BABI NA ASHIRIN DA UKU

1.8K 115 0
                                    

*SANGARTA*

©
*ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

*23*

"To ni ina zan sani masu, abu ɗaya dai na sani shi ne sun ɓata mini rai." Cikin takaici Ummiee ta ƙarasa maganar.

"A dai ƙara haƙuri Aunty."

"Yo ai haƙuri ya zama dole, tashi ki je wajen autar ƙila tana buƙatar wani abun."

"To Aunty." Shi ne abin da Aunty Saude ta faɗa tana miƙewa.

***********

Asmad ne kwance a ɗaki sai juye juye ya ke yi, tunda garin Allah Ya waye sallah kawai ya yi, sam baya jin daɗin jikinsa tunanin rabuwa da abar sonsa Ameesha shi ya haddasa masa wannan zazzafar zazzaɓin, duk da ya sha magani amma babu wani sauƙi.

"Sannu Hamma ya jikin?" Aneesa ce ta yi maganar tana zama a bakin gadon.

"Da sauƙi." Asmad ya yi maganar cikin ƙaramar murya.

"Allah Ya ƙara sauƙi, ko za'a sanar da su Nenne ne?"

"A'a Ba sai kin sanar masu ba, kar hankalinsu ya tashi, ai na samu sauƙi zuwa anjima zan fita."

"Allah Ya ƙara lafiya."

"Amin! Haɗa mini ruwan wanka ƙila ko na ƙara samun ƙwarin jikin." Ya dire maganar yana tashi zaune.

Cikin ƙanƙanin lokaci har ta gama haɗa masa ruwan, sannan ta fito tana faɗin

"Hamma na gama!"

"Na gode, ɗan taimaka mini."

Da taimakon Aneesa ya yi wankan, har ya shirya babu laifi ya ɗan samu ƙwarin jikin, tunda har falo ya fito ya kunna t.v .

*Yau saura kwana daya biki*

Zaune suke a falo Ameesha ce da Meena, Meena ke gyara mata gashinta kanta wanda suka je aka wanke, shi ne kaɗai abin da Ummiee ta yarda aka yiwa Meesha don ta ce 'yarta bata da lafiya abarta har zuwa lokacin da zata samu sauƙi sai a yi shagalin auren.

Meena ta kalli Meesha ta ce

"Meesha gobe iwar haka kin zama amaryar Najeeb."

"Amaryar Najeeb?" Meesha ta tambaya.

"Eh! Gobe zaki tafi ki bar mu, zan yi kewarki sosai."

Wannan karon Meesha shiru ta yi kamar mai tunanin wani abu, haka Meena ta ci gaba da mata hira amma taƙi amsawa.

"Alhaji wai kuwa kana ga yaron nan na son Auta?" Ummiee ta yi tambayar cikin takaici.

"Wannan wacce irin tambaya ce?"

"Allah Ya baka haƙuri, amma ni sam tsarin auren nan bai mini ba."

"To ni kuma ya min." Abba ya kai ƙarshen maganar yana barin wajen.

"Allah Ya kyauta, amma wannan auren ban taɓa ganin ko jin irinsa ba."

**

Yau kam jikin Dr ya yi sauƙi don har fita ya yi asbitin su, sai da ya kammala da duba marasa lafiya tunkun ya koma office, duk da yau ɗin ta kasance Lahadi ne, babu aiki amma shi Asmad ya saba ya je don duba marasa lafiya.

Office ya koma, ya zauna tare da janyo laptop ɗinsa, wani bincike yake yi akan wata ciwon, wayarsa dake gefe ta soma ƙara, ɗan tsaki ya ja don bai so a katse masa aikin da yake, sunan Hafiz ya gani .

Hannu yakai tare da ɗaukar wayar ya kara a kunne

"Hello Dr kana jina?"

"Eh! Dr ya amsa a takaice.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now