Yar Gidan Yaddiko

17.5K 935 34
                                    

*👩YAR GIDAN YADDIKO👩*

*HAZAK'A WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu.
Dedicated to Aisha alto

*Page 1*

A garin Gumau, gari ne da fulani da manoma ƴan gudun hijira da suka fito daga Jos suke zama, sun fito daga barikin Ladi da Yalwan Shandam.
Garin Gumai wani yanki ne da ya had'a yankoki guda biyu, Bauchi da Jos. Toh duk abinda aka shuka sai Allah ya albarkace shi. Manoman suna noma kabeji, gurji wato cumcumbe. Latass, karasa, dan kalin turawa da ta hausa, kai har doya sunayi, ga masara wanda aka zuwa da manyan j5 ana saya.

Mutanen gumau akwai haɗinkai da taimakon juna.

Wannan knn.....
Hajiya Tabawa wacce yan garin ke mata lak'abi da Yaddiko, tsohuwace mai zuciyar niman na kanta, gata bafulatana ce amma mai zuciyar nima, dukda Y'ay'anta masu kuɗi ne, amma haka bai hanata niman nakanta ba, dan har noma take ga kiwon da take.
Ko maigari a gurinta yake niman aron kuɗi dan ɗan hasafi, duk wani mai ji da kuɗi a garin gumau yasan bai kai Yaddiko ba, dan karamin ɗanta babban ma'aikacene a custom, babban kuwa shima ɗan kasuwa ne,dan har gidajen mai gare shi. Allah ya albarkaci Yaddiko da yara huɗu biyu maza biyu mata sai dai ɗaya mace ta rasu.

Alhaji Imarana shine babba yana bauchi a Ibrahim bako yake da zama, Sai Alhaji Rabi'u yana zaune a abuja da iyalinshi shike karamin ɗanta.
Sai Hajiya Sadika da take aure a jos, da yaranta, sai Hajiya Aisha wacce ta rasu a shekaran da Yaddiko ta tsinci Yar gidan Yaddiko, ta sanadin hatsrin mota ita ɗaya ce aka tsinceta dan motar ta kama da wuta.

A duniya babu abinda Yaddiko ta tsana irin kukan Shatuwarta dan lokacin da aka sameta itace ta amsheta da saran ko danginta zasu tawo nimanta. Har yanzun shiru kake ji. Daukacin mutanen garin gumau suna shakkar jarabar yaddiko da yar gidanta, dan duk laifin da tayi hakuri suke aje gurin mai gari a gaya mishi.

Wannan knn bari mu duba yar gidan Yaddiko.

Faran faran kamar mi faret haka take tafiya tare da ɗaga kuran hanyar, sanye take da unifoam ruwan bula. Tsabar niman tada hankalin jama'a take ɗaga kuran.

A gaban Lamiyo mai kosae ta ci birki, kallon dandazon mutanen da suke bin layi tayi ta taɓe bakinta. Da mugun sauri tayi kan kaskon mangyaɗar take duk sukayi baya.
Akwai mai shayi a gurin irin yan nijar ɗin nan ne dariya yayi sannan yace.
"Yar gidan Y
addiko tinkiya sarkin tamɓele."

Murmushi tayi sabida tana nazarin abinda zata mishi ai tasan nufin maganarshi.

Washe hakorana nayi ina kallon Ila da taburin shayinshi, girgiza kai nayi na koma da baya, na gyara zaman hijabina wanda yake a cukurkuɗe. Sakamakon tauneshi da nake, idan duniya tayi min daɗi.

Da gudu na antayo na dunbuli kosan tare da ture wasu mutanen suka ture taberin ila mai shayi, jin karan kwai kake tassssssss. Na cikawa bujena iska ina dariya,

Ina cikin tafiya, naga babangidan alhaji dauda ya sayo kamu, dama ina cike da ɗan banza da gudu nace.
"Ba burki burki."

Kafin ya shalake harina tuni na banke ɗan wofi, na cikawa bujena iska.

Har zan wucce sai na hango gwaibar gidansu Ta asibi, kallon katangar gidan nayi na buga tsalle na kama jikin bangon na ɗanne kamar wata yar biri na tsinko, dayawa sannan nace.
"Ta asibiii ki hito gani nan na sace miki gwaiba alkur'anan nayi maganin masu dukiyar ɗan karuna."
Aikuwa yan gidan suka fito asaba'in na dire abuna na arta a guje duk na zubda gwaibar,

Ban tsaya ba sai makaranta sabida ranar monday ne. Ina shiga naga firifet suna tsaren lati, fuska nayi na shige," keee " inji garbebe, turusss nayi na tsaya tare da cin wani burki na juya, tare da kallonshi.
"Zo nan yar kwal uba kinhi sauran yaran ne."
Taɓe fuskan nayi tare da girgiza kai, nace.
"Ni ba yar kwal uba bace."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz