BABI NA ASHIRIN DA BIYU

1.9K 129 2
                                    

*SANGARTA*

                      ©
            *ZULAYHEART RANO*

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

_*Masoya abin alfahari, duk inda nake ba ni manta masoyana Allah Ya barmu tare da ku*_

*Ina yan TEAM NAJEEB MANSUR?*

*Jinjina yake maku da fatan Alhairi*

*Ina yan TEAM DR ASMAD ABUBAKAR (ɗan fullo)?*

*Dr ya ce yana godiya sosai da k'aunar da kuke masa, ku ta ya shi da addu'ar samun farin cikinsa*

                      *22*
"Madallah! Ni ɗimma zuwan da na yi don mu ƙara shawarta yadda bikin zai kasance."

Wani irin farinciki ne ya ziyarci Mummy da jin batun Alhajin

"Abba da gaske ka yarda in aure Ameesha?" Najeeb ya yi maganar jikinsa har yana rawa.

Ɗaga kan Najeeb ɗin Alhaji Mansur ya yi ya ce

"Haba Najeeb duk duniya ba ni da burin da ya wuce in faranta maka, don haka na yarda da auranka  da Ameesha, don Alhaji Taheer bai cancanci haka daga gare ni ba."

Don farinciki ai Najeeb bai masan lokacin da ya rungume Abban nasa ba, ya soma zuba masa godiya kamar zai ari baki. Ita kanta Mummy farinciki hana ta magana ya yi, amma da gani kasan tana cikin tsantsan jin daɗi.

Shi ma Alhaji Mansur ganin yadda suka samu farinciki sai ya ji abin ya masa daɗi.

"Ya maganar gidan naka?" Alhaji Mansur ya dawo da shi daga duniyar mamakin da ya shiga.

"Em! Um! Abba na gama sai 'yan abin da ba za a rasa ba."

"To ai shi ke nan, tunda ka kammala komai, motar da na saya maku kai da matarka suna hanya In Sha Allahu."

"Mun gode Abba Allah Ya saka da Alhairi Ubangiji Ya ƙara buɗi."

"Amin Najeeb."

A ranar dai haka gidan Alhaji Mansur ya kasance cikin farinciki da kwanciyar hankali.

***************************

"Ki bari kawai Rukky, ai wato ranar yana fita ni ma na yi fice, wato wani lafiyayyen asbiti na shiga mutanen sun iya aiki fa!"

"Allah Hajiya yanzu cikin ya zube kenan?" Rukky ta yi tambayar daga ɗaya ɓangaren.

"Tun yaushe na sa aka zubar da shege, duk da dai na ci wahala wajen fitarsa, ban da yawo da hankalina da wani likita ya yi ta yi, amma a ƙarshe da yaga ruwan kuɗi sai kawai ya yarda, ke har wata 'yar harƙalla muka ƙulla da shi sai dai ina tsoro, gashi jinin har yanzu yaƙi tsayawa."

"Tsoro! Wani irin tsoro, ke Wallahi ki saki jiki ki fantama har duniya ta sanki, ke ke nan kullum zaune cikin gida, shi kuma jini ki samu magani dole ya tsaya ko baya ƙaunar Allah."

"Eh! Ina tsoro duk da dai guy ɗin ya haɗu, ko da ya ke bai kai Hamma Asmad ba, tom zan koma asbitin zuwa gobe, kuma dai ina tsoron abin da zai je ya dawo, don Wallahi Hamma ba saurara mini zai yi ba muddin ya san abin da na aikata."

Mtsssw! Rukky ta ja tsaki ta ce

"Amma ke banza ce, fitowa fili za ki yi ki faɗa masa? Wai halan ke ba mace ba ce, da har ba za ki iya yin abin ki cikin sirri ba?"

"Zan duba Rukky ni ma ina muradin saurayin, duk yadda muka yi za ki ji labari, nan da 'yan kwanaki."

"Yawwa 'yar gari, sai ki tanaji magungunan hana ɗaukar ciki, da na tsayar da jini don kar a samu matsala, tunda shi Dr ya zo hannu bana jin zai samu salama a kwanakin nan."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now