TALATIN DA TARA

2K 106 0
                                    

*SANGARTA*


                     ©
         *ZULAYHEART RANO*

       *Sadaukarwa ga khadija s Muhammad My Besty*

 
                  *39*

Gida kai tsaye Dr ya nufa, bayan ya kira Hafiz ya sanar masa, yadda suka yi da Abba, cikin kwanakin sam Dr baya samun zama domin aikin da akewa sashin Ameesha, suma a bangaren Nenne da Ummi abin haka yake, Ameesha tana ta shan gyara, wata mata aka dauko mata musamman domin ta gyara ta.

Shirye-shiryen biki ya kankama yau saura kwana biyu tarewa, duka gidajen biyu cike yake da mutane wanda suka zo domin taya su murna, sosai Dr ya yi bajinta wajen haɗa mata akwatina. Aneesa kam idan hankalinta ya yi dubu to fa a tashe yake, musamman da taga irin kuɗin da Dr ya kashe wa Ameesha, duk sai ta ji ta raina kanta. Cikin tashin hankali ta dauki waya ta danna Number din Rukky ringing biyu ta dauka

"Hello Rukky! Aneesa ta faɗa cike da tashin hankali.

"K'awata lafiya kuwa na ji muryar ki a haka?"

"Babu lafiya kam domin jibi matar Hamman zata tare, kin ga irin kuɗin da yake kashe mata kuwa?"

"Ina zan sani ina Adamawa kina Kano?" Rukky ta faɗa.

"Wallahi kuwa Rukky, wallahi ina cikin tashin hankali, Please ki bani shawara."

"Kin ga Aneesa kwantar da hankalinki, ki bari ta tare sai asan yadda za'a yi, amma ki fito fili ki nuna masa fushinki."

"Hmmmm! Rukky kenan wai kina ganin Hamman yana wani damuwa ne idan yaga ina fushi?"

"Ko baya damuwa ki nuna masa."

"To shi kenan zan jaraba, zaki ji komai." Daga haka suka yi sallama, ita kam Aneesa ta ci gaba da kai komo tana neman mafita.

Wow gaskiya bangaren da za'a sanya Ameesha ya haɗu sosai, tuni aka kawo kanya daki an daka komai sai jiran zuwan amarya, Dr kam cike yake da farin ciki, ko yaushe fuskarsa ɗauke da murmushi.

Dinner kawai suka shirya, wanda za'a yi ranar tarewar, Dr ya yi gayyata sosai musamman abokansa da abokan  aikinsa na kasashe daban daban, ciki har da Dr Ansar wanda ya taso takanas don hidimar bikin Dr Asmad, ya samu tarba mai kyau daga  Hafiz domin shi ne ma masaukin baki, kuma babban abokin ango.

Abba, Bobbo da Dr, sai Hafiz angon wata dakakkiyar shadda suka yi, zanenta iri ɗaya da ta su ya Jaheed sai dai kalar ya bambanta, karfe uku aka tashi daga walimar da Bobbo ya haɗa don farin cikin Auren Asmad

Nenne da Bobbo suka zaunar da Dr suna masa nasiha akan ya riki matansa cikin amana da adalci

"Kana jina ko Asmad? Ina so ka sanya hakuri da juriya da kai zuciya nesa a cikin zamantakewar ku, ka kasance mai adalci tsakanin matanka, ka zama tsayayye namiji mai mulkar da adalci."

"In sha Allah Babbo zan yi amfani da duk abin da ka faɗa  min."

"Allah ya maka albarka, Ubangiji ya baka zuri'a dayyaba."

"Amin." Dr ya amsa.

Ita ma Nenne haka ta yi masa nasiha mai tsuma zuciya, kafin suka sallame shi. Komawa cikin abokansa ya yi inda aka ci gaba da harkoki.

Ameesha da Dr Asmad yau ranar ta kasance ranar farin ciki ne a gare su, kallon fuskarsu  kawai zai baka tabbacin haka, sanye take ciki wani rantsattsen lacce mara nauyi, wanda ya yi mugun amsar jikinta fuskar nan ta sha meka'up har wani kyalli take, duk inda ta gifta sai kamshin turarenta ke tashi, kawaye ta duk sun halarci taron tarewar ta, ciki har da Ni'eema sosai Ameesha ta yi farin cikin ganin ta.

SANGARTA COMPLETEWhere stories live. Discover now