BABI NA TAKWAS

2.3K 126 0
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

              *SANGARTA*

                      ©
      *ZULAYHEART RANO*

   Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad my Cittah

                 8
Kallon Asmad ɗin Nanne ta yi don ganin irin zaburar da ya yi ta ce

“Lafiya kuwa Asmad? Ko zaɓin ne bayyi maka ba?”

Saurin daidaita nutsuwarsa ya yi, da ya tuna fa a gaban Nanne yake, ya fara magana cikin ƙasƙantar da murya

“Haba Nannena ta ya zan ce zaɓin ku bayyi mini ba? Kawai dai gani na yi kamar Aneesar ba za ta yarda da haɗin ba.”

Murmushi Nanne ta yi cikin jin daɗi, da samun Asmad ɗin matsayin ɗa don bai taɓa jayayya da duk wani umurnin su ba, koda hakan bayyi masa ba amsa ya ke ba tare da ya nuna ɓacin ransa ba.

“Haba karka damu ai Aneesa 'yar'uwar ka ce, kuma da amincewar mahaifinta hakan zai faru, don haka ka yi haƙuri da zaɓin In Sha Allah za ka yi alfahari da shi.”

Gyaɗa kai kawai ya iya yi, tare da miƙewa ransa a ɗan ɓace don bai so wannan zaɓin ba, to amma tun da Bobbo shi ya yi masa ya zama dole ya yi biyayya.

Kai tsaye yana fita daga falon Nanne, ɓangarensa ya shiga kan kujerar dake falonsa ya faɗa yana ambaton Allah, da Ya kawo masa ɗauki cikin wannan baƙon lamarin da ya kunno masa kai, abin da ko  mafarki bai taɓa tunanin gani ba. Amma yau sai gashi ido buɗe ya ji kuma ya gani, da sauri ya miƙe tunawar da ya yi yana da shiga CS a daidai wannan lokacin.

Bedroom ɗinsa ya shiga, ya watsawa jikinsa ruwa, bayan ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya riga da wando, bai koma falon Nanne ba sai ya nufi motarsa, ba kuma don wannan maganar ce ta hana shi komawar ba, a'a ganin da ya yi lokacin ya kusa, har ya buɗe mota zai shiga sai kawai ya fasa, ya zama dole ya je ya yi wa Nannensa sallama, domin bai saba fita ba tare da ya yi sallama da ita ba.

Asmad ke nan yaro mai neman albarkar iyayensa.

***********************************

Ameesha na shiga cikin falo, bedroom ɗin Ummi ta zame, wannan karon Ummin ta idar da abin da take yi

“Ummiee na dawo.”

Cewar Ameesha tana zama abakin gadon ɗakin Ummiee.

“Madallah! Sannu da dawowa, har ya tafi ne?”

“Eh, Ummi.”

Ta bata amsa a takaice.

Ɗan juyo wa Ummiee ta yi ta kalli Ameesha, ganin ta kwanta sai kawai ta girgiza kai, a ranta ta ce

‘Allah Ya shirya mini ke Ameesha, yarinya kullum ciki zurfin ciki. Da Abban tane da yanzu ta soma ba shi duk labarin abin da ya faru, amma ji yanzu ko ta sanar mini yadda su ka...’ Maganar Ameesha ya tsinka mata tunaninta.

“Ummi wai kin san waye ya zo wajena?”

Ameesha ta yi maganar tana ci gaba da latsa wayarta.

“Ta ina zan sani Ameesha, ni da ko falo ban leƙa ba har kika dawo?”

“Najeeb ne yaron Alhaji Mansur abokin Abba, shi ne ya zo.”

Ameesha ta yi maganar ba tare da ta ɗago kai ba.
Ɗan ware ido Ummi ta yi cikin mamakin jin abin da Ameesha ta faɗa

“Najeeb kuma? To mai ya ce maki?”

“Ya ce zai dawo in ba shi rana, shi ne na ba shi.”

“Allah Ya tabbatar da Alhairi.”

SANGARTA COMPLETEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora