BABI NA UKU

3.6K 186 2
                                    

3

“Wa ye ubansa a north Nigeria da har zai kai hannu fuskar ki da sunan duka?” Kai da jin yadda yake maganar ka san a zazafe ya yi ta.

Ɓangaren Ameesha kuwa hawaye ne suka cigaba da zuba tamkar an saki famfo, domin kuwa ba ƙaramin shigar ta marin ya yi ba. Don haka murya a sanyaye ta fara magana, “Abba ba ɗan kowa ba ne hasalima shi ɗin wani ƙasƙantaccen mutum ne, wanda ba shi da ko sisi, Motar da yake hawa ko kyauta aka ba ni ba zan iya hawanta ba.” Ta dire maganar tana ƙara fashewa da kuka.

“Maza ɗauko mini lambar motar, zan yi maganin kowaye shi.”

Ɗago kan da Ameesha za ta yi sai taga wayam! Babu motar babu kuma mai motar, wani tuƙuƙun baƙin ciki da takaici ne suka taru suka lulluɓeta, “Abba ya wuce ban san ma lokacin da ya wuce ba.” Ta faɗa cikin takaici.

“Maza ki dawo gida, ko in zo in ɗauke ki ne?” Ya faɗa cikin sigar lallashi.

“No Abba ba sai ka zo ba yanzu zan dawo.” Ta gama maganar tare da buɗe mota ta shiga ciki, a ranta ta ƙudirta ba za ta ƙara zuwa Sahad store ba, domin a yanzu wajen ya zamar mata wajen jin kunya.

Cikin gida kuwa Abba sai kai komo yake, sai jan tsaki yake yi mtswwww! Don kuwa hankalin shi ya tashi matuƙa da jin maganar abin da ya samu Ameesha, Hajiya Halima da ta fito daga kicin ta tsaya tana kallon maigidan nata, har za ta wuce sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, don haka sai ta fara magana cike da kulawa “lafiya kuwa Alhaji?”
Bai tanka mata ba sai ya ƙara sakin tsaki tare da aikawa Ummiee harara, sannan ya fara magana  “Yo ina fa lafiya Hajiya? Wai daga fitar yarinyar nan, har an samu wani ɗan-iskan ya zazzabga mata mari, ta ya hankalina zai kwanta ban ga dawowarta ba.
Cike da mamakin furucin shi na ƙarshe ta fara magana “Wai wace aka mara ne?”

“Inada wata 'yar ce bayan Uwata? Ya cigaba kin ga Hajiya karki kuma ɓata mini rai, dama fa na kula tun farko baki so fitan yarinyar nan ba, don haka burinki ya cika tun da an wulaƙanta mini ita a waje.” A masife ya ba ta amsa.

Girgiza kai Ummiee ta yi, ita dai har kullum lamarin mijinta yana ɗaure mata kai, wani lokacin idan ya yi abu sai ta ji kamar ta rufe shi da duka, zuciyarta na tuƙuƙi ta fara magana, “Ni kam Alhaji abubuwanku yana ba ni matuƙar mamaki, musamman idan ka faɗi wata maganar, ta ya za ka ce wai na ji daɗi saboda an wulakanta Ameesha? Karka mata fa ni na haife Ameesha, kuma banƙi ace Ameesha ta fi kowace 'ya mace nutsuwa ba, na tabbata Ameesha babu ta yadda za a yi wani ya ɗaga hannu ya mareta ba tare da ta yi masa komai ba, wata ƙila ma irin rashin kunyar da saba da yi ne ta yi masa ta yi masa shi ya sa ƙila ya mareta, amma kai ba za ka yi bincike ba, sai dai ka yanke hukunci ka ɗaura laifi a kan wai mutum daban kuma magana ta gaskiya ba hakan babu kyau.”

Ɗaga mata hannu ya yi alamar ta yi masa shiru, daidai lokacin Ameesha ta shigo, kai tsaye jikin Abba ta faɗa tare da sakin wani sabon kukan.
Bubbuga bayanta Abba ya soma yi alamar rarrashi ya fara yi mata magana cikin rarrashi “Yi haƙuri Uwata karki bar wannan ya dame ki, In Sha Allah zan ɗauki mummunar mataki a kan koma waye shi, duk ranar da Allah Ya haɗamu.”

“Da zan baka shawara ka ɗauka, to da sai na ce  ka bi komai a hankali zai fi, amma wannan maganar da kake ba shi ne daidai ba.” Ummiee ta yi maganar tana zama a kan kujera.

“Haba Ummiee kin ga kuwa irin wulaƙancin da ya yi mini, da har kike cewa a bi komai a hankali, wallahi Abba karka bi a hankali.”

“To uwar rashin kunya, da ke na yi magana? Da har kike cewa kar ya bi a hankali? To shi kenan ku je ku yi, na tabbatar wata rana sai kun yi nadamar duk abin da kuke aikatawa nadamar ma mara amfani.”

“Ni fa wallahi Hajiya bana son irin wannan maganar da kike yi, ke kullum bakinki ba ya furta Alhairi a garemu kullum sai mugun baki, to wallahi ta Allah ba ta ki ba.”

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now