BABI NA SHA HUDU

2K 134 1
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
                    *14*

Tsaye ya ke a kofar gidan hannayen sa rungume a kirjin sa, ya zubawa get ɗin gidan idanu, burinsa bai wu ce yaga ta fito ba , gefe ɗaya kuma yana tunanin yadda zata kaya, rabon sa da zuwa wajen ta yau kusan wata biyu kenan.

Yanzu ma nazari ya yi ya ga dai tabbas bata cancanci irin wannan hukuncin daga gare shi ba, sosai ya lula duniyar tunani,sai jin Muryar ta ya yi ta na faɗin

" Barka da zuwa, yau  a  gari, ashe talaka na ganin ku?"

Ju yowa ya yi tare da sauke idonsa a fuskarta, wanda ke ɗaure kamar bata taɓa sanin wani abu wai shi  murmushi ba balle dariya ba, take ya ji gaban sa ya faɗi da yanayin ta, da kyar ya dage tare da tattaro nutsuwar sa ya buɗe bakin sa da ya masa nauyi ya ce

" Ki yi *Rufaida* wallahi abubuwa ne su ka yi min yawa."

(Fatan masu karatu basu manta da Rufaida ba, asalin budurwar Najeeb?")

" Har suka hana ka ɗaukan  wayata?"

Ta yi saurin jefa masa tambaya, har yanzu bata ko kalli inda ya ke ba.

"No Ruffy ba shi ne yasa ba ."

" Ok ganin dama ne kenan? Ashe haka k'auna take komawa? Wallahi Najeeb ka bani mamaki ban taɓa tunanin haka daga gare ka ba"

"Kiyi hakuri Ruffy na yi kuskure, amma insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba."

" Hmmmm Najeeb kenan ai bana jin akwai abin da zaka gaya min in yadda."

"Haba Please Ruffy ki fahimce ni, kin fi kowa sani halina fa, Please ki yafe ni."

Da kyar ya lallaɓata ta yadda, da abin da ya ke faɗa mata.

"Fatar kin yafe min?"

"  Ba komai Najeeb amma tabbas kasani a damuwa, har nake tunanin na aikata maka ka dai dai ba."

" Baki min komai ba, kuma gani yanzu nazo fitar da ke." Ya karasa maganar cikin murmushi.

Itama murmushi ta saki ta ce

" Tom nayi farin ciki, amma fa Najeeb ina ga lokaci ya yi da zaka gabatar da kan ka a wajen Abbana."

" Karki damu na kusa shiga,so nake na kammala wasu abubuwa."

"Allah ya tabbatar da Alhairi."

Haka Najeeb da Rufaida suka kasance cikin hira irin ta masoya.

Sam Rufaida Allah ya yi ta bata da fushi, ko da yaushe fuskantar a sake take bama idan tana tare da Najeeb manta duk wani damuwa ta ke yi.

Shi kuma Najeeb gefe ɗaya tunanin Ameesha ne ya addabi zuciyarsa, tabbas yana don Ameesha sai dai kuma yana alhinin rabuwa da Rufaida.

Ameesha kuwa ko da ta fita a gida, ta yi tafiya mai dan nisa bata samu adai dai ta ba, ga jikinta na ci gaba da ciwo, kan wani ɗan dakali ta zauna tare da zubawa hanyar ido, duk wanda ya ganta ba zai ce ita ce Ameesha yar Abba ba, gaba ɗaya ta canza ta koma wata silet.

Tana zaune dai a wajen, tana kuma hango nafef ɗin amma ta kasa yadda zata tsayar da su,don bata saba ba,  sunkuyar da kai k'asa ta yi wasu siraran hawaye suka zubo, hak'ik'a tana son Najeeb sai dai kuma bata jin sa kamar yadda take jin Asmad a zuciyarta, ta rasa gane wani irin abu take ji ɗin game da shi... Firgigit ta yi saurin ɗagowa da kai sakamakon jin hon na mota a gaban ta.

Kallon mai motar ta yi cikin rashin sani, murmushi ta cikin motar ta yi wanda suka amshi fuskarta, cikin Muryar ta mai sanyi ta ce

" In ba za ki damu ba muje na rage maki hanya?"

Lokaci ɗaya Ameesha ta ji tana son matashiyar matar, da bazata wuce shekara ashirin da biyu zuwa da uku ba

Saurin share hawayen ta yi , don kar ta fahimci halin da ta ke ciki.

" School fa zani." Ameesha ta bata amsa.

" Wane school ɗin? don nima can na nufa."

"B.U.K"

Ameesha ta bata amsa.

" Ok shiga muje , nima can zan shiga ina da laccan safe ne."

Shiga motar Ameesha ta yi , ta zauna tana mai ambaton Allah a zuciya.

" Sunana Khadija Yaseer amma an fi sanina da *Ni'eema* fatan zamu zama kawaye?

Murmushi ta saki ta ce

" Insha Allah ni kuma Maryam Taheer wacce a ka fi sani da *Ameesha*."

"Masha Allah Ameesha Allah ya bamu ikon zama da juna cikin amana, ina da aure da yara biyu asali mu yan Kaduna ne aiki ya dawo da mijina nan, in  zan tafi makaranta ina yawan ganin ki da wata cikin mota kuna tafiya"

Murmushi ta saki don tana jin daɗin hiran da su ke yi ,gefe guda kuma tana mamaki da Ni'eema ta ce tana da yara biyu, don ba mai kallonta ya ce ta yi aure bare kuma a ce da yara, saurin kawar da tunanin ta yi ta ce

" Eh matar yayana ce , kuma kawata tare muke tafiya yau bata da laccan safe, ni bani da aure tare da iyayena na ke."

Da wannan hirar suka isa school ɗin, har a zuciya Ameesha ta ji tana son Ni'eema, har musayan number su ka yi da ita .

Da yake Ni'eema tana 300 level ne, Ameesha kuma na 200 level.

*********************************

Can kuma wajen ango da amarya an sha shagali sosai ko dinner sai biyun dare aka tashi, washe gari kuma aka buɗe asibitin Ango Asmad mai suna *A&A* special hospital asibitin da ya samu kwararrun likitoci.

Sai muyi fatan alheri ga wannan gudunmawa ga al'umma wanda Asmad da Alhaji Abubakar suka samar.

Amarya Aneesa buri ya cika fata ga Asmad matsayin miji da mata, sosai Asmad ɗin ya ke k'ok'arin sauke duk wani nauyi na Aneesa da ke kansa, duk wani tana jin farin ciki ya na bata, shi yasa cikin kwanaki kaɗan ta murje ta yi kyau sosai.

Meena ce ta haura saman Ameesha, ta kalli ta a tsorace cikin mamaki ta ce

"Meesha anya kina da lafiya kuwa?"

"Me ki ka gani?

"Meesha ki kalli yadda ki ka koma, baki magana baki cin abinci, baki da walwala ko yau she kina cikin daki ki zauna ki yi shiru, why why Meesha?"

Hawayen da take makalewa suka zubo, bata damu da share su ba ta kalli Meena ta re da sakin wani murmushi mai kama da kuka ta ce

" Meena ta ya zan samu farin ciki? Bayan farin cikin nawa baya tare da ni, ta ya zan yi walwala? bayan abokin walwalar tawa ba ta ni ya ke ba."

"Ba zan ɓoye maki ba Meena, wallahi ina cikin wani hali mawuyaci, Meena ke ce kaɗai zan iya faɗawa damuwa ta."

Meena shiru ta yi zuciyar ta cike da tausayin kawarta ta cikin sanyin murya ta ce

" Meesha faɗa min insha Allah zan yi kokarin sama maki mafita."

Murmushin takaici ta yi ta ce

" Kar kiyi mamaki inda na ce maki Allah ya jarabceni da son Dr Asm..."

_*Yar Mutan Rano*_

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now