5

5.9K 434 30
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu....

           _A gaskiya Na fahimci yanda kuka sakawa Yar Yaddiko idanu toh kuyi ku gama babu wanda zai ci Hinkafa da Jar Miya_

       

Page....5
   Haɗani yayi da bango ya rikeni sosai, ɗago kai nayi zan ɓare bakina naga yanda ya runtsa idanunshi, har jijjiyar goshinsa sun mike.
     Sake kai saran macijin yayi yana rike dani, a hankali nace.
"Ya Mayyer, sauke ni." buɗe idanunshi da sukayi ja yayi ya hankaɗa can na faɗi ya juya ga macijin wanda yake hankoron kai mishi sara na uku, cikin hikima ya cafke wuyar macijin, dan dai naga ya duka, mikewa yayi yana kallona. Aikuwa na fasa ihu na juya a guje,

    Daure macijin yayi akafar da ya sareshi yafito a hankali. Sai lokacin Naga mutanen gidan sunfito da gudu na ɗanne Yaddiko, ina niman maɓoya tace.
"Lafiya kuwa! Shatuwa?"
      "Yaddiko maciji xai cuna min."
   Rungume ni tayi, zata fara masifa. Ganin halin da yake ciki yasa ta zaro idanunta, tana cewa.
"Kaiii ku kaishi asibiti mana."

  A gigice Hafsat da Ammar sukayi kanshi,, da sauri Najib ya janyo mota har inda yake, ya shiga ya xauna.

   Da gudu najib suka fita  tare da Ammar,suka nufi asibitin bauchi.
         Nikam ina nasan mike faruwa, part ɗin Yaddiko muka nufa da ita, na shige falonta wanda girmanci yayi wani ɗaki biyu. Sai manyan kujeru ga manyan labulaye, tsakiyar an sanya wani jar kafet,
       "Yaddikooooooo"
A kiɗime tazo, tace.
"Yar lafiya."
   " Yaseen wannan jar abar tsarkiyar tsoro yake bani."
Na nuna mata kafet, tsaki tayi tace.
"Ga ɗakinki can, ki shiga. Akwai komi a ciki."
   Ta juya tabar ni a gurin hankalinta yana kan Mayyer, taɓe bakina nayi bayan na kumburashi na shige ɗakin.

          Da gadona ɗan karami, komi nawa dai daini ne,
      ........A can asibiti kuwa anyi sa'a dake ɗhyaje da macijin take aka duba ruwan alluran dafin kalar macijin, aka mishi sannan suka cire a hakoran macijin, suna mishi dariya.

        Ban ɗakin na shiga na karewa ko ina kallo, kafin na shikawa Yaddiko kira.
     “Yaddikooooo"
  Da sauri tashigo ban ɗakin kallonta nayi ina murmushi nace.
"Kahi zanyi."
    Shiru tayi sannan tafita can sai gasu tare da Hafsat, bayani hafsat tayi min yanda zanyi amfani da komi, ta kai hannunta gashina da na sake shi a kafaɗana.
     
         Koda nagama abuna na wanke na kuma buɗe masa ruwa na kura mishi ido,(😂 Sowiee banyi dan na ɓatawa wani rai ba)
             Tsuka nayi nace.
"Hima kahin sai an kai hi, inda zai zauna."
    Bahun wanka na cika ruwa na shiga ciki na zauna, can na sake kwallawa Yaddiko kira, tana shigowa nace.
        "Yaddikona ki min wankar mana."
   Soso na taje ta ɗauko min, sannan tazo ta saɓeni, sam ban lura da damuwarta ba, itama kuma bata damu da nasani ba, tana gama min wankar na fito nasaka kayana, na fito falon na zauna ganin nafito ta kama hannuna ta kaini cikin gida, gurin Mahaifiyar Mayyer mace mai kirki da sanin ya kamata. Tana gani na tace.
"Aishatu ce ta girma haka Yaddiko?"
      "Eh itace Safiya, Ya jikin yaron nan hankalina yaki kwanciya."
      Duba wayar hannunta Mamansu Maheer tayi cikin murmushi tace.
"Yaddiko da sauki fa tayu zuwa gobe ma su sallame shi, ai yaje musu da macijin kuma an sami maganin gubar."
    Shiru Yaddiko tayi, amma zuciyarta ba haka yaso ba.
     Abinci aka kawo mana, tuwon shinkafa miyar ganye, murmushi nayi nace.
"Yaddiko ga abinci nan, ni ba yanzun zanci ba."
       D'aukar abincin akayi zuwa gidanmu, nan Mamansu Maheer kejana da hira, har nasake da ita nuna min ɗakin Hafsat tayi na shige, sannan tace.
"Yaddiko ko zan kaiki ki ga halin da yake cikine."
     Ajiyar zuciya tayi tace.
"Haka yafi."
   Mikewa Yaddiko tayi tasaka hijab ɗinta Mama kuma ta shiga ɗaki ta ɗauko key mota, tace.
Mufito.
      Haka muka nufi asibiti, sai kale kale nake, mun same shi yana zaune suna hira da Ya Najib.
           Muna haɗa idanun shi ya zabga min harara, ni kuwa na koma jikin Ya Najib na murguɗa mishi baki.
      Lumshe idanunshi yayi, kaman yanda yasaba, idan na bashi haushi. Kowa ya gaishe ni ni kuwa na koma jikin Ya Najib ina mita.
"Ya Najib hine ka tahi kabarni? Ni ɗaya na."
   Nuna min gadon Maheer yace.
"Baki gaidashi." ya faɗa min tare da tsare ni da ido.
   Kwal kwal nayi da idanuna ina kallonshi nace.
   "Ince muna higowa ya harareni."
     "Toh tunda haka ne babu ruwa na dake, daga yau mun daina abota."
  Juyawa nayi cikin kuka nace.
  "Ya jiki?"
      Basar dani yayi, kamar bai ji me nace mishi ba, sai da Mama tace.
"Bana son wulakanci tace maka ya jiki kayi banzada ita."
    Taɓe baki Yaddiko tayi cike da takaici tace.
"Zan sami Iro ya shiga tsakanin shatu da Mahar. Dan kiyayyar tayi yawa."
         "Kiyi hakuri Yaddiko nima zan tsawatar mishi."

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now