BABI NA SHA UKU

2.1K 139 1
                                    

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*(NWA)*

                 *SANGARTA*

                        ©
            *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga Khadija s Muhammad my Cittah*
                      *13*

" Lafiya kuwa?"

Daga can ɓangaren Aneesa ta ce

" Hamma ina yini?"

"Lafiya."

Ya yi maganar fuskar sa ba yabo ba fallasa.

" Ehm daman..." Sai kuma  ta yi shiru.

" Aneesa ina jinki akwai matsala ne?"

Dan murmushi ta yi ta ce

"Dama so nake na ce muna da buk'atar kuɗi, wanda zamu yi amfani da shi."

"Ok"

Shi ne kaɗai abin da Asmad ya faɗa ya katse kiran.

Aneesa kuwa sororo ta tsaya da waya a hannu, tana mamakin Asmad ɗin , sai kuma ta saki murmushi da ta tuna kwana kaɗan ya rage su kasance matsayin miji da mata, tana alfaharin kasance wa da Asmad a matsayin miji.

Da wannan tunanin ɓacin ran da ya ɗan sa mata ya gushe.

Asmad kuwa falon ya koma inda iyayen sa suke, zama ya yi tare da kallon Bobbo ya ce

" To Bobbo yau she za'a buɗe asibitin?"

Asmad ya yi tambayar yana kallon Alhaji Abubakar.

" Ranar ɗaurin Aure ina kamar zai fi."

Bobbo ya bashi amsa.

" A'a ko dai washe gari, don kasan fa kafin a dawo gida za'a daɗe a hanya."

Nenne ta faɗa.

" Tom a barshi haka ɗin, tunda muna da buk'atar mutane."

Allah ya sa albarka ya taimaka, Ubangiji ya ida nufi ka kula da kyau Asmad ka taimaki bayin Allah, domin kaima Allah ya taimake ka ."

"Insha Allah Nennena zanyi yadda kika umurta, kudai ci gaba da yi mana addu'a."

Kullum muna yi maku Allah ya yi albarka.

********************************

" Abba wai ni kam sai yaushe za'a sallame ni?"

"Ina zan sani uwata? Ki bari dai har ki kara samun sauki."

"Nidai gaskiya na gaji, shi mutumin nan tunda ya aje mutum babu wanda ya kuma ganin shi."

Ameesha ta karasa maganar kamar zata yi kuka.

Harara Ummi ta watsa mata ta ce

"To ai ko yanzu kina iya tashi ki wuce, tunda ke kamar karamar yarinya ki ke ji."

"A'a Hajiya me kuma na harara? Baki ganin ba lafiya ne da ita ba?"

Kai Alhaji sai kayi ta goyon bayan Ameesha, duk maganar da taga dama shi take yi, yanzu don Allah ina laifin yaron nan?"

Dan murmushi yaja ya ce

"To naji amma dai lallaɓata ya kamata kiyi."

Su Alhaji Mansur ne su ka yi sallama, shi da matarsa fara'a sosai Alhaji Taheer ya saki da ganin abokin nasa.

" Sannu da zuwa Alhaji ku ne a wannan lokacin?"

Faɗa ɗa murmushi Alhaji Mansur ya yi ya ce

" wallahi mune muka ce yau dai tunda mun samu lokaci bari muzo mu duba mai jiki."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now