan magana ba.

Gaba daya suka fita sai Nenne kawai aka bari a daki,  Nenne bata yi musu ba domin babu mamaki Ameesha ta farka tana bukatar wani abu babu kowa.

A inda suke Dr ya same su "Abba ina son magana da ku a office." Dr Ansar ya yi maganar yana tafiya, bayan sa suka bi Ummi da Abba da Bobbo, sai Dr Asmad da ya bisu a baya.

A hankali likitan ya zare farin gilashin da ke fuskarshi, lokaci d'aya kuma ya tattara hankalinshi a kan Su Abba da suke zaune su ma hankalinsu a kanshi.

"Ita cutar Amnesia cuta ce da take samuwa ta hanyar duk wani abu da zai taba Kwakwalwa sannan a rasa hankali gabadaya, musamman idan kai ya bugu sosai. Lokacin da mutum zai dawo hankalinshi sai ya manta dukkan wasu abubuwa da suka faru  da shi. Wannan ita ce ake kira Amnesia."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now