17

5.4K 474 42
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

      *_Kuna shagali Yar Yaddiko zata dawo kayya banki ba dai fansa amma....._*

Page.17
Hankaɗe Sailuba yayi ya tashi da sauri ya shigo kitchen ɗin, a gigice ɗago ni yayi tare da manna ni da jikinshi, ganin yanda hancina yake fitar da jini tare da kunne na, yasa kirjinshi yayi muguwar bugawa.
    "Allah Wahid Ahad" ya furta a hankali sannan ya ɗauke ni zuwa falo, sai lokacin Yaddiko tafito dan tana sallar walaha ne, a ruɗe take tambayarshi bai iya bata amsa ba, dan yana kiran motar aaibitine.

            Ko minti uku ba'ayi ba, suka iso ɗaukana yayi ya fita dani aka ɗaurani a gadon, shiga dani sukayi shima ya shiga motar.

             A gaggauce aka nufi asibiti dani.

            Koda muka isa asibitin hanzarce aka shige dani, shashin kwakwalwa. Aka shiga dubani sunfi awa biyar a kaina.
    Kafin suka fito, mikawa Ya Maheer Hannu dr rodg yayi cikin murmushi yace.
"Dr Ina tayaka murna sisternka tana dabda dawowa normal ɗinta."

        Yake Ya Maheer yayi tare da cewa.
"Nagode dr"
              Bayan fitarsune ya shiga ɗakin yana kallon yanda nake barcin wahala, shafa fuskana yayi cikin mutuwar jiki.
      "Don Allah Aeesha karki juya min baya."
    Ya faɗa a hankali, kamar ya fasa ihun haka yake jinshi tabbas farkawata ba lallai bane, wannan shakuwar ta sake dawowa. Tunda ba kaunata yake ba,

                A gida kuwa Yaddiko hurawa Sailuba wuta tayi akan sai ta kawota asibiti, haka suka tawo asibitin. Har ɗakin da nake daga waje suka tsaya ta gilasi.
            Mikewa yayi ya fito ya samesu.
              "Wani hali take ciki yanzun?" yaddiko ta wurga mishi tambaya.
     Shafa kanshi yayi cikin nutsuwa yace.
"Hmm! " yace tare da kifa hamnunshi a fuskarshi, dakyar yasake cewa.
"Ta dawo yanda take Yaddiko! Sai dai ina cikin...."
           "Karka damu Allah yana tare da kai." tace mishi,
        Shi kaɗai yasan yanda yake cikin fargaba, ya san sarai ina farkawa ba lallai bane mu cigaba kamar da, jingina yayi da bango yana mai sunkuyar da kanshi kasa, gani yake duk abinda ya faru duk shine silar faruwan haka.
           
         ⏰ Bayan awa biyar na farka daga barcin wahala, mika nayi ina kallon ɗakin da nake kwance.
     Komawa jikin pillow nayi ina fikifiki da idanuna, ɗago su nayi na kalli Yaddiko da ta zuba min idanu. Ba ita kaɗai ba har shima kallona yake, cikin alamun gajiya na tura musu baki nayi cikin shagwaɓa nace.
"Yaddiko wata duniya aka kawo ni."
        "Sannu Shatuwa! Ina ke miki ciwo." Inji Yaddiko.
      Shiru nayi idanuna nakan Sailuba wacce tayi tsuru tsuru, abinda ya farune ya shiga dawo min, na zabga mata harara cikin masifa na mike tare da dafe goshina na zauna nace.
"Wallahi sai na rama, kamar yanda kika hantsilo ni daga sama, nima sai na rama."

             Dirowa nayi daga gadon tare da fincike karin ruwa da gudu nayi kanta, aikuwa ganin zan murkushe masa matarshi da cikinshi ya tare ni, da karfi ya mai dani kan gadon ya koma Ya Mayyern shi na asali.
      "Wallahi kika taɓa min mata da ciki, sai na sake gwara miki kanki kin mutu kowa ya huta, da wannan jarabarkin fitinanniyya kawai." ya faɗa min a tsawace.
     Cikin taurin kai da tsiwa tare da ruwan masifa nace.
   "Wallahi sai narama, dan ita Yar uwarka ce shine zaka bi bayanta, ni kuma bare yar tsintuwa mara galihu, an cuce ni an hanani magana, Yaddiko kina gani ko, an zalince ni babu wanda ya bi min hakkina ba damuwa."
      Juya musu baya nayi tare da sake musu kuka, sosai.
       Kallon Sailuba tayi kafin tace.
"Kukan Yaran Sadika kunyi asara, dama..."
    "Kaii ..Yaddiko!" faɗa a raunanne,
         Cikin masifa nima na juyo nace.
"Kingani ko da idanunki irin kiyayyar da yake min, nagode." dirowa nayi daga gadon, na shige ban ɗaki. Zama nayi a cikin naki fitowa gashi na rufe ina kuka. Yaddiko buga kofar har ta gaji ban buɗe ba.

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now