36

5.7K 641 101
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

    _____________________________
     '''Chaiiiii Jama'a kubar ni huta ma bazai yu ba kowa Y'ar gidan Yadikko Musamman Ummu Adnan  ga Shatuwa nan Nagode''''
    _________________________
 

     Allah kajikan Mahaifiyarmu da na sauran Yan uwa musulmai😭

     _Allah ka bani ikon ganin kowa da daraja da kima kaman yanda ka karrama
ɗ'an Adam👏_
_____________________________
Page.36

       Shiru Mamie tayi tana kallon Bawan da ya kawo mata, gulmar Ya Maheer. Wai khairat tana bibiyarshi murmushi tayi cikin nutsuwa kamar bazata kula ba tace.
       "Karka damu kasanya min ido akanshi, zan san abinyi."
     "Toh Ranki shi daɗe za'ayi haka." a rusune yayi maganar sannan ya mike yabar falon, yana fita ta ɗauki wayarta a hankali ta shiga niman Annur, yana ɗauka cikin nutsuwa tace.
"Kayi ƙoƙarin cusawa Yarinyar nan soyayyarka dan bana son ayi baikonku da wata matsala, kaji ko zan san yansa zanyi da Daddanku dan shi yake goya mata baya."

         Katse kiran tayi cikin nutsuwa tana murmusawa.
       ........ Dafa shi D'ayif yayi cikin nutsuwa yace.
       "Wallahi najiyo wani magana, amma don Allah ka rufa min asiri."
Waigawa yayi yaga bai ga kowa ba sannan yayi mishi raɗa a kunne, tsura mashi manyan idanunwanshi yayi cikin jin mamaki, murmushi yayi sannan yace.
    "Toh ba damuwa."  ya share batun kamar bai damu ba nan kuwa yafi kowa damuwa.
          *****
    Bayan kwana biyu sai da ya tabbatar Khairat tana lambu ya shiga ciki, tare da manna wayarshi a kunne. Hannunshi ɗaya na cikin aljuhun wandonshi yana tafiya yana magana, har ya isa lambu. Tana tsaka da karatu tagansa mikewa tayi tabi bayanshi tare da cewa.
  "Ji mana!"
    Ya cigaba da tafiya kamar ba da shi take ba, da sauri yake tafiya dan har ya kusan ɓace mata ta sake d'aga murya tace.
"Ji mana!"
    Ina cikin wani masifaffen sauri ya fita daga kofar, da gudu ta isa jikin kofar ya tafi babu alamarshi idanunta ne suka cika da kwalla wanda suka samu nasaran saukowa daga ciki, kifa kanta tayi  tare da sake kuka,
Tace.
   "Dame yake takama? Dan ya taimake ni shine zai na wulakantani, toh miye laifina godiya kawai zan mishi fa."
   Tana gama faɗar haka ta juyo da niyyar barin kofar, bazato tayi karo dashi bata san lokacin da tayi baya zata faɗi cikin zafin nama yasanya hannunshi na dama ya riko ƙugunta, dan har ta rufe idanunta akan zata faɗi, a hankali ta buɗe idanunta akanshi hannunta d'aya na kan kirjinshi d'aya na sake a baya a hankali ya d'agota tare da sakar mata murmushi, hararanshi tayi cikin tsiwa tace.
"Me yasa baka bar ni na fad'i ba? Sai wani wulakanci kakewa mutun."
  Tana gama gaya mishi magans tayi gaba abinshi, a bangaren shi dama abinda yake nima kenan, bin bayanta yayi ya tsaya, zama tayi ta d'ago kanta tana kare mishi kallo, kafin ta kauda kanta murguɗa mishi baki tayi irin ya gama bata haushin nan, tace.
"Zaman ma rokonka zanyi ko?"
     Murmushi ya sake mata sannan ya nime guri ya zauna a ranshi yace.
*Duk halin da zan shiga duk Sabida itace babu wata a idanuna sai ita farin cikina haskena duniyata*

     Kura mushi ido tayi har ya kamata kauda kai tayi tana murmusa mashi cikin sakaltacciyar murya tace.
    "Shine kaketa gudu na? Bayan aikin da kayi min kasan..."
     "Shiiishit, karki kuma cewa komi rufe idanunki", kamar yanda yace mata haka tayi a hankali ya mike tare da cafke wuyar katon macijin da ya saɗaɗo ta jikin fulawar da take zaune, fari dashi. Jin abu mai sanyi kamar igiya yasata  bud'e idanunta da sauri takuwa ga labcecce maciji, ragwab ta zuɓe a jikinshi, hannunshi ɗ'aya rike da maciji ɗaya rike da ita, murmushi yayi cikin jin daɗi dan dama aikinshine, kiran D'ayif yayi ya amshi macijin, cikin farin ciki yace.
"Nagode Abokina ka gama min aiki."
        "Haba ba komi yanzun ya zakayi da ita?" D'ayif ya jefa mishi tambaya.
         "Karka damu zuba mana ido kaga yanda wasar zata kayya, dan wannan shine wasa na biyu da zan fara, dan tuni an fara wasan."
      "Amna baka tunanin aka samu akasi a ta b'angaren Gimbiya Nafisatu ko a b'angaren Gimbiya khairat ?." D'ayif yayi masa wannan tambayar

YAR GIDAN YADDIKO🧕Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum