BABI NA SHA TAKWAS

2K 117 0
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Gaskiya dai bani da bakin da zan ce wani abu domin kuwa masoya wannan littafin kun gama min komai, ko da yaushe ina samun sakonnin ku masu text message da masu kirana ta waya, fatan alheri nake maku ina jin dadin addu'oin ku, masu korafi kuyi hakuri wannan Nobel fa yanzu aka fara matukar dai kuna bina a hankali zaku fahimci komai,  AMEESHA ma tana godiya da addu'ar ku.*_

                     *18*
Rike masa hannu ta yi gam, sai zarrare ido take kamar wacce taga wani abin tsora. Dr ɗan fullo kuwa kunya ce ta kamashi da sauri ya ja hannunta zuwa bakin gadon yana faɗin "Princess kin tashi? Barka da safiya!

Shiru ta yi ta dai zuba masa ido tana kallon bakin sa, murmushi ya saki don ya fuskanci halin da take ciki.

Mai da duban sa kan su Ummi ya yi ya ce
"Hajiya Princess fa yunwa take ji, matukar kuka ga ta natsu bata maimaita magana abu biyu ne ko dai yunwa ko kuma bata jin dadi."

"Insha Allah zamu kula, bari a bata shayi tunda babu abinci mai ɗan nauyi." Ummi ta yi maganar tana kokarin jawo flask. Sai ko ga sallamar yayyinta gaba daya, Ya Jaheed ne a gaba sauran suna binsa a baya. Kallo ɗaya ya yi masu ya shaida su ɗin yan'uwan tane musamman muguwar kamar da suke yi. Ita kuwa da kallo Ameesha ta bisu kamar idon zai fado, zuwa can kuma sai ta lumshe ido.

"Autar Ummi sannu ya jikin?" Abdul ya yi tambayar yana matsawa kusa da gadon.

Bata buɗe ido ba, amma ta maimaita abin da ya faɗa.

Hawaye ne yake tsiyaya daga idanuwansu, suna matukar tausaya yar'uwar tasu wai Ameesha autar Ummi ce cikin wannan halin, lallai ikon Allah ya fi gaban wasa. Kuka sosai Abdul ya yi domin dai dama shi ne abokin kaftawarta to kuma yanzu ga yadda Ubangiji ya maidata.

"Kunga bafa kuka za ku yi ba, ku yi mata addu'a ne." Ummi ta kai karshen maganar cikin kulawa ci gaba da fifitawa Ameesha shayi.  Share hawayen su  su ka yi sannan suka soma gaida iyayen nasu, Ya Jaheed ya mikawa Dr ɗan fullo hannu suka gaisa "Dr ya mai jiki?"

"To jiki Alhamdulillah sai godiyar Allah."

"Allah ya bata lafiya!"

"Amin." Dr ya amsa yana mikawa Ummi takardar sallama domin Abba ya fita daga dakin ya ce zuciyarsa zata iya bugawa matukar dai yana kallon Ameesha a irin wannan yanayin, ko a jiya da kyar ya kawo safe don yadda zuciyarsa ke masa wani irin zafi. Ummi kam amsa ta yi tana masa godiya, lokacin shayi ya ɗan huce.

"Auta amsa ki sha! Tayi maganar tana  mika mata cup din  amma fir taki amsa, juyin duniya amma ta ki, Abdul ne ya je ya kira Dr. Tare suka dawo da  shi,  yana zuwa ya amsa ya kai bakin sa sannan ya mika mata yana faɗin
.
"Amsa Princess ki sha kin ji?" Babu musu ta amsa tare da kaiwa baki kamar yadda Asmad ɗin ya ce.

Kafin ta gama sha har sun gama kwashe kayan su daga ɗakin.

Wajen tafiya gida ma da kyar aka lallaɓa ta, don tirjewa ta yi ita fa adole babu inda zata je sai tare da Asmad, to shi dinma yana alhinin rabuwa da ita, sai dai bai nuna ba don karda su yi tunanin wani abun.

"Please Dr ko zaka taimaka mana ne ka kasance gida?" Muryar ya Jaheed kenan.

"No  babu damuwa, domin ni ma gida zan ta fi." Dr ya ba shi amsa.

"Mun gode sosai Allah ya bar zumunci." Ya ida maganar yana nufa inda su Ummi su ke.

"Ummi Dr ya ce zai kai ta gidan tunda kinga fa bata yadda da kowa sai shi."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now