TALATIN 30

2.2K 122 0
                                    

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

''' Wannan page din kyauta na baki RUFAIDA OMAR fatan Alhairi a gareki da zuri'arki baki daya, Zulayheart Rano tana yinki sosai Allah ya kara maki basira da kaifin k'wak'walwa na fasihiyar marubuciya mai baiwar fikira da Nagarta'''

                      *30*

Tsam ya rungume ta cikin jikinsa, yana kallon yadda take fusgar numfashi da kyar! Duk tausayinta ya cika shi. ɗago da kai ya yi ya ce

"Nenne bani ruwa da towel a goge mata jiki zafin zai ragu." Yana maganar ne yana kuma tallabar ta.

"To." Nenne ta amsa tare da fita. Cikin sakan ashirin har ta kawo masa ruwan, koda ta  ba shi fita ta yi don ta ba shi waje. Yana ganin Nenne ta fita sai ya yi saurin kwantar da ita, ya zame rigar ta cikin nutsuwa yake bin jikinta da jikakken towel din yana manna mata, jikin dai har lokacin da zafi amma numfashi ya daidai ta.

Rasa yadda zai yi da ita ya yi, domin shi a wannan lokaci ya manta shi fa Dr ne, sai zuwa can wata basira ta fado masa cikin sauri ya kuma rungumota ya cusata a jikinsa ya soma murza mata baya ahankali, ya yi kusan minti sha biyar kafin ya ji zafin jikin ya koma daidai.

A lokacin kuwa har bacci ya yi gaba da Ameesha, a hankali ya zame jikinsa ya gyara mata kwanciya. Fita ya yi ya dauko first aid kit ɗinsa, allura ya haɗa ya yi mata. Ya zauna a gefenta yana kallonta fuskarsa ɗauke da damuwa, sosai yake jin Ameesha a zuciyarsa baya k'aunar koda 'kuda ne ya sauka jikinta balle aje ga batun ciwo.

"Sannu Asmad har ta samu bacci kenan?" Muryar Nenne ya ji.

"Eh! Ta samu yanzu." Dr ya bata amsa.

"To ya kamata dai ka tafi gida, domin dare yana kara yi fa, yanzu tara harda rabi." Ta dire maganar tana kallonsa.

Jikinsa sam babu kwari ya mike yana faɗin,

"To Nenne sai da safe duk yadda ake ciki da safe sai ki sanar min, duk da nayi mata allurar saukar da zazzabi." Cikin sanyin murya ya yi maganar.

"Allah ya kaimu, insha Allahu za ta samu sauki zuwa safen ma." Cikin karfafa masa gwiwa ta yi maganar.

Fita Dr. ya yi badan ya so tafiyar ba. Da tunanin Ameesha ya isa gida, ko da ya shiga cikin falon babu kowa don haka bai tsaya ba sai ya nufi bedroom ɗinta. Kwance ya same ta kallo ɗaya zaka mata kasan ba bacci take ba, zama ya yi kusa da ita yana faɗin

"Madam har kin kwanta?"

Wani mugun kallo ta aika masa da shi tare da juya masa baya, mamaki ya kama Dr. ganin dai lafiya lau suka rabu ɗazun amma yanzu har ta ɗauki fushi

"Wai lafiyar ki kuwa?" Ya kuma mata magana.

Tsaki ta ja mai karfi ta ce,

"Ina ruwan ka da lafiyata? Ba wajen amaryarka ka je ba? Ita wato ka damu da damuwarta? Amma ni da yake baka kaunata baka damu da halin da zan shiga ba, ai shi yasa ka yi tafiyar ka sai yanzu kake dawowa anya ma kuwa Hamman kana tsoron Allah?"

Murmushi mai ciwo ya yi ya ce, "Ki yi hakuri duk yadda kike tunani ba haka bane, amma ki yi hakuri." Daga haka yasa kai ya fita.

Domin dai zafin karshen maganar Aneesa basu da maraba da saukar tafasasshen ruwa a jikinsa, ya barta mata dakin ne don karda zuciya ta sashi aikata mummunan aiki. Amma tabbas maganar ta ta bata ransa, duk iya kokarin da yake akanta bata gani, yana lallaɓata ne ba dan komai ba sai su Nenne amma yau har ta iya bude baki tana fada  mishi *Yana tsoron Allah kuwa*. Ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta, "Aneesa kenan kinci daraja ɗaya amma karki bari laifin ki ya kara girma, domin dai  akwai babban laifin da kika aikata min mafi muni amma na barki ne har zuwa lokacin da zan baki mamaki.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now