ARBA'IN DA BIYAR

1.8K 102 0
                                    

*SANGARTA*

              
                     ©
    _*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                 *45*

A firij ɗin kicin ta sanya sannan ta fara aikinta hankali kwance, tafashen nama ta ɗaura bayan ta wanke, yana fara taushi ta sauke sannan ta haɗa masa kayan hadi lokacin an shiga sallar la'asar don haka ita ɗin ma bedroom ta shiga ta gabatar da sallar, bayan ta idar ta koma ta ci gaba da aikinta, dambun shinkafa ta yi masa sai farfesun naman rago da sansanyan abin sha. Ƙarfe biyar saura ta kammala aikin ta jera komai akan dining bayan ta gyara kicin ta wanke duk kayan da ta yi amfani da shi.

Falo ta koma ta kara gyara duk inda ya kamata ta turare shi da turaruka masu ƙamshi da daɗi gabaɗaya gidan ya cika da ƙamshin abincin tare da na turare, cikin sauri ta faɗa toilet don ganin lokacin shigowar Dr ya kusa, wanka ta yo ta mulke jikinta da mayuka masu ƙamshi cikin wata riga ta shirya wanda iyakar sa cinya, santala santalan cinyoyinta duk sun bayyana sosai ta yi kyau duk da ba wani make up ta yi a fuska ba. A falo ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana canza tashoshin t.v. kamar a mafarki ta soma jiyo fitinannan ƙamshin turaren Dr wanda ya yi sanadin da ta lumshe ido wani irin feeling ya saukar mata, tana jiyo takun shi ta yi saurin tashi tare da nufa ƙofar.

Dr na buɗewa Ameesha ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi, cikin siririyar murya ta ke faɗin "Baby sannu da dawowa." Bai amsa ba sai ƙoƙarin yakice ta daga jikinsa ya fara, ita kuma ta ƙi sakin shi sai ma kukan sangarta da da fara yi masa, sam ya kasa tankwara zuciyarsa akan kar ya sauka daga fushin da yake da ita, ɗaukarta cak! Ya yi ya ƙarasa shiga falon da ita. Sam Ameesha ta ƙi barin kukan kuma ta ƙi ɗagawa daga jikinsa, shafa sumar kanta ya soma yi cikin wani irin salo ya kasa magana sai zuwa can ya ce "Haba Cutie kukan ya isa haka kar ki bata mini kwalliya ga yi ko gani ban yi ba." Da taushin murya ya yi maganar. Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarta ta kara lafewa a ƙirjinsa tana ci gaba da shessheƙa. "Ba na ce kukan ya isa ba?" Wannan karon a ɗan hasale ya yi maganar.

"Ni dai ba zan yi shiru ba sai ka faɗa min laifin da na yi maka kake yin fushi da ni?" Da shagwaɓaɓɓiyar murya ta yi maganar. Kiss ya yi mata a kumatu ya ce "Wannan maganar ya wuce tuni na bar yin fushi dake, domin ba zan iya ba duk kuwa da girman laifinki."
"Laifi na Wallahi ban san na yi maka laifi ba baby ka yi haƙuri ka yafe mini In Sha Allah ba zan ƙara ba."  Ta gama maganar sabbin hawaye suna zubowa.
"Kin yi mini laifi Cutie wanda yasa har na ƙasa ɓoye fushi na." "To ka yi haƙuri ka yafe min." "Na haƙura Allah Ya yafe mu baki ɗaya." Amin ta amsa tana ɓalle masa botirar rigarsa, kwashe kayan ta yi ta kai masa bedroom sannan ta haɗa masa ruwan wanka, ita ta taimaka masa ya yi wankan ya shirya sannan suka fita falo.

Ameesha da kanta ta rika ciyar da Dr har ya ƙoshi, kwashe kayan ta yi ta kai kicin sannan suka koma kan three sitter, soyayyar su su ke Ameesha ta kuma narkewa a jikin Dr ta yi ƙasa da murya ta ce "baby wai wane laifi na yi maka da ka kira shi mafi muni? Ina son sanin laifi na domin gujewa sake aikata maka irinsa nan gaba." Shafa kanta Dr ya yi cikin soyayyar ta da ta yi masa yawa ya ce "ki bar tuna min Cutie wannan fa ya wuce kuma bana fatan na ƙara kamaki da makamancinsa, a wajen ki ba babban laifi ba ne domin ban san manufar ki ta yin haka ba, amma ni a wajena babban laifi ne Maryerm." Ya ɗan takata da maganar sa, jin ya yi shiru sai ta ɗago kai ta kalle shi ta ce "In Sha Allah ba ni kumawa amma ina son jin sunan laifin."
   "Hmmmm! Dr ya saki ajiyar zuciya ya ce "Maryerm kina shan maganin hana ɗaukar ciki saboda karki  wahala wajen haihuwa ko?" Wani irin zabura Ameesha ta yi murya na rawa ta ce "Maganin hana ɗaukar ciki baby?"

"Yes Ameesha da idona na gansu ranar da kanki ke ciwo na je ɗauko maki magani ." Ya dakata da maganar yana kallon Ameesha, saurin mayar da hawayen ta ta yi sai dai duk da haka mamakin maganar Dr bai bar fuskarta ba, ta dai kasa magana don bata da kalmar kare kanta tunda ya gani da idonsa kuma cikin kayanta.

SANGARTA COMPLETETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang