ASHIRIN DA TAKWAS

2.1K 127 1
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username *ZulayheartRano89*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Wannan page din sadaukarwa ne ga NAFEESA ANKERH (mr korafi) na sadaukar maki da shi ki yi yadda zaki yi dashi idan ma kika ce kar kowa ya karanta wannan ikon ki ne, ni dai kawai a barnin in inke yin typing a time da na samu dama hhhhhhhhh!, Fatan Alhairi a gareki Zulayheart Rano tana yinki sosai*_ 😍😍

                       *28*

Daddaɗar muryarta ne ya ratsa kunnuwansa, musamman yadda ta faɗin sunan sai ya ji ta saukar masa da kasala, dadingushi kuma yadda ta lafe a jikinsa, sai wani feeling wanda tunda yake da Meesha duk fadawa jikinsa da ta keyi, bai taɓa jin irin saba, gyara mata zama ya yi a maimakon da da yake zameta daga jikinsa ya ce

"My Meesha ya ki ke?"

Bata ce komai ba sai lumshe ido da ta yi, fuskarta har yanzu da murmushi, Meena kam tsayawa ta yi tana kare masu kallo don yadda Dr ya yi ko wanda bai san SO bane ya gansu to zai iya shaida su ɗin masoyan junane, murmushin farin ciki ta yi a ranta tana faɗin

"Alhamdulillah! Ashe Dr ma yana son Meesha Amma wannan abu ya min daɗi."

Ganin hankalin Dr yana ga Ameesha bai masan da wata Meena ba sai ta ɗan gyaran murya ta ce

"Dr ina wuni! An daura aure lafiya?"

Wata kunya ce ta kamashi, don da farko yaga lokacin da suka shigo tare da Meena ɗin, amma tunda Meesha ta matsa inda yake sai ya manta da komai ya maida hankalinsa kan Ameesha.

"Lafiya lau Meena ya kuke?"

"Duk muna lafiya." Ta bashi amsa tana tafiya.

Meena tana wucewa ya maida hankali kan Meesha da ke ta daddana wayar Dr ɗin. Ya ce

"My Meesha zaki bini gidanmu?"

Da sauri ta daga kai alamar "eh!"

Murmushi ya yi ya ce "to bari Abba ya dawo, sai na kaiki wajen Nenne ku gaisa." Ya ida maganar dai dai da zuwan Meena, abin motsa baki ta shiryo masa.

"Thanks Meena sannu da k'ok'ari."

"Your are welcome!" Ta faɗa tana tafiya. Shi Dr tunda Ameesha ta wanzu kusa da shi sai ya nemi yunwa ya rasa, don kasancewarta kusa da shi ba karamin farin ciki ne a gare shi ba.

Kallon ta ya yi tana ci gaba da danna wayarsa, cikin zuciyarsa fadi yake

"Ina ma ace Ameesha tana cikin tunanin ta aka daura masu aure! Lallai yasan da ace tana tunanin ta, to yau da abin ya fi masa jin dadi, amma a haka ma yana farin ciki, yana godiya ga Allah."

Dr ya manta da komai ya dauki lokacin da kacokan ya dankawa Ameesha, sam ya manta a gidan surukai yake, soyayya kawai yake nuna mata irin mai tsayawa arai dinnan, ya yin da ita kuma ta wani lafe a jikinsa kamar wani ya ce zai raba su, bai tashi farga ba sai da ya ji kiran sallar magriba, ɗago da ita ya yi yana faɗin

"Meesha time for prayer, zan je masallaci."

Da kallo take binsa don bata fahimci inda maganar sa ta dosa ba, ganin zata bata masa lokaci har ya rasa jam'i yasa ya kira Meena yana sanar mata to zo ta tafi da Meesha, babu bata lokaci sai gata, da wayau Dr ya samu ya guje mata.

****

Aneesa kam tana shiga dakin wani sabon kuka ta fashe da shi, zuciyarta tana wani irin zafi tana jin kishin Dr fiye da komai, zata iya yin komai don ta hana Dr zama da amaryar sa, yadda take kukan Ni kaina sai da na tausaya mata, don *kishiya ko ta kashin dankali ne babu daɗi*  balle wacce aka auro don ku zauna a karkashin inuwar mutum ɗaya.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now