BABI NA BAKWAI

2.5K 134 1
                                    


SANGARTA

©
ZULAYHEART RANO

7

Nanne ɗan murmushi ta saki, tana mamakin yadda maigidan nata yake farincikin sanar mata da maganar, ita ma nan take ta ji ta ƙosa ya sanar mata zaɓin da aka yi wa Asmad ɗinta.

"Aneesa na masa zaɓi, don nasan ita ce kaɗai zata iya zama da shi cikin mutunci."

Kara gyara zama Nanne ta yi, da jin zaɓin da aka yi wa Asmad, wani kyakkyawan murmushi ta saki, wannan shi ne burin da ta jima da shi a ranta, sai dai ta yi shiru ne don kar ta shiga haƙƙinsu, sai ga shi mijinta mai dogon tunani, shi ma ya yi irin nata nazarin."

Murmushi ta kuma sakewa a karo na biyu, wannan karon bakinta yaƙi rufuwa, cikin jin daɗi ta ce

"Allah Ya sa Albarka cikin wannan haɗin, Ubangiji Ya kaɗe fitina, Allah Ya ba su zama lafiya da zuri'a tagari."

"Allahumma amin, Hajiyar Asmad ga dukkan alamun dai wannan maganar ta yau ta yi maki daɗi?"

"Sosai kuwa Alhaji, ai wannan abin farin ciki ne, zumuncin mu da Hamma Bashir zai ƙara ƙarfi, lallai na ji daɗin hakan Allah Ya tabbatar da Alhairinsa."

Haka suka ci gaba da hiransu, cikin jin daɗi.

*************************

Ameesha ce zaune cikin falon su, waya ce a hannunta da alama game take yi ko chat, Haidar ne wato Yayanta wanda take bi mawa ya shigo falon da sallama.

Ta yi saurin ɗago da kai ta ce

"Yawwa Ya Haidar, wallahi tun ɗazun zaman jiranka nake."

Harara ya banka mata cikin ɗaure fuska, Allah Ya yo Haidar da iya haɗa fuska, baya ƙaunar raini ko kaɗan, ballantana kuma Ameesha da take da rawan kai.
"Kai Ya Haidar daga magana sai ka soma min harara to na fasa."

Zama ya yi yana faɗin
"Kin yi wa kanki, tashi ki kawo min abinci."

"Kai don Allah ni fa game nake yi, kuma ina tashi zasu cinye ni."

A shagwabe Ameesha ta ƙarasa maganar.

"Ba zaki tashi ba kenan?"

Ganin mugun kallon da yake watsa mata yasa ta miƙe, komai sai da ta haɗo masa sannan ta aje masa a gaba, komawa ta yi kan kujera ta lafe, cike da jin takaicin yadda Haidar ɗin ya mata.

" Yawwa ƙanwata kin san mene ne? Zo ki ji?"

Haidar ne ya yi maganar, wannan karon fuskarsa a sake take, kamar ba shi ba.

Banza ta masa tare da ci gaba da buga game ɗin.

"Meesha my lovely sister zo ki ji please? "

Kallon inda yake ta yi tare da turo ƙaramin bakinta ta ce

"Ba yanzu ka gama min masifa ba, kuma kaƙi tsayawa ka ji abin da zan ce."

"Oh! Sorry my sister, faɗi in ji mai kike so? "

Murmushi ta saki ta ce

"Dama so nake in ce maka laptop ɗina ya lalace, ji ya da zan dawo daga school."

"Yanzu ya kike son a yi?"

"Abba nake jira ya dawo, sai in amshi kudi sai ka sayo min sabo, tunda wancen ya tashi aiki."

"Je ki ɗauko in gani." Ya yi maganar yana aje plet ɗin.

Ta miƙe da zumar tafiya, sai ta ji sallama a ƙofar falo, amsawa ta yi tare da tambayar "Waye? Daidai lokacin ta isa ƙofar.

SANGARTA COMPLETEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora