TALATIN DA BIYAR

1.8K 113 1
                                    

*SANGARTA*

  
                        ©
           *ZULAYHEART RANO*
My Wattpad username
*ZulayheartRano89*


    *Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                      *35*

So take ta tuna wani abu, sai dai sam k'wak'walwa ta ta kasa tunowa, Meena ta kula da haka sai kawai cikin sauri ta ce

      "Kin manta ranar da muka je sahad, kika ga turaren har ki ka ɗauka! Duba sunan ki gani Obsessed sunansa."

    "Meena Obsessed! Ameesha ta maimaita sunan da wata irin murya.

     "Yes! Shi fatan kin tuna?"

A hankali lokacin da ta saya turaren ya fara dawo mata, sai dai ta kasa tuna wani abu bayan shi, kanta ne ya yi wani irin sarawa

        "Wash! Ta furta a fili

       "Mu je ki yi wanka kafin Abba ya zo."

      "Abbana? Ina Abba yake Ummi fa?"

       "Duk za ki gansu, yanzu dai ta shi ki yi wanka."

Da kanta ta yi wanka, ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, sosai kayan sun yi mata kyau, Nenne ta haɗa mata shayi domin babu abinci cikin dakin, Dr Asmad ya tafi kawowa.

    "Na gode! Ta faɗa tana kai cup bakinta, tas ta shanye tana aje cup din ta furta

     "Alhamdulillah!"

Murmushin nasara Nenne ta yi, domin kuwa tabbas ta yadda Ameesha ta fara samun lafiya, tunda gashi har tana abubuwa da kanta.
   
     "Ga wayar ki Ummi zata yi magana da ke." Meena ce ta yi maganar tana mik'awa Meesha wayar.

Amsar wayar ta yi tana kallon ta, sai kuma ta ɗago kai ta zubawa Meena ido, kafin ta yi magana sai jin sallamar su Abba suka yi, cikin masu amsawa har da Ameesha, wacce ta yi saurin tashi tsaye tana faɗin

      "Abbana ina Ummi?" Ta kai karshen maganar tana fadawa jikinsa, don sam bata kula da Ummi ba balle su ya Jaheed.

   "Kai masha Allah autar Ummi ta samu sauki, ga Ummin ki da su Jaheed." Abba ya faɗa yana dagota.

   Kallon su ta yi tana ganin Ummi da sauri ta nufeta ta rungume ta cikin zallar farin ciki

Duk sun ji dadin ganin yadda ta koma, hira suka shiga yi ita dai Ameesha tana jin su, bata furta komai ba domin bata fahimtar inda hiran tasa gaba, a haka Dr Asmad ya yi sallama lokacin idonta a lumshe yake, jin sallamar sa yasa ta yi saurin bude ido domin dai take ta dauki muryar sa.

Fes ta sauke idonta akan fuskarsa, wani kallo suka wa junansu mai cike da ma'anoni daban daban, murmushi Dr ya saki tare da fadin

        "Princess kin tashi?" Wani kasala ta saukar mata jin muryar sa, bata iya bashi amsa ba sai lumshe ido da tayi tare da buɗewa.

Kana kallon Dr zaka iya fahimtar yana cikin zallar farin ciki, da kansa ya zuba mata abincin ya mika mata, amsa ta yi har a time ɗin bata daina kallonsa ba.

Haka dai a hankali sauki ke samuwa ga Ameesha har aka yi kwana uku, a lokacin Dr Ansar ya ce zai sallame su, tunda zuwa yanzu ta fara tuna wasu abubuwan a hankali zata tuna komai.

Suna zaune dukan su, kanta yana saman cinyar Nenne ta yi kamar tana bacci, su kam dama hira suke zumbur kamar an tsikare ta ta mik'e tana waige-waige

         "Ummi Ina Najeeb?"

     "Najeeb kuma? Wanne Najeeb ɗin?"

      "Ummi Najeeb mana yaron Alhaji Mansur abokin Abba?" Ameesha ta fada tana gyara zama.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now