BABI NA SHA TARA

1.9K 127 0
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*Saboda yadda ki ke son wannan Nobel din yasa na baki kyautar wannan page din na yau, MARYAM BINTU hakika kin cancanci fiye da haka, amma ki yi haquri da wannan, fatana Allah albarkaci rayuwarki Ubangiji ya rabani da sharrin makiya, YAR MUTAN RANO tana k'aunar ki har cikin ranta.*

'''Masu korafin in bude groups, don Allah ku yi hakuri ba sai na buɗe group daban ba, a kawai groups na yan'uwana da yawa, irin su UMMYN YUSRAH NOVEL, MARYAM MUKHTAR FAN GROUP, da dai sauransu duk ina post a ciki, ba sai na buɗe ba, ina godiya da shawarwari Allah ya barmu da k'aunar juna.'''

                     *19*
Sadda kai k'asa Najeeb ya yi, cikin zuciyarsa yana mai tsantsan jin takaici da halin mahaifinsa. Muryar Alhaji Mansur ya ji yana faɗin "tashi ka bani waje shashashan banza kawai, kuma dole ka yi yadda na ke so , ko kuma wallahi ranka ya yi mummunan ɓaci."

Jiki a sanyaye ya mike bai nufi inda sashin sa yake ba, sai ya nufi wajen motarsa ya ɗauka, cikin nutsuwa ya tashi motar bai zame ko ina ba sai gidan Alhaji Taheer. Ya yi parking sannan ya k'arasa cikin gidan.

A babban falo ya samu su Abba zaune suna hira da Ummi, gefe guda kuma Ameesha ce ke kwance akan three sitter. Cikin sakin fuska Abba ya amsa masa sallamar da ya yi.

Tsugunawa ya yi har kasa ya ce

"Ina kwana Abba ya mai jiki?"

"Lafiya lau Najeeb  mai jiki ta ji sauki, ya su Alhajin?"

"Yana lafiya ya ce a gaida ku!

"Muna amsawa."

Kansa ya kuma saddawa da alama magana ya ke son yi. Abba ya fahimci haka

"Kamar kana son yin magana ko?" Alhaji Taheer ya tambaya.

"Eh! Abba. Ya bashi amsa

"Ok ina jinka." Ya ida maganar yana maida hankalinsa shi.

  "Ehm uum! Dama kan maganar Ameesha ne, Abba don Allah karka fasa bani ita, wallahi zan iya aurenta a ko wane hali take."

Murmushi Abba ya yi cikin jin daɗi da maganar Najeeb ɗin, don har cikin zuciyarsa yana tunanin yadda lamarin zai kasance, musamman daga halin da Ameesha ta samu kanta a ci, amma yanzu Alhamdulillah tunda ga Najeeb yana jaddada masa son da ya kewa Ameesha ɗin.

"Haba karka damu da wannan insha Allah Ameesha taka ce, bata da wani miji da ya wuce kai."

"Na gode Abba." Ya yi furucin cike da jin dadi.

Kallon agogon hannunsa ya yi tare da mik'ewa, don tuni Ummi ta bar falon

"Najeeb zan fita! In ka koma ka gaida su Hajiyar." Ya kai karshen maganar yana fita.

Shi kuma matsawa kusa da ita ya yi ya ce

"Meesha ya jikin?"

Idonta biyu amma in ba ka duba da kyau ba sai ka ce bacci ta ke yi, ko da  ya yi maganar tana jinsa amma da yake yan maimaita maganar basu kusa ko ɗago kai ta kalleshi bata yi ba, domin dai wannan muryar bata saba jin taba, ita kuma so take ta ji irin wanda ta saba ji. Haka ya gaji da magana ya tafi.

Yana fita Meena ta shigo falon, ganin ta ita ɗaya a kwance sai ta matsa tana faɗin

"Meesha ke ce kawai a falon?"

Bata yi magana ba sai buɗe dara daran idonta da ta yi tana kallon Meena ɗin. Gyara zama Meena ta yi tare da sanya game a wayar Ameesha, kuma shi ne game din da Ameesha ta fi so akan ko wanne. Zuba wa wayar ido ta yi tana kallon yadda Meena ke buga game ɗin, har wani murmushi ta ke yi alamar abin ya mata daɗi, ganin haka sai itama Meena ta ji dadi.

"In baki kema ki buga?"

Bata fahimci me Meena ta ke nufi ba, don haka sai ta ci gaba da kallon wayar, mika mata wayar ta yi , amma sai ta bata rai, cikin sauri ta kamo hannun Meena ta daura akan wayar alamar dai ta ci gaba da bugawa .

Da ta fahimci nufin ta sai kawai ta ci gaba da bugawar, haka suka kasance cikin farin ciki, domin dai a duniya Meena tana son farin cikin Meesha.

*************************

Aneesa ce zaune a can kuryar gado, ta zabga uban tagumi kai da gani kasan cikin tunani take, can dai ta sauke tagumin tare da jawo wayarta dake dan nesa da ita. Number ta lalubo sannan ta danna kira ringing biyu aka daga wayar.

"Hello k'awata gaskiya fa ina cikin wani mawuyacin hali." Ta yi maganar ciki rashin nutsuwa.

Daga ɗaya bangaren ta amsa

"Anee mai ya sameki?"

"Ki bari kawai wallahi ina cikin matsala."

"Ke nifa bani son wannan abin na, ki yi min magana sak bana don kwana kwana."

Ajiyar zuciya Aneesa ta sauke ta ce

"Kinga wai fa ciki ne da ni, kuma ke kinsan bana son haihuwa a irin wannan lokacin."

Mtsss Rukky ta ja tsaki, ta ce

"Amma wallahi Aneesa har kin bani haushi, yanzu don Allah saboda cikin ne ki ka tada hankalin ki?"

"Dole in tada hankalina duka yaushe aka yi auren? Wata fa na uku kenan, shi ne har zan samu ciki?" Ta ci-gaba

"Gaskiya dai ban shirya haihuwa ba, kuma bana kaunar cikin nan wallahi, yanzu ya ki ke ganin za'a yi?"

"Gaskiya nima dai ban baki goyon bayan haihuwa yanzu ba, don mazan yanzu da kun haihu suke daina ya yin ki, musamman irin su Dr da yanzu suke ganiyar tashen su. Akwai hanya amma da fatar bai san da cikin ba?"

"Eh! Gaskiya dai bana tunanin yasan da shi, domin da ya sani da kansa zai sanarmin don dai yana da son yara sosai."

"Gud! Haka yana da kyau, kina ji kawai ki shirya ki je asibiti sai a zubar da shi, tunda bai wani girma ya...

"Ke! Aneesa ta yi saurin katseta, ta ce "nifa nan babu inda na sani."

"Dallah! Ke wallahi baki haɗu ba, ga asbitoci nan da yawa a gari, ki bari in ya fita kema ki fita abinki, kafin ya dawo kin gama komai, kuma ai nan layinku naga wani asbiti ki gwada zuwa, ke kam wani lokacin kamar wacce bata waye ba."

"Tom shi kenan, zan gwada ɗin. Zaki ji kirana a kowane lokaci."

"Yawwa ko ke fa! Amma ki yi kokari don matukar ya fahimci kina da ciki to fa sai kin haifa masa, musamman da shi fa a gidansu shi kadai ya taso, zai so ganin jinin sa."

"Karki damu an gama."

"Sosai Aneesa ta yi na'am da  shawarar Rukky, don ita fa bata son ta rasa Dr Asmad ne, kar ta haihu ya je ya sake auro wata, ita kuma ya daina ya yinta, tana wa Dr wani irin so ne ba na wasa ba."

*( Hmmmm Aneesa kenan, wannan sam ba shawarar arziki ba ce, Allah ya baki kyauta mafi daraja amma saboda wani banzar hujjar ki ki ce baki so? Ina ji ye maki zuwan ranar nadama)*

Aiko cikin zuciyarta ta kudurci niyyar gobe yana fita, itama zata kama kanta.

     *ASBITIN MALAM AMINU KANO*

Asmad ne zaune ya zuba wani uban tagumi, tunanin Ameesha kawai ya ke yi, shi bai taɓa tunanin sonta ya kama shi haka ba, sai da wannan ciwon ya kamata, ya ji daɗin kasancewar su a asbitin, yana son Ameesha so mai tsanani amma ya rasa hanyar da zai bi don ganin ya mallaketa. Masifar sonta yake don ko motsi ya yi sai ya tuna ta, musamman murmushinta, kallonta, dariyarta, uwa uba kuma *SANGARTA* da take yi, kai komai nata yana burgeshi.

Wayarsa ya jawo ya soma buɗe pic din da ya mata lokacin da take asbiti, wasu tana bacci wasu kuma idonta biyu, wani kuma tana murmushi, yana kallon pic din yana murmushi tare da girgiza kai a fili ya furta

*Princess kin haɗu iya haɗawa, Allah ya mallaka min ke matsayin matar aure*

_Don Allah ku yi hakuri da wannan, wallahi shi din ma da kyar na tafa shi_ ''' I hearttttt you all my fans'''😍😍

_*YAR MUTAN RANO*_

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now