ARBA'IN DA HUDU

1.6K 100 1
                                    

*SANGARTA*

              
                     ©
    _*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_Ina dai bada hak'urin rashin ganin post kullum wallahi dai abubuwa ne sai a hankali amma zan fara k'ok'ari ina typing ɗin. Matsalar baku yi comment._

                 *44*

Zama ya yi kansa na wani irin sarawa, juya kwalin maganin yake yana karawa ya yi kusan minti biyar a wajen sannan ya ɗauki maganin ciwon kan ya fita falo inda Ameesha take, miƙa mata ya yi bayan ya yi ƙoƙarin danne zuciyarsa. Amsa Ameesha ta yi sam bata kula da yanayin da yake ciki ba tunda idanunta a rufe suke, sai dai ta yi mamakin ganin ya miƙa mata maganin ba tare da ya ɓare ba, bai saba yi mata haka ba sannan kuma babu ruwa.

   "Baby baka ɓare mini maganin ba kuma baka kawo mini ruwa ba." A shagwaɓe ta gama maganar, da muryar ciwo.
Ɗan tsaki Dr ya ja zuciyarsa cike da haushinta ya ce "Sai na kawo maki ruwa za ki sha maganin? Ashe kam yau ba za ki sha ba." Yana gama faɗin haka ya yi shigewarsa bedroom.
  Kan Ameesha ya ɗaure da maganar da Dr "Me hakan ke nufi?" Tambayar da ta yi wa kanta kenan hankali tashe, sai ma ta ji ciwon kan ya ware, jiki a sanyaye ta nufi ɗakinsa tana faɗin "Baby wai yau ba zaka mini wanka ba ne tunda ka ki ba ni ruwa na sha maganin to na fasa sha." Tana maganar hawaye suna barazanar zubowa.

Mtsww! Dr ya ja tsakin da ya yi sanadin ɗaukewar numfashin Ameesha na sakonni, sai kuma ta tsinkayo muryarsa yana magana cikin muryar da bata taɓa sanin Dr na da irinta ba "Ke bana son damuwa, ki bar ni na huta kina neman takura ni fa Ameesha, je ki waje bana buƙatar ki kusa da ni." A zafafe ya ke maganar. "Ameesha." Ta maimaita yadda Dr ya kira sunanta kai tsaye, saurin toshe kunne ta yi tana ambaton sunan Allah a fili. Wasu hawaye suna zubowa daga idonta jikinta ya yi sanyi ƙalau take ciwon kan ya dawo sabo, da ƙyar ta buɗe baki ta ce

"Baby me kake nufi da maganar da na ji, shin kunnena sun ji.." Hannun da ya ɗaga mata yasa ta yin shiru da sauri. "Za ki fita ko ni na bar maki ɗaki?" Tambayar ya yi yana ɗaukan wayarsa. Kallonsa ta yi sai ta ga kamar ba Dr Asmad da ta sani ba ne wannan don shi kodayaushe fuskarsa ɗauke da murmushi yake, saɓanin wannan da ya wani murtuke kamar wanda bai san wani abu dariya ba, da sauri ta fita tana kara fashewa da kuka.

Dr na ganin ta fita ya furzar da wani iska mai zafi, zuciyarsa cike da takaicin matan nasa yanzu duk so da tattalin da yake wa Ameesha da wannan zata saka masa, shi ko me yake wa matansa da suka zaɓi su musguna masa ta hanya mafi muni, Aneesa ta zubar masa da ciki bata tsaya iya nan ba ta ci gaba da shan magungunan hana ɗaukar ciki, sam bai damu ba don yasan kanta ta ke yi wa, shi ne ita ma Ameesha zata ɓullo da haka me ya yi masu da zafi da basu ƙaunar haɗa jini da shi? Wannan tambayar shi ya ci gaba da yi wa kan shi sai dai ya rasa amsarsu.

Ameesha kuwa tana shiga bedroom ɗinta kuka ta ci gaba da yi, duk iya tunanin ta ta kasa tuna laifin da ta aikatawa Dr mafi muni da har ya jefa ta cikin wannan mawuyacin halin, kwana ta yi idonta na hawaye sam bata rintsa ba yadda taga rana haka ta ga dare, shi ma ɓangaren Dr da ƙyar wani wahalallen barci ya kashe shi ko da asbah sallah kawai ya yi ya koma barcinsa.

Ameesha tana idar da sallah ta shiga kicin ta fara shiryawa Dr abin break tana yi tana hawaye a haka ta kammala, sannan ta gyara kicin ɗin da falo, kafin ta yi wanka sai da ta gyara bedroom ɗinta ta turareshi da turare, wanka ta shiga bayan ta cika ruwan wankan da turaruka masu sanyin ƙamshi, bata wani jima ba ta fito simple dressing ta yi top da wani three kwantan wado ta sanya ta raba  gashinta gida biyu da reboom kalar rigar ta, jikinta sai ƙamshi yake fitarwa kallo ɗaya zaka mata kasan tana cikin damuwa musamman yadda idanuwanta suka kumbura sosai. Jiki a mace ta nufi ɗakin Dr.

Ta kai hannu da niyyar buɗewa sai ta ga an buɗe ƙofar, baya ta ja tana faɗin "Barka da safiya." Bai amsa ba sai ma hanyar wucewa da ya lalubo, ganin da gaske zai wuce sai ta yi saurin riƙo hannunsa tana faɗin "Mai na yi maka baby kake fushi da ni tun jiya ga shi kuma yanzu gaisuwata ma kaƙi amsawa?" Zame hannunsa ya yi daga riƙon ba tare da ya furta komai ba. Wasu sabbin hawaye suka zubo daga idonta murya na rawa ta ce

"Na kammala break please ka tsaya ka yi." Sai yanzu ya yi magana shi ma a takaice ya ce "Bana buƙata." Daga haka ya yi wucewarsa, inda ya bar Ameesha zaune cikin kuka ta kasa ko da tashi a inda take, duk iya tunanin ta bata gano laifin da tawa Dr ba, haka dai ta kasance cikin hawaye har bayan la'asar da kyar ta iya yin break shi ma sai da ta ji tana shirin hallaka kanta, tana zuba idon ganin Dr amma sai ta ji shiru, duk da tasan yau ba ita keda shi ba amma ya saba zuwa ya yi mata sallama yau kam shiru har bayan magriba.

Sabon kuka ta fashe da shi tana tir da halinta tunda ta kasance mai saɓawa mijinta har ya ɗau fushi da ita mai tsanani, sam ta manta da wai ana cin abinci don rabonta da shi tun na safe ta nemi yunwar ta rasa, alwala ta ɗauro ta zo ta zube gaban Ubangijinta ta ci gaba da kai kukanta bata gushe ba har sai da ta yi sallar asuba sannan nannauyan barci ya kwashe akan sallayar.

Duk da ya ji zafin abinda da yake ganin Ameesha ta ha'ince shi da shi, wani gefen na zuciyarsa tana jin haushin yadda Ameesha ta kasance daga dare zuwa safe, kukanta ya tsaya masa a rai sosai, har ya ji kamar ya je ya lallasheta sai dai ya zama dole ya nuna mata kurenta. Aneesa ma tunda taga Dr da ya dawo office yau bai je sallama da Ameesha kamar yadda ya saba ba sai ta yi tunanin ƙila ba'a gidan ta kwana ba, ci gaba ta yi da kulawa da Dr tana son ta ba shi dukkan wani farinciki. Sosai ya yi ƙoƙarin biye mata ko dan ya sauke hakkinta da ke kan shi, duk da hankali da tunaninsa suna ga Ameesha.

****
Najeeb ne keta kai komo tsakanin repretion da ƙofar ɗakin haihuwa, gefe guda kuma Mumynsa ce da alama Rufaida ce a ɗakin don yadda Najeeb ke zarya hankali a tashe. "Haba Najeeb ka kwantar da hankalinka In Sha Allahu lafiya zata sauka." Da taushin murya take masa kalaman.

"Na kwantar Mumy Allah Ya sauketa lafiya." Amin Mumy ta amsa tana ci gaba da kwantar masa da hankali, minti talatin tsakani wata Nurse ta fito ɗauke da jaririya cikin towel mai laushi da kyau, miƙawa Mumy ta yi tana faɗin "Hajiya ga baby girl nan Madam ta sauka." "AlhamduLillah!" Suka haɗa baki wajen faɗa, Najeeb kuɗi ya zaro ya mikawa Nurse ɗin ya ce ga goron albishir nan. Amsa ta yi tana godiya Mumy ta cika da murnar samun jika yarinya kyakkyawa da ita, ko kunya Najeeb bai ji ba ya amshi yarsa yana kiss da addu'oi. Babu jimawa aka fito da Rufaida zuwa ɗakin hutu tunda lafiya ta haihu sai gajiya.

Cikin ɗakin bayan Mumy ta haɗa mata shayi mai zafi ta sha, sai Najeeb ya kuma rungumar yarsa ya bata zamzam da zuma kafin ya soma yi mata huɗuba, Mumy ta kalleshi ta ce "huɗuba kake mata?" "Eh Mumy na yi mata huduba da *Maryam*. _Littel Ameesha_." Murmushi Mumy ta yi ta ce "Allah Ya raya Maryam cikin musulunci." Domin dai tasan irin son da Najeeb ke yi wa Ameesha.

Ita kanta Rufaida bata ji haushin sunan da ya sanya wa jaririyar ba, sai ma addu'a da take yi wa yarta, babu daɗewa jama'a suka cika asibitin domin taya su murna.

****

Wasa wasa dai har Dr ya fita ɗakin Aneesa bai saurari Ameesha ba, yau take sa ran zata karɓi Dr kuma ta yi alƙawarin sai ta daidaita tsakaninta da Dr kuma sai tasan laifin da ta yi masa domin a kwanaki biyun nan ita kaɗai tasan a halin da ta yi su. Miƙewarta ke nan daga kujera zata nufi kicin domin uku da kwata ta yi sai ta ji ana buga ƙofarta, da mamaki ta isa ƙofar tana faɗin "Waye?" Muryar da ta ji ya sanya ta buɗewa tana kallonta baki buɗe. Aneesa kam wani kallo ta watsawa Ameesha tare da jan siririyar tsaki ta ce "Hamman ne ya ce in kawo maki wannan lemon ki sanya masa a firij don ke kike da shi." Har ba za ta amsa ba, domin bata taɓa ganin haka ba sai kuma ta yi Murmushi  wanda ya tsaya iya labba tasa hannu ta amsa tare da shigewa ciki.

  YAR MUTAN RANO

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now