ARBA'IN DA BAKWAI

1.8K 114 5
                                    

*SANGARTA*

              
                     ©
    _*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                 *47*

"Masha Allah! Nenne Meesha na dauke da ciki har na wata daya da kwanaki." Wani irin farin ciki ne ya ziyarci Nenne wanda rabonta da jin irin wannan farin cikin tun lokacin cikin Asmad "Alhamdulillah! Ta furta a bayyane fuska cike da zallar farin ciki. "Sannu da k'ok'ari Hafiz na gode da wannan kyakkyawan albishir ɗin." Meesha kam tana gama jin bayanin Dr Hafiz sai wasu hawaye na farin ciki suka soma zubowa daga idonta, hakika wannan rana ta zame mata na farin ciki domin daga wannan rana ta fita daga zargin da Dr ke mata, tana son ganin farin cikin da Dr zai yi idan ya ji tana dauke da cikinsa, gaba daya sakin baki suka yi suna kallonta don hawayen da take ba na wasa bane "haba Ameesha ke da zaki yi farin ciki sai kuma ki ke hawaye?" Hafiz ne ya yi maganar cikin sigar lallashi.

Murmushi ta yi kanta a kasa, bata jin zata iya sanar da kowa sirrinta da mijinta, don haka sai kawai ta ce "Babu komai fa Hafiz farin ciki ne kawai." Ta dire maganar tana sinne kai cikin filo. Murmushi suka yi gaba daya, sannan Dr Hafiz ya mik'e yana faɗin "Nenne zan k'arasa gida anjima zan kawo mata wasu magunguna." "Allah ya kaimu." Nenne ta faɗa da murmushi. Bayan tafiyar Dr Hafiz sai Nenne ta tsare Ameesha akan sai ta faɗi abin da take so.

"Nenne ni fa bana jin cin komai." "A'a Ameesha kin ga ki daure ki faɗa min bana son zama da yunwa balle kuma ba ke daya ba ce yanzu." "Zan rika ci Nenne faten dankalin turawa nake so." "Yawwa Yar Nenne haka nake so." Nenne ta yi maganar tana mik'ewa, da kanta ta shiga kicin ɗin ta soma haɗawa Meesha abin da ta ce tana so, faten ta yi mata mai ruwa ruwa yadda zata ji daɗin sha har da alayyahu ta yanka ciki da hanta, lokacin da ta shiga har bacci ya soma daukar Meesha, don haka cikin hikima da dabara ta tashe ta. "Sannu da k'ok'ari Nenne." Ameesha ta yi maganar tana tashi daga kwanciya. "Yawwa ta shi ki sha da zafinsa." Ruwa ta bata ta kuskure baki sannan ta   bata abaki, ba ta wani ci da yawa ba ta ce ta koshi.

Duk yadda Nenne taso ta kara dole ta barta, toilet ta nufa ta sakarwa kanta ruwa masu dan zafi don ta ji dadin jikinta, bayan ta fito kayan jikinta ta mai da domin bata da kaya a gidan, Nenne ne ta shigo ta kalli Ameesha ta ce "Har kin fito?" "Eh" Nenne sai dai "bani da kayan sawa." A shagwaɓe ta yi maganar. "Kuma fa bari na kira Asmad ya kawo maki." To kawai ta amsa tana ci gaba da wasa da zaren rigarta. Tana kallon Nenne ta fita tana waya.

Ba a fi minti talatin ba, tana kwance kewar jikin Dr take tana son ta ji dumin jikinsa, Kamar daga sama ta ji sallamar sa murya ciki ciki, da sauri ta tashi zaune tana amsa sallamar "Sannu da zuwa baby." Ta faɗa tana kallonsa. "Yawwa." ya amsa a takaice fuska babu walwala. "Ga kayanki nan da kika sanya na kawo maki, dama na kula tuni baki son zama da ni shi ne dalilin ki na shan magani, tunda ba ki son zama dani me ya kawo ki gidan iyayena?" Ya kai karshen maganar yana daka mata tsawa.

Tun kan ya gama maganar, hawaye ya soma wanke mata fuska  domin maganar sa yana daga mata hankali, murya na rawa ta ce" Ka yi hakuri ba da wata manufa nazo nan gidan ba, kuma wallahi laifin da kake tuhumata da shi bani da masaniya..."  Hannun da ya daga mata ne ya sanya ta yi shiru da maganar ta amma hawayen basu tsaya ba.

"Kinga ki yi min shiru ai kin sire min Ameesha yadda na daukeki kin bani kunya, sai an yi magana ki farawa mutane kukan SANGARTA." Mtsww ya ja tsaki kafin ya bar mata dakin. Ragaf ta faɗa kan gadon ta saki sabon kuka sam bata son irin abin da Dr yake mata, duk da yanzu tasan Allah ya wanketa to amma ai muggan kalamai Dr bai daina furta mata ba, haka ta ci gaba da kukan har bata san lokacin da Nenne ta shigo ba sai jin muryar ta ta yi "Ameesha lafiya kike kuka?" Hankali tashe ta yi tambayar.

Saurin share hawaye ta yi ta kalkalo murmushi ta ce "kaina ke min ciwo Nenne kamar zai rabe biyu." "Allah ya baki lafiya, fatan kin sha magani?" Ta yi tambayar badan ta yadda da abin da Meesha ta faɗa ba. "Eh na sha." Ameesha ta bata amsa. "Ki bar kuka zai daina." Nenne ta k'arasa maganar tana fita, cikin zuciyarta tana sanyawa Meesha albarka ta tabbata Ameesha suruka ce ta kwarai tunda har tana iya ɓoye matsalar ta da mijinta, kwafa ta yi a ranta ita kadai tasan abin da zata yiwa Dr.

Ameesha na ganin Nenne ta fita ta kuma sakin wani kukan, tana tausayin kanta da hukuncin Dr. Asmad kuwa yana fita gidan su Hafiz ya yiwa tsinke, har ya karya kwana zai shiga layin ya tuna kila Hafiz din baya gida, don haka sai ya dauko wayarsa ya kira  layinsa, ringing biyu ya dauka bayan sun gaisa ne yake tambayarsa Allah yasa yana gida "Eh ina gida ban jima da shigowa ba." "Ok gani nan zuwa." Yana gama faɗin haka ya katse wayar.

Yana fakin motar ya kara kiransa, minti biyu kacal Hafiz ya fito musabaha suka yi kamar yadda suka saba sannan Hafiz ya kalli Asmad da kyau ya ce "mu shiga daga ciki mana abokina?" "A'a ba sai mun shiga ba, sam na rasa jin dadi na gaba daya bana cikin nutsuwa." Da damuwa Asmad ya gama maganar. " Subhanallah! Dr me yake faruwa haka? Mu shiga ciki zai fi." Ciki suka shiga a falo suka yada zango, ruwa mai sanyi Hafiz ya kawo masa bayan ya sha sannan ya soma magana "Wato Hafiz Aneesa da Ameesha suna neman caza min k'wak'walwa, ko kasan duk tsayin lokacin da muka dauka da Aneesa maganin hana daukar ciki take sha?" "Maganin hana daukar ciki?" Da mamaki Hafiz ya yi tambayar. "Sosai kuwa ina tabbatar maka har cikina Aneesa ta zubar wanda take tunanin ban sani ba." "Zubar da ciki?" "Sosai kuwa." Dr ya tabbatar masa.

"Inna lillahi! Wannan wacce irin masifa ce? Kuma kana sane baka dau mataki ba" "Ban ɗauka ba sai yanzu nake son ɗauka akansu duka, domin Ameesha ma sau biyu ina ganin maganin a bangaren ta." "Au har Ameesha din ma?" Hafiz ya yi saurin katse shi. "Tabbas, na farko ranar da ta dawo daga gidansu, na biyu shekaran jiya da dare, wallahi bazan ɓoye maka ba na Ameesha ya fi bani haushi domin yadda na dauketa ba haka ta ɗauke Ni ba, abin haushi kuma tana gaya min bata taɓa sha ba ka ji wani rainin wayau bayan na gani da idona..."  "Amma Dr ka binciki na Ameesha kuwa? Ban ji ajikina Meesha zata ma haka ba...  Idan har Aneesa ka sameta da laifin dumu dumu Ameesha fa? Bana jin zata iya aikata maka makamancin haka..."

Mtsww Dr ya ja tsaki "ya Ina sanar maka abu kana neman karyatani...? "Ka taɓa ganin ta da maganin a hannu tana sha?" Hafiz ya yo saurin jeho masa tambaya. "Look Hafiz bana son irin wannan tambayar please." "Am sorry to say Dr Asmad amma wallahi na yi rantsuwa Ameesha ba zata iya abin da kake tunani ba, shin ina hankalinka ya ke da baka bincika ba? Shin menene na saurin sanya zargi cikin rayuwar aurenku? Ina mai baka shawara ka je ka yi bincike domin tabbatar da abin dake wakana a gidanka." Wannan karan a zafafe Hafiz ya gama maganar.

"Bincike! Hmmmm ai ba sai na yi bincike ba, domin amsar a fili take na gani da idona, kuma ba sharri na yi mata ba, don haka Hafiz sai anjima." Yana direba maganar ya mike da niyyar barin falon. "Ka je Dr amma ka yi gaggawar daina wannan fushin tun kafin ta kai ka ga dana sani." Bai fasa tafiyar ba sai da ya kai kofa kafin ya juyo ya kalli Hafiz ya ci gaba da tafiyarsa.

Tafiya yake a mota maganganun Hafiz na yi masa yawo a k'wak'walwa, ya rasa ta ina zai fara matsalar sam Nenne bata sakar masa fuska balle ya je can ya samu mafita, to kuma idan ya je sangartacciya tana can haka zata sanya shi gaba da kuka mtsww ya ja tsaki a karo na barkatai.
****

Haka kwanaki ke tafiya yau watan Ameesha uku a gidan Nenne, tattali Nenne ke bama Ameesha sam bata barin ta da damuwa, ita dinma tana jin dadin zama da Nenne domin tana samun kula a wajenta har wata kiba Ameesha ta yi, ba lallai ne mutum ya kula tana da ciki ba, bata neman abu ta rasa duk kankantar sa Ummi da Abba sau uku suna zuwa duba ta, sun yi farin ciki da jin Autar su na dauke da ciki Ummi har tana tsokanarta "Oh! Autar Ummi yanzu kuma dole a rage sangarta domin kin kusa zama uwa." "A'a Hajiya Halima Ameesha ai sangarta ba zai barta ba yar gatan Abba da Nenne da Bobbo ne fa, ta ya zata daina sangarta." Gaba daya suka saki dariya Abba ya ce "Faɗa mata dai ai ba a canzawa tuwo suna sangarta kuwa uwata yanzu ta fara ko a gaban kanwata ko kanina (yaron Meesha ko yarta Abba ke nufi.) Kar ki fasa komai uwata. Murmushi ta yi bayan ta gama tunawa.

Dr ya yi na cin duniya Nenne ta bari Ameesha ta koma amma ta ki yarda, da taga zai dameta sai ta soma haɗe girar sama da ta kasa idan ta kasa gaisuwa ma da kyar yake samun ta amsa balle ya samu damar ganin Ameesha, har ya ɗan zama abin tausayi. Duk wannan abin da ake yi Aneesa bata taɓa sanin Ameesha tana gidan Nenne ba, domin ita bata wani damu da zuwa gidan ba kuma ko taje bata dadewa take tafiya, Ameesha kuma kullum cikin bedroom take sai kuma garden in tana son shan iska take zuwa.

A gaggauce ya yi parking motarsa ko tsayawa rufe motar da kyau bai yi ba, domin har ya je asbiti ya yi mantuwa shi ne dalilin dawowarsa, kai tsaye bangaren Aneesa ya yi, yana tura kofar ta buɗe kutsa kai cikin falon ya yi duk sallamar sa bai samu an amsa ba, yasan har matar gidan shi yasa bai damu ba ya yi wucewar sa bedroom ɗinsa, ya ɗauko file har zai fita  sai ya fasa don yana son ya sanar mata da ta shirya idan ya dawo su je gidan Nenne, abin da kunnuwan sa suka soma jiyo masa ne yasa shi daskarewa...

     *YAR MUTAN RANO*

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now