BABI NA TARA

2.2K 124 0
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

            *SANGARTA*

                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

     ''' Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah'''
  
                     *9*
Girgiza kai  ta yi tace

" Ayya Najeeb ai Ameesha bata soyayya, don bata iya wa da kayan takaicin da ke cikin soyayya."

Kasak'e ya yi yana kallonta, tare da mamakin furucin ta, in har hasashen da yake yi gaskiya ne, kenan Ameesha bata tab'a soyayya ba.

"Kayi hakuri Najeeb gaskiya ba zan iya amince maka ba, don ban son in jefa zuciya ta cikin halaka, shi yasa ko kadan bana ɓata wa kaina lokaci."

Tana gama faɗin haka ta yi waje.

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta tashi tafita, tabbas sai ya yi da gaske hak'an sa zai cimma ruwa, da wannan tunanin ya tashi jiki a sanyaye.

Ameesha na barin falon bak'in bedroom dinta ta shiga, hankalin ta ya tashi b'ata tab'a soyayya ba, haka kuma bata jin zata iya soyayya da wani, wayarta ta jawo ta dan nawa Meena kawarta kira.

Bayan sun gaisa ne Ameesha ke sanar mata da yadda sukayi da Najeeb din. Daga bangaren Meena ajiyar zuciya ta sauke ta ce

" Bai kamata kiyi saurin fada masa haka ba, kamata ya yi ki zauna kiyi dogon tunani akan maganar, musamman dai kin ga Najeeb ba wai mutumin banza ba ne."

" shi yasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'a yi? "

"  OK mu haɗu a school gobe. "

Daga haka sukayi sallama.

Bayan sunyi sallama ne, ta mike ta koma falo jin alamar shigowar Abbanta, ai ko shi ɗin ne yana zaune ga yayyenta suma a zaune kusa dashi, da sauri ta karasa tana fad'in
" oyo-yo Abbana welcome back."

Murmushin jin daɗi ya yi ya ce

" Thanks my daughter ya gida? "

"  Lafiya lau Abba, gaskiya nayi kewarka fa."

Ta karasa maganar cikin shagwaba.

" Zo zauna uwata, ayi min Afuwa nima ina can tunanin rashin ki kusa dani ya dameni."

Sai da ta zauna kusa da Abbanta, sannan ta gaida yayyenta, wanda suke zaune cikin jin daɗin ganin Abban nasu, a tare suka amsa cikin kulawa don suna matukar son Ameesha sosai, kasancewar ta ita ɗaya ce mace cikin su.

"Wai Abba waye naga kun tsaya da shi ɗazun da ka shigo? "

Jaheed ne ya yi tambayar.

" Najeeb ɗin ne kuma yau baka sani ba? "

Alhaji Taheer ya yi tambayar fuskar sa cike da mamaki.

Dan rufe baki Jaheed ya yi cikin dan mamaki ya ce
"  badai Najeeb din Alhaji Mansur ba?  Allah Abba ban gane shi ba, naga ya canza."

" Aiko shi ɗin ne, nima nayi mamakin ganin sa a gidan."

"yo Alhaji wajen Ameesha yake zuwa, Yau shi ne zuwansa na biyu. "

Ummi dake zuwa falon ta yi maganar. Ai Ameesha tana jin maganar Ummin ta kwasa a guje tayi stair, bata zama ko ina ba Sai bedroom ɗinta.

Da kallo suka rakata, Jaheed ya dan kada kai take ya fahimci in da maganar Ummi ta dosa, Kai kusan dukkan su sun fahimta, amma shi Jaheed tuni ya fahimci zuwan Najeeb din, don yasan ba abin da zai kawo shi wajen Ameesha sai soyayya.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now