BABI NA ASHIRIN DA HUDU

2K 115 1
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                  *24*

Zama ya yi akan kujera, don duk wannan maganar da suke yi a tsaye ya ke ya ce

“Wato Halima da mutuncina da komai aka so tozarta ni, babu komai domin Allah Ya kawo canji mafi Alhairi.” Abba ya dire maganar cikin takaici.

“Alhaji ka fara magana kuma yanzu ka dauko wata, wacce ban fahimci komai daga ciki ba?” Cikin ƙosawa Ummiee ta tambaya.

“Haba mene ne abin saurin tambaya kuma? Ai gani gaki dole ne ki san komai da ke faruwa, wallahi Alhaji Mansur ya ba ni mamaki matuƙa ya dasa mini bakin ciki a zuciyata.”

Tagumi Ummiee ta yi tare da zuba masa ido tana kallonsa, har zuwa wannan lokacin bata gane ina maganarsa tasa gaba ba. Ganin ta ƙosa ta san komai sai Abba ya miƙa mata takardan ya ce karanta wannan.

Cikin sauri tasa hannu ta amsa tare da buɗewa ga abinda saƙon ya ƙunsa.

“Malam Alhaji Taheer ke nan, nasan ya zuwa yanzu kun riga da kun hallara wajen ɗaurin aure ko? To kar ka yi mamakin rashin ganina da jama'ata, don tuni aka ɗaura auren Najeeb da matarsa lafiyayya, in faɗa maka maganar gaskiya shi ne ka nema wa mahaukaciyar 'yarka miji daidai ita, amma fa ba dai Najeeb nawa ba, domin shi lafiyayye ne kuma lafiyayyar mace zai aura. Wato tun lokacin da ya kamata ka yi maganar zaka haɗa su aure ba ka yi ba sai da 'yarka ta haukace tukun ka ɓullo da maganar don kana son rabuwa da ita, sai ni kuma ka kwaso ka kawo mini gida, to ba zai yuwu ba, ni ma ba zan haɗa zuri'a da marar hankali ba, don haka ka sama mata miji daidai da rashin hankalinta, in ya so sai su yi ta haifo maka jikoki marasa hankali saƙo daga ni ALHAJI MANSUR.”

"inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shi ne kalmar da Ummiee ke maimaitawa a fili.

"Ai dama wallahi jikina ya ba ni, an so shirya mana walak'anci baccin haka ta ya za'a ƙi  kawo kayan da gidan ango suke kawowa? Tun farko abin da na guda ke nan sai gashi ya afku yanzu Alhaji ya ke nan za'a yi?
Ta ci gaba "Amma Wallahi Alhaji Mansur ya ba ni kunya ban yi tunanin haka daga gareshi ba."

“Sosai kuwa, domin ko ni lokacin da wasiƙar ta same ni, gaskiya na yi mamaki don har kiran wayarsa na yi ya kuma tabbatar mini da shi ya aikota.”

“To ai shi ke nan, tunda haka ne yanzu ya za'a yi ke nan?”

“Kamar ya fa?” Abba ya tambaya.

“Game da ɗaurin auren mana.” Ummiee ta bashi amsa.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, tare da muskutawa ya ce

"Bayan Jaheed ya gama karantawa kuma na kira Mansur ya kuma tabbatar min da shi ya aiko da takardan, sai Alhaji Usman ya ce sam haka ba zai yiwu ba, in samu wani ko da a cikin 'ya'yan yan'uwana ne a ɗaura da shi, nan ma naga ba wata mafita kada a samu cin mutuncin da yafi na Mansur, sai ga wani mutum ya nufo inda muke tsaye, shi ne fa ya tambaya me yake faruwa take muka sanar sa, sai ya ce in ba damuwa a ɗaura da  ɗansa duk da a farko na so bijirewa amma sai Alhaji Usman ya hana, nan take na amince amma fa can ƙasan zuciyata ina tunanin abin da zai je ya dawo, an ɗaura auren ASMAD ABUBAKAR DA MARYAM TAHEER, a kan sadaki Naira dubu hamsin.” Abba ya dire maganar yana sakin murmushi, wanda daga gani kasan har cikin zuciyar shi daɗi yake ji.

“Ma sha Allah Alhaji Allah Ya tabbatar da Alhairi, Ubangiji Ya sa haka shi ne mafi Alhairi a garemu da ita bakiɗaya.”

“Allahumma Amin.” Abba ya amsa

“Yanzu dai ki tashi ki je ki ci gaba da sallamar baki zuwa anjima sai mu kara shawartawa, ni ɗimma da sauran mutanen da zan sallama.” Ya gama maganar yana miƙewa tsaye.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now