44

9K 570 80
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAK'A WRITER'S ASSO*

Mai_Dambu
*Watpad:Mai_Dambu*

_Kyauta ga Masoyan Asali_😘💃🏼

Alhamdulillah........

Page.44
A hankalin Mamah a tashe ta zauna akan kujeran mirorr tana kare mata kallo ta sake tambayarta da cewa.
"Lafiiya binta? Kike kuka haka.?"
"Mamah tausayin Humaira nake ko shekara ɗaya batayi ba, kuma ga."
Shiru tayi kanta a sunkuye, mikewa Mamah tayi ta ɗauki humaira ta fita da ita tana zuwa palour tace.
"Ammar ka haɗu min kayan Aisha ka kawo min Allah ya raba lafiya."

Ƙurawa Mamah ido yayi yana jiran karin bayani, tayi waje da yar tana faɗin.
"Sakara matarka cikine da ita."
"Eeeeeeeeewuwuu, Wallahi nima na zama Abba." wancakalar da kaya hannunshi yayi,ya shige dakin a guje, tsayawa yayi akanta yana murmushi yace.
" Dagaske kina da cikin?".
Hararar shi tayi cike da masifa tace
"Ka amso min Y'ata nikan zubda cikin zanyi dan sai..."
Tsabar ɓacin rai bai san lokacin da ya shaketa ba, jikinshi na rawa, yace.
"Butula kawai wacce bata san halacci ba, idan kin fasa zubda cikin ke ba y'ar halak bace wawuya shashasha, mara kan gado."
Cillata yayi yabar ɗakin, kuka tasaka me cike da tashin hankali.
......Tun daga ranar Ammar ya shiga gasa, babu wanda yasan da halin da suke ciki sai ita da take ta lalacewa. Shi kuwa kaura cewa duk wani abinda zai haɗa shi da ita yayi dan yana matuƙar azbtuwa da halin da suke ciki.

*****
Kwana biyu tsaƙan Dadda ya gabatar da Ya Maheer a ciki masarautar shehun barno. Sannan aka saka bikin tarewa na nan da sati uku.

Washi garin da aka gabatar dashi ya bar garin bayan mun kashe arna ba iyaka, kafin ya tafi ya roki Dadda ya dawo da Mamie toh kawai yace mishi.
****
Yo Mamie ita a tunaninta Dadda zai janye da zaran ta faɗawa Modibbo abinda yake faruwa, tasan kuma zasu goyi bayanta, murmushi Modibbo yayi sannan yace.
"Tsakaninki da Allah zaki iya tsayawa Maciji ya sareki dan kina kaunar Yarki ta rayu? Ko zaki iya artabu da aljanu dan kawai ki cirota daga matsalarsu?"
Girgiza kai tayi sannan ya cigaba da cewa.
"Kinga ko iyayenshi sun girmama kaunar da yake mata, me yasa ke bazaki kauna ce shi ba, mutumin da yaso ɗanka ya gama maka kome fa Nafi, amma tunda kin zaɓe zaman gida bismillah akwai kome a gidan, amma kisani mutuncinki kike zubdawa a idanun Mijin yarki."

Shiru tayi har ya gama maganarshi batace ƙala ba.
Karshe mikewa tayi tabar falon, kwananta biyu ta shirya zuwa ganin kakanta, koda taje ta same shi da baƙon bafulatani, gaishesu tayi sannan ta shiga gidan.
"Malam kana ganin abinda na gani kuwa? Jikarka ce ɗauke da damuwa."
A jiyar zuciya kakan Mamie yayi yace.
"Na gani, nima sai dai mu tayata da addu'a."
Allon karfe mutumin yace kakan Mamie ya bashi take ya zauna ya shiga rubutu.
Yana gamawa yace a wanke a jefa gaushi a cikin ruwan rubutun, a bata tasha yanzun nan.
Kamar yanda yace aka kakanMamie ya umarta aka kuwa bata tasha, tunda tasha ta fara tari da atishawa, karshe da mingira da barci.
****
Ya Maheer ya isa bauchi lafiya, murna a gurin Yadikƙo ba'a cewa kome, zama yayi yana bata labarina.
Da dare ya gabatar musu da sakon Dadda, farin cikin da kowa ya shiga ba'a cewa kome.
Koda ya shiga part ɗinshi, ya same sailuba a birkice. Mamaki yasha amma dan a zauna lafiya yayi kokarin sauke mata hakkinta.

****
A cikin sati biyu aka haɗa kayan aure aka kai, Dadda na gani Yakira Ya Maheer yace.
"My son me yasa baka ji kaima Mamienku ta koya maka halinta ko."
"Kayi hakuri Dadda, ya batun Mamienmu?"
Murmushi Dadda yayi ranshi na kara yin fari yace.
"Cikin week ɗin nan zan dawo da ita dan bana son a kawo mata ƙishiyoyinta bata nan"

Yayımlanan bölümlerin sonuna geldiniz.

⏰ Son güncelleme: Nov 04, 2019 ⏰

Yeni bölümlerden haberdar olmak için bu hikayeyi Kütüphanenize ekleyin!

YAR GIDAN YADDIKO🧕Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin