ARBA'IN DA TARA

2K 102 7
                                    

*SANGARTA*

                   ©
     _*ZULAYHEART RANO*_

         *SADAUKARWA*
*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Wow Masha Allah hakika na ji dadin comment ɗin ku, hakika ya sanya Ni nishaɗi ku ci gaba da ina son comment dinku hakan ya nuna min kuna bibiyar labarin sosai, masu korafin cewa Ameesha ta yi wauta da ta yi wa Aneesa kyautar 'yarta ku sa ni cewa ba wauta Ameesha ta yi ba, domin rama Alhairi ga mai sharri ba illah ne ba, ko ni zan iya fiye da abin da ta aikata.*_
                        *49*
"Yau kuma sangartar ne da wauta ya fado kanmu ni da ɗiyata?" Turo baki Ameesha ta yi ta ce "Babu wani wauta ni dai wannan maganar har cikin zuciyata na yi ta ko bayan babu raina Aneesa zata riki 'yar na..."  Saurin rufe mata baki  Dr ya yi cikin sauri ya ce " ki bar yi min wannan mummunar fatan in sha Allah babu maganar mutuwa yanzu sai kin haifa min 'ya'ya goma sha biyar." Zaro ido ta yi ta ce "Sha biyar? Tab sannu baby ai mutuwa ta Allah ce idan lokaci ya yi babu makawa." Kasa furta komai ya yi sai kallonta  yana matukar mamakin maganar ta.

Wani kallo ta aika masa da shi  wanda ya sanya jikinsa mutuwa murus, shi sai yaga kamar ba Ameeshar sa ba, duk lokacin da suka hada ido sai yaga murmushi ne kwance a fuskar ta wanda ya kara fito da zallar kyaunta, "Cutie kin yi kyau da shayarwa fa." Ya yi sauri kawar da wan can maganar."Babu wani kyau ni kuma zafi nake ji baby." "Kwantar da hankalinki ki saba tukun, idan na fita zan shigo maki da magunguna wanda za su rage maki zafin." "Tom kafin na saba da aiki, ka fadawa Nenne kuwa?"

"Eh! Har da su Ummi sai dai na manta ban fadawa Meena ba." "Ok bari na kira ta har da k'awata Ni'eema Allah yasa tana gari." Ta ida maganar tana lalubo wayar. Amsan babyn ya yi a hannunta, tare da zuba mata ido "Cutie Wai yarinyar nan da wa take kama?" "Yo Ina zan iya bambance wa kasan jarirai rikida ne da su, amma kamar tana kama da Autar Ummi." Ta karasa maganar cikin sigar tsokana. "A'a da Autan Nenne ta ke kama Malama." Dariya suka sake gaba daya kafin su yi wata maganar Aneesa ta yi sallama, hannunta rike da plet na farfesun kayan ciki. "Ki fara cin wannan kafin na yi maki girki." Amsa Ameesha ta yi tana faɗin"Na gode." Idonta akan Aneesa don gani ta yi kamar ta yi kuka. Sai dai bata yi magana ba ta soma shan farfesun suna dan taɓa hira. Kwantar da jaririyar Dr ya yi ya fita.

"Wai Yar'uwa kuka ki ka yi ko?" Ameesha ta yi tambayar tana ci gaba da shan farfesun ta. "A'a ban yi kuka ba mai kika gani?" "No! Ban ga komai ba, amma yana da kyau komai a rika fawwalawa Allah shi zai kawo karshen damuwa." "In sha Allah ina godiya." Tabbas Ameesha ta yi gaskiya domin ba karamin kuka Aneesa ta yi ba, nadama sosai ya shige t da yanzu ita Dr ya fara yi wa hidima, tana ji Dr har kyautar sabuwar mota ya yi wa Ameesha dalilin haihuwa, lallai ta cutar da kanta. Cikin hiransu sosai  Aneesa ta fahimci wasu daga cikin halayyar Ameesha kuma ta tabbata  mutum ce ita  mai sanyin hali da cikakken imani, tana yi wa 'yarta fatan ta dauki halinta na karamci. Mik'ewa ta yi tana faɗin kin ga "bari na je na dafa maki abu mai dan nauyi yadda baby zata samu ta koshi. Tana mik'ewa Meena tana yin sallama, sai da suka gaisa kafin ta fita.

Fitar ta babu jimawa Dr ne ya shigo hannunsa dauke da ledoji irin ta pamarcy Ameesha ya mik'awa yana faɗa mata yadda zata yi amfani da shi, sannan ya amshi yariyar a hannun Meena har tana tsokanarsa "Oh! Yau ga ɗiyar sangartacciya Ameesha a hannun Dr! Dariya ya yi ya ce "Meena kar ki ta do min baya yanzu dai ita kanta ta shaida ta girma sangarta sai a barwa yara. Harara kawai Ameesha ke aika masu, Meena fita ta yi ta bar Dr   dauke da 'yarsa yana mata addu'a bayan ya gama ya dubeta tare da ya ce "Cutie kin ga kyautar da Allah ya yi mana wanda babu mai iya bamu sai Ubangiji sai  mu godewa Allah." "Alhamdulillah! Ta furta cikin sanyin murya. "Yanzu wani suna kike son a sanya mata?" "Bani da zaɓi bari Aneesa ta shigo." "Ok." Ya amsa yana ci gaba da kallon yarsa. Cikin kananun lokaci  har ta kammala girkin da taimakon Meena cikin babban tire suka shiryo.

Da sallama ta shiga dakin ta aje tana faɗin "Hamman Baban baby Sannu da hutawa, Yar'uwa sannu." Yawwa suka amsa a tare, zuba mata abincin ta yi ta mikawa Ameesha. Dr ya dubi Aneesa cikin kulawa ya ce "Uwar 'ya wane suna za a sanyawa ɗiyar taki?" "A'a tambayi Yar'uwa duk wanda ta zaba ya yi min." "A'a zaɓa dai Yar'uwa na baki dama." "Tom ina godiya da wannan dama a sanya mata sunan Nennena." Dariya Dr ya yi ya ce "Babban BURINA kenan to Allah ya raya mana FATIMA BINTA." Take ya yi mata huduba ya kalli Aneesa yana faɗin.

"To kuma ya lakabin ta?" "*(Miemie)*." Zamu rika ce mata. Ameesha dai tana gefe sai murmushi take dokawa, yau abin masha Allah daɗi yake mata tana fatan Allah ya dauwamar da su cikin farin ciki mai dorewa. Babu jimawa Nenne suka iso kamar haɗin baki su Ummi ma suka zo, gida ya cika da murna babu kamar Nenne da ta samu takwara.

Haka suka ci gaba da zama kullum gidan cike da masu zuwa barka, har ranar suna ya zagayo inda aka yi gagarumin taro wanda ya amsa sunan sa, an ci an sha an yi komai cikin kwanciyar hankali, su Nenne sun taka muhimmiyar rawa haka ma  Hafiz da yan gidan su sun yi hidima sosai wa Ameesha da yarta.

Bangaren gidan su Ameesha ma sosai aka yi hidima. Ba a bar Aneesa a baya ba ta yi bajinta sosai wanda ya ba wa kowa mamaki ciki har da Dr, domin akwati guda ta yi ma Ameesha da diyarta. Haka dai taro ya tashi lafiya Ameesha ta ci gaba da kula da Miemie yarinya mai kama da ubanta sak, idan kaga Miemie a wajen Ameesha to abinci aka kawota ta ci amma wajen Aneesa take wuni komai ita ke mata, zaman su abin burgewa da sha'awa. Yanzu watan Miemie biyu ta yi wayau sosai abinta gwanin sha'awa gata tubarkallah.

Sai dai fa Allah ya yi Miemie da shegen rigima, kullum kuka har asbiti suka je aka tabbatar lafiyar ta lau, sosai kukanta haushi yake ba Ameesha,  Aneesa kaɗai ke iya lallashinta.

****
Kaiwa kawai yake yana komowa a cikin katafaren falonsa , hannunsa rike da waya yana kiran amininsa Alhaji Mamman "Hello ina jiran ka cikin gidana dake bayan gari." Daga haka ya katse wayar yana jero tsaki marasa adadi, ban abin da yake so a yanzu sai dai ya samu mafita domin kullum tsanar Alhaji Taheer gaba yake a zuciyarsa. Ba a jima ba Alhaji Mamman ya iso, gaisawa suka yi ya bashi ruwa don tsabar tashin hankali kasa ce masa komai ya yi sai girgiza kai da yake irin dai yana cikin muguwar damuwa  Alhaji Mamman ya muskuta tare da cewa

"Wai Alhaji Mansur ya maganar ka da Alhaji Taheer ne?" A jiyar zuciya ya sauke mai karfi kafin ya yi karfin halin cewa"Yo wane amsa zan baka ai Ni kam Taheer ya zame min ciwon ido na rasa ya zan yi da shi, wannan shashashan da matarsa ta haihu ko shawara dani baiyi ba ta sanyawa 'yarsa sunan mahaukaciyar yar Taheer wannan abu ya min ciwo amma akwai shirin da nake masu." " Gaskiya dai ka dage don kullum abin gaba yake kayan da ake shigo masa da shi har sun haura na da, ga yar tashi ma ta haihu ba kaga irin dukiyar da suka kashe ba."

"Kai dai zuba ido ka yi kallo kidnapped ɗinsa zan sa ayi,  kila ko tanan ma samu rabonmu." "Wannan gaskiya ne, yin haka shi ya fi maka." Haka dai suka ci gaba da hira Alhaji Mansur yana ci gaba da bayyana munanan manufofin sa akan Alhaji Taheer.

Kwanci tashi babu wuya wajen Allah har Miemie ta yi shekara a duniya, yarinya mai shegen wayau tasan kowa na gidan, bata saba da Meesha da Dr ba kamar Aneesa komai Momma haka take faɗawa Aneesa, Ameesha kuma Mami Dr Kuma Daddy, tun tana da wata bakwai a duniya ta soma tafiya magana kuwa kamar wacce ta hadiyi rediyo, wani lokacin har mamakin wayanta suke yi. Meesha ce kwance idonta lumshe kamar mai bacci, Miemie ta kwaso da gudu ta faɗa kanta tana faɗin "Mami tashi." "Oh! Allah Miemie ke kam ba ki son na huta idan na tashi mai zan yi maki?" Aneesa dake zaune a falon ta saki dariya tana faɗin " ke kuwa Yar'uwa tashi mana ki ji me zata faɗa maki." Ta shi ta yi zaune hannunta dafe da goshinta, ta ce "wallahi kaina ciwo yake." "Ayya sannu." "Yawwa ina za ku je ne haka?" Da sauri Miemie ta ce cikin Hausar ta mara fita "gitan Nenne ta mu je." "Shi ne ko ku faɗa min na shirya?" "A'a yi zamanki wannan baccin da ya sarface ki a kwanakin nan bana jin zai barki zuwa unguwa." "Hmmmm! Ki dai bari Yar'uwa wallahi kamar mai cutar bacci haka nake jina, sam na rasa gane kaina ɗazun indomie zan dafa daga daura ruwan zafi kafin ya yi zafi na dawo falo wallahi bacci ya dauke ni, in da Allah ya rufa min asiri ruwan bai kai ga kone wa ba na farka." Murmushi Aneesa ta yi ta ce "Bari Hamman ya zo ya kamata ya duba ki wannan sleeping ɗin ba na lafiya ba ne."

Zaro ido ta yi ta ce "A'a nikam lau nake bacci ne kawai Allah ya kawo bari ma ki ga na tashi." "Za ki ga lafiya Yar'uwa mu dai Ni da babyna mun ce Allah ya inganta." Tana dire maganar ta suri Miemie suka fice, ya yin da suka bar Ameesha cikin mamaki. Bata bar mamaki ba har zuwan Dr bayan ya gama cin abinci ya fara tambayarta ko me ke damunta, a sanyaye ta ce "ɗazun Aneesa ta yi wata magana kamar nufin ta ciki ne dani." "To kuma shi ne abin damuwa?" "Haba beby ciki tun yanzu wallahi haihuwa da wahala duka yaushe na haifi Miemie?" "Kwantar da hankalin ki Cutie Yi addu'a Allah ya baki nagari, domin ciki ya tabbata a gareki har na wata biyu." Kara zare ido ta yi da jin maganar Dr ta ciki? Ai ni sam ban ji wani alamomi ba sai bacci kamar wata mai cuta." "Baccin shi ne alamar da ya kamata ki gane, nikam tun bai kai wata ba na fahimci ajiya ta don wannan karon ban yi sake ba." Fuska dauke da murmushi mai nuna zallar farin ciki da jin dadi Dr ya dire maganar.

Ameesha kam kasa cewa komai ta yi sai kallon Dr da take yi.

     Mu je zuwa dai an zo final in sha Allah.

     *YAR MUTAN RANO*

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now