BABI NA SHA BIYAR

2.1K 136 0
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*

_*AYSHA WAZIRI kina raina har na rasa bakin da zan ya beki, amma duk da haka Allah ya tsare ki a duk inda kike ya kare ki da sharrin mahassada and  kuma ba zan manta da ke ba i heart you*_

*Fans Ina jin korafin ku, amma Please kuyi hakuri wallahi harkoki ne suka yi min yawa amma insha Allah zan yi kokari na rika yi maku post a kai akai, don farin cikin ku shi ne namu, in babu ku tofa muma babu mu, a dai ci gaba da hakuri, tare da bin Yar Mutan Rano sannu a hankali* jin jina ga surbajo novel👍

''' My Besty taki salon ta daban ce, Yaseen ina mugun yinki'''😍😍

                      *15*

Mamaki karara ne a fuskar Meena, ido kawai ta zuba tana kallon ta, tsawon minti biyar sannan a hankali ta saki ajiyar zuciya ta ce

"Meesha me ki ke nufi? Shi Najeeb kuma ya za ki yi da shi?"

"Shi ma ina son sa, Meena ba zan ɓoye maki ba ina son Dr ɗan fullo har cikin zuciyata,so fa ba na wasa ba, wallahi kar ki so kiga halin da na shiga da jin maganar auren sa."

" Kar ki damu da auren sa, ki sa a ranki in mijinki ne zaki aure shi ko da yaushe ne, amma abin da yake bani mamaki yadda kika ce shi ma Najeeb kina son sa."

" Eh ina son Najeeb saboda yana da halayya masu kyau, amma so ɗaya tak yana ga Dr Asmad."

"To Allah ya zaɓa mafi alheri."

"Amma Please Meesha ki yi kokarin danne son sa a zuciyar ki kar ki bari ya sani, ki ci gaba da dauriya har ya furta maki da kansa yana son ki."

Murmushin takaici ta yi ta ce

"Haba Meena kema kin san halina, ba zan taɓa bari ya sani ba ko da kuwa son na sa zai zama ajali..."

Saurin toshe mata baki Meena ta yi ta ce

" Please bar maganar ajali insha Allah zaki auri Dr ke dai ki ci gaba da addu'a ni ma zan ta ya ki, ba ri na kawo maki abinci."

"Ko kar ki kawo na koshi."

Harara Meena ta jefa mata cikin wasa ta ce

"Ai ko ya zama dole ki ci abinci, don baki zama da yunwa."

Ta ida maganar tana sauka daga gadon, Meesha kam gyara kwanciya ta yi tare da lumshe ido.

Gidan ango Asmad kuwa ana ta shan angonci, zaune ya ke a babban falon gidan daga shi sai singlet da gajeren wando, laptop din sa ya ke matsawa, zuciyar sa cike da tunanin Ameesha wacce ya kwana biyu bai ganta ba, inda so samu ne yau ya leka asibiti don babu mamaki ta na ciki a yanzu haka, sai dai ya san halin yar matsala wato Aneesa, tana iya hana shi fita.

Lokacin da ya ke tunanin, tana tsaye a bakin koriɗo ta zuba masa ido, cikin wani irin shaukin so. Ita dai Allah ya jarabeta da son wannan bawan Allah, cikin kwalliya  ta ke kai da gani kaga amarya, kai tsaye wajen sa ta nufa da zuwa bata jira komai ba tasa hannu tare da zare laptop din, ta wani narke fuska kamar za ta yi kuka ta ce

" Haba Hamma aikin me kake ta yi ne har yanzu, ya ci fa a ce kana samun hutu"

Kallon ta ya yi tare da ɗan sakin murmushi ya ce

"Ban da abin ki ina hutu a wajen Dr? Ke dai kawai kin rasa abin korafi, yanzu ma tashi zan yi in shiga asibiti don duba petient  ɗina."

Saurin ɓata rai ta yi ta ce

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now