10

5.4K 469 27
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
      *Wattpad:Mai_Dambu*

     *Godiya ta gareku Kungiyata abin alfaharina Yan uwana rabin jikina, Masoyan asali HAZIKAN MARUBUTA, Tsintsiya Maɗaurinmu D'aya Masu fatan ɗan uwansu ya cigaba Ya Allah ka haɗe kan Hazakan mata masu burin cigaban ɗ'an uwansu, Allah ya kara haɗe kanmu baki ɗaya*

          *_Wannan shafin nakune Matan quartes musaman Ummu Amrah_*

       Thank you so muche Ameerahraji😘
Page.10
   Da gudu na shiga cikin gidansu Mama na ɗibo kuka a kitchen, nazo na watsa a kofar fita na koma gurin Yaddiko na zauna, dan gidansu Ya Najib yafi kusada gidan Yaddiko.

     Kuma kana iya jin ihu daga can, zama nayi ina jiran faruwan aikina.

      Cikin ikon Allah sai na fara jin ihun kartin mata, ana salati da salami.
       Murmushi nayi, nace.
"Wani na jiranku a bakin kofa."
      Dakyar suka fito kowa na ɗingishi, suna saka kafarsu a bakin kofar santsi ya kwashi Hajiya Sadika, ta hantsila Umma tazo ɗagata itama ta kifa akanta.
       A guje Shamsiya tayi kan uwarta nan kake jin ɗimm, Sailuba zata juya kawai itama jin kake timmm...
        "Wayyo Allah ."
Suka fasa ihu, da gudu muka fito har da masu aikin gidan.
     Haɗa idanu mukayi da sailuba na kashe mata ido, nace.
"Sannunku lallai kasa ta ɗibi kaya jibadau, yanzun dai kutashi sai a baku abonike."

        Mikewa suke amma da zaran sun mike zasu sake hantsilawa, sai kaji jagwab,, kallon sa'ido nayi nace.
"Kaga Sa'ido kawo ruwa ka watsa santsin ya tafi su samu su mike."
     Kallonsu nayi nace.
"ko bai muku bane taimakon da nayi."
      Girgizan min kai sukayi,
     Misar bayi yakawo nace ya bani, ruwan na shiga watsawa a kasa, na wanke gurin, sannan nace.
"Zaku iya mikewa."
         Aikuwa suka mike da kwarin gwiwa, ayarinsu guda kowa na tsoron takawa, Umma tayi kundunbala ɗaga kafarta take hajiya sadika ta rikota suka sake hantsilawa,
       Bani da niyyar darawa, amma sai da nayi, wasa wasa sai gasu suna rarrafe.  
   Jin karan motarshi yasa na yarda tiyo ɗin na falla a guje ina dariya, sai cikin gida ɗaƙin Mama na wucce kai tsaye na boya.
              Yana parkin ya hangosu Umma dasu sailuba, da sauri ya fito. Jan iska yayi ya furza yasan lallai nice da wannan aikin. Zuwa yayi ya taimaka musu suka mike ya kai su cikin gida, sannan ya nufi gidan su. 
      Dubani yayi yaga bana ɗakinmu, sai ya koma ɗakin Mama.
   Hango kaina yayi a can kuryan gadonta, a hankali ya taka har inda nake ya zauna a bakin gadon.
      Kamshin turaranshi na shaka, kawai sai na fashe da kuka na ɗago  kaina, zuba min ido yayi, cike da mamaki.
      "Toh basune suka ce min, tsintarcciyar mage ba,Sailuba har da murɗa min kunnena wai na fara yawon iskanci a ina na samo abin wuyana."
   Tsuke fuskarshi yayi sannan yace.
"Na tambayeki ne."
         Tura bakina nayi, ina share munafuƙan kwallar da suke bin fuskana, sanya yatsar hannunshi yayi ya ɗane min baki, na kuma sake ihu.
   Fisgoni yayi ya haɗani da jikinshi, yana kallon fuskana da na kaudashi gefe ina kuka.
        "Daga yau na kuma samunki da laifin ki zubawa wani abu ya faɗi, ni dake ne a gidan nan sai na ɓalla miki kafa duk aljanun dabobinki sun haye kanki, sai tsabar fitina ke ko kallon kanki bakiyi ne kin girma amma kina abin yara kananu."

       Cikin shashekar kuka nace.
"Wallahi wani yasake taɓa ni sai na rama, tunda su baka musu faɗa sai nice da ka tsana baka kaunar ganina, kurwata kur...."
             A tsorace na shig kwace kaina sabida yanda ya ɗaura kanshi a wuyana, aikuwa na fashe da kuka nace.
      "Ni ba yar iska bace, da zaka min is....."
         "Ya Man!!!... Miye haka wani irin abu nake gani, lallai zaki ci Ubanki, mijin da zan aura kikewa sanabe har da shiga jikinshi.... Haba Ya Man abinda baka taɓa min ba, ina matar da zaka aura. Shine kake make love da wancar baka mumunar, mai zubin. Bakakken aljanu."
      Janye ni yayi daga jikinshi ya mike, tare da tsuke fusksrshi ya kamo hannunta suka fita. Daga ɗakin ni kuwa nace.
"Ban yafe ba, mugu ɗan is.."
  "Kul Aishatu!.... Bai kyauta min ba nima dana haifeshi, amma kisani komi yana da sila."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now