ARBA'IN DA UKU

2K 112 2
                                    

*SANGARTA*

              
                     ©
    _*ZULAYHEART RANO*_

*Sadaukarwa ga Khadija S Muhammad My Besty*

                 *43*

Haka Ameesha ta sha kukanta daga karshe ta lallashi kanta, a three sitter ta kwanta tana mai ambaton sunan Allah a hankali wata nutsuwa ke saukar mata. Dr kuwa ko da ya shiga bangaren Aneesa kwance ya sameta kamar ko da yaushe tana aikin latsa waya, ko kallo Dr bai isheta ba balle ya samu arzikin sannu da zuwa. Zama ya yi tare da bismillah yana faɗin "my Anee barka da hutawa."
  Bata amsa ba sai dan dagowar da ta yi ta kallaceshi, kamar wacce aka tsikara kuma sai ta mik'e tare da shigewarta bedroom. Girgiza kai kawai Dr ya yi shima ya shiga bedroom ɗinsa, kayan jikinsa ya rage sannan ya nufi toilet alwalarsa ya dauro ya zira jallabiya sannan ya nufi masallaci, bai shigo gidan ba sai bayan ishsha da tek away ya shigo da su, a dining ya aje ledojin babu kowa a falon hakan ya nuna Aneesa bata fito ba, bai bi ta kanta ba don yasan masifa take nema da shi shi kam ba zai biye mata ba.

   Leda ɗaya ya ɗauka ya nufi bangaren Ameesha, kamar yadda ya zata kuwa a falo ya sameta tana zaune ta buga uban tagumi jin an bude kofa yasa ta yi saurin ɗagowa ido hudu suka yi da Dr wani irin lallausan murmushi ta sakar masa, sai da gabansa ya fadi da yadda yaga idanunta sun kumbura a lamar ta sha kuka, "Cutie lafiya kuwa kalli idonki fa?" "Babu komai fa baby." Ameesha ta ba shi amsa tana amsan ledar da ya shigo da ita.
    "An ya kuwa Cutie?" "Allah nifa baby babu wani abu." A shagwaɓe ta yi maganar. "Ok tun da babu komai ai shi kenan, amma Please abar kukan haka nan ya isa." "Na daina." "Promise?"Dr ya fada yana kallonta. Murmushi ta saki ta ce "Yes promise." "Ga abinci nan ki ci sai ki kwanta, karki manta da addu'a fatan kin yi sallah?" "Eh na yi." Ameesha ta bashi amsa. Fita Dr ya yi yana mata sai da safe, bayan fitar Dr abincin ta jawo hankali ta soma ci, duk da dai turawa kawai take sam bata wani jin dadin sa, bata ci da yawa ba ta ture shi gefe tare da hamdala ga Allah.

Dr kam ko da ya koma falon Aneesa bata fito ba, don haka sai ya ɗauki leda daya ya nufi bedroom ɗinta akwance bisa gado ya sameta, cikin nutsuwa ya zauna a bakin gadon yana kallonta a hankali ya furta "My Anee." Sarai tasan da shigowar sa sai ta ɗauke kai, jin yadda ya ambaci sunanta sai da wani abu ya tsirga mata tun daga tsakar kai har yan yatsun kafarta, amsawa ta yi ba tare da ta tashi ba. "Tashi mu yi magana." Fuska babu walwala ya yi maganar.

Tashi ta yi tare da kauda kai gefe taki ko da kallonsa, murmushi ya yi ya ce "Aneesa faɗa min laifin da na yi maki kike fushi dani?" Ya ida maganar yana kafeta da ido. Shiru ta yi kamar ba zata yi magana ba sai kuma ta ce "Ni baka min komai ba." "Ban yi maki komai ba kike fushi da ni Aneesa?" Cike da mamaki yake tambayarta. "Eh gaskiya na faɗa maka babu abin da ka yi min." Ta faɗa tana mik'ewa. Sam Dr baya son jan magana don haka sai ya ce "Shi kenan tunda kika ce haka, amma nasan mutum haka kawai bazai fara fushi ba tare da an yi masa komai ba."  "Ni dai Hamman na faɗa maka baka min komai ba." "Ok dawo ki zauna, kila babu abin da kika ci ga abinci nan idan kin gama ina jiranki a bedroom."

   To kawai ta amsa tana shigewa bedroom, ruwan sanyi ta sakarwa kanta zafin da zuciyarta take ta ɗan ragu ko yanzu tasan tana da matsayi a idon Dr tunda har ya yi mata magana cikin tausasa murya, duk da tarin rashin mutuncin da ta yi masa, bayan ta fito ta zauna ta ci ta koshi da yake ta yi sallah sai kawai ta koma toilet ta kuskure baki, rigar bacci ta zura ta nufi dakin Dr. Lokacin Dr na zaune cikin tunanin halin da Ameesha ke ciki, kalkalo murmushi ya yi ya ce "Barka da zuwa My Anee." "Hmm! Barkammu dai Hamman." Tana gama faɗin haka ta yi kwanciyar a kan gadon, wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta don ganin ta a kwance a gadon Hamman ɗinta.

Dan ɗago kai ya yi ya ce "Daga zuwa sai kwanciya? Ko dan hira baki taya mijinki." Kunya ce ta kamata don haka sai ta sauka daga gadon ta nufi inda yake zaune, kusa da kafafunsa ta zauna. Murmushi ya saki sannan suka soma hira irin ta mata da miji, idan ka ga yadda Aneesa ta saki jiki  sai murmushi take yi ba ka taɓa cewa ita ce. Tsakanin miji da mata sai Allah nan take suka ɗinke, dama dai Aneesa kishin Dr ke damunta.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now