BABI NA SHIDA

2.8K 134 0
                                    


               SANGARTA

                         ©
           ZULAYHEART RANO

                     6
"Bayan Najeeb ya rufe budadden bakin shi tun sa'adda ya ji sunan Ameesha  a bakin mahaifinshi sai ya ce

" Na san ta akwai wani abu ne? Ko ba yar gidan Alhaji Taheer ba?" Shi ma Najeeb ya rufe maganar da tambayar mahaifin na shi.

"Eh ita, to ka buɗe kunne ka ji ni da kyau."

Gyara zama Najeeb ya yi, tare da mayar da hankalinsa kan Abban na shi. Sannan Alhaji Mansur ya ci gaba da maganarsa

"Kana ji na ko Najeeb? So nake daga yau zuwa satin sama masu zuwa ka tabbatar ka cusa kanka gareta, so nake yi na yi amfani da wannan damar don cimma burina."

Najeeb da kallo ya bi mahaifin nasa, don kwata-kwata bai gane inda yasa gaba ba, kamar Alhaji Mansur yasan tunanin da Najeeb ya faɗa, don haka sai ya ce

"So nake ka je wajenta da batun soyayya, ka san yadda zaka yi har ta soka wannan shi ne abin da nake umurtanka."

Zaro ido ya yi baki na rawa ya ce

"Abba kasan fa yarinyar nan ba wata kunya ce da ita ba, kuma dai da ƙyar zata amince min don ba mutunci ne da ita ba."

Tun kafin ya kai ƙarshen maganar Alhaji ke aika masa da wani mugun harara, wanda har ya firgita Najeeb ɗin,  cikin fushi ya soma magana, "Kai kam Najeeb an yi shashasha, yanzu kai a matsayin ka ka ce baka iya tsara wannan 'yar yarinyar? To bari kavji dole sai ka yi abin da na sanya ka."

Girgiza kai kawai ya yi, yana mamakin halin mahaifin nasa sosai.

"To na ji Abba amma in ta amince ya zan yi da Rufaida, kasan dai ita nake so."

Mtsww! Alhaji Mansur ya ja wata doguwar tsaki, don takaici

"Kai fa Najeeb da alama kana son raina min hankali, ina ruwana da maganar Rufaida indai buƙata ta zata biya, daga baya kasan yadda za'a yi da ita."

"Amma Abba baka tunanin a samu matsala, yarinyar nan fa da wuya ta soni, kuma nibma dai ba wani sonta nake yi ba. "

"Bani son rashin ta ido, kana jina ko? Maganar da ma faɗa maka dole ne ka yi amafini da ita don abin da nake son yi kai ne zaka yi alfahari da shi ba ni ba."

"Yi haƙuri Abba zan yi yadda kake so In Sha Allah."

Cikin ladabi Najeeb ya ƙarasa maganar.

"Yawwa ɗan Albarka haka nake so." Alhaji Mansur ya yi maganar cikin farin ciki.  Miƙewa Najeeb ya yi yana mamakin halin mahaifin na shi.

Bayan fitar Najeeb, sai Alhaji Mansur ya  manna bayan shi da   kujera haka ya sauke wani numfashi me kauri.

Ya kai hannunshi yana shafa goshin shi, wannan ita ce hanya ɗaya tilo da yake ganin zai yi amfani da ita don cikar wani buri na shi da ya daɗe a zuciyar shi.

Idan har wannan buri na shi ya cika, bai san irin kalar murnan da zai yi ba.

Zumbur!Kamar wanda ya tuna wani abu haka ya tashi, ya  ɗauki  key ɗin motar shi ya nufi waje.

*****************
Nanne ce zaune a bedroom ɗin Bobbo, magana yake faɗa mata kuma ga dukkan alamu maganar nada muhimmanci, cikin nutsuwa ta ce

"Amma kana ganin bamu shiga haƙƙin yarinyar ba?"

"Maganar shiga haƙki bata taso ba, tun da asalin maganar ba daga wajenmu take ba, abin da nake so kawai shi ne in samu Asmad ɗin ya yarda."

"Kai ma Alhaji kasan ba shi da matsala kuma yana ƙoƙarin yin biyayya, kar ka yi tunanin haka, Ubangiji Allah Ya sa haka shi ne Alhairi."

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now