BABI NA ASHIRIN

2K 126 0
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*I love you all SANGARTA FANS* 😍😍😍😍

Dedicated to *SHAMSHIYA SALIS*

_*Na yi mamaki sosai a lokacin da na samu labarin harda SHAMSHIYA SALIS, cikin masu bibiyar wannan Nobel din. Gaisuwa ta musamman tare da fatar alheri a gareki*

             *20*
Sosai ya mayar da hankali wajen kallon pic ɗin Ameesha, sai ko ɗayar wayarsa ta soma ruri, sunan wanda yaga yana kiran ne yasa shi ɗauka tare da karawa a kunne

"Hello abokina ya garin?"

"Lafiya lau! Aka ba shi amsa daga ɗaya ɓangaren.

"Kana ina ne?" Dr ya tambaya.

"Gani zan shigo asbiti, shi ne na ce bari na kira ko ka fita?"

Ɗan dariya Dr Asmad ya yi ya ce

"Ina office ka shigo kawai."

"To! Ya amsa ta re da kashe wayar.

Minti biyar tsakani sai ko ya ji nocking ɗin ƙofar office ɗin. "Yes shigo mana!"

Babu ɓata lokaci ya shigo, a tare suka sakarwa juna murmushi, tare da gaisawa.

"Kai Wallahi na yi farinciki da ganin ka Hafiz, domin dai ina da buƙatar shawararka."

Zama Hafiz ya yi tare da fuskantar Dr ɗan fullo, yana sauraron maganar da ya ke masa. A jiyar zuciya Dr ya sauke yana ci gaba da kallon pic ɗin Ameesha.

"Dr. Ka fara magana kuma ka yi shiru, wai me ya faru ne?"

Murmushi ya yi ya ce

"Haba Hafiz, babu fa wani abu na damuwa, shawara kawai nake nema a wajen ka."

"Ok ina sauraron ka!"

Gyara zama ya yi tare da mayar da hankali kan Hafiz ɗin ya ce

"Wato maganar dai ita ce, kasan wannan yarinyar dana taɓa baka labarinta, wacce muka haɗu a shahad store har na mareta?"

"Yes! Na gane ta, amma ban san yarinyar ba." Hafiz ya ba shi amsa.

"Ok! Mun kuma haɗuwa da ita, har ma na zama mata Malami ta fannin karatu, duk da dai a da ba wani shiri muke ba, amma a 'yan kwanakin can kafin ta samu ciwo mun fara daidaitawa, tun ranar farko da na ganta nake jin sonta, har zuwa yau ina jin kishin in ganta da wani saurayin ɓalle inga tana masa murmushi, kai a takaice dai ina mugun sonta so irin mai tsanani ɗin nan, wallahi sonta ya hana ni sukuni, kodayaushe cikin tunaninta nake, duk wannan abin bata masan ina yi ba, na yi dogon tunani ya kamata in sanar mata,  sai dai an samu matsala, domin ranar da nake niyyar bayyana mata ƙudirina sai Allah Ya gifto da wani iftila'i."

Dr. Ya yi shiru da maganarsa yana mai tsantsan tausayin Ameesha.

"Ina jinka ." Hafiz ya faɗa.

"Eh iftila'i domin dai ta samu ciwon mantau, ma'ana ta manta komai na rayuwar ta na baya, ina sonta tare da tausaya mata, ina burin ta zama matata, amma na rasa ta yadda zan yi wa su Nenne bayani."

Jinjina kai Hafiz ya yi ya ce "duk ta su Nenne mai sauƙi ne, matsalar tana ga ita yarinyar domin a yanzu komai zaka faɗa mata ba zata gane ba, hasalima bata sanka..."

"No! Hafiz wallahi tun ranar da ta samu ciwon babu wanda ta yarda da shi kamar ni, domin da ƙyar nake guje mata har kunya ta riƙa ba ni a gaban iyayenta."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now