20

5.3K 468 54
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*

Page.20
        Kallonta nayi cike da tausayi sannan na girgiza mata kai nace.
"Banzo dan na cutar daku ba, nagode da tarɓan da kuka min."
   Mik'ewa nayi zan bar gurin tace.
"Zauna"
        Zama nayi tare da fashewa da kuka na rike kaina, nace.
"Yaddiko tace min butulu, shima yace min muguwa, sun koreni daga rayuwarsu. Kuma dama nice matsalarsu, na fita a cikinsu zanyi rayuwa ni ɗaya na xan zauna, dole ma su koreni tunda taurin kaina yaja min, da rashin haƙurina da nayi haƙuri da abinda tayi min da haka bai faru ba, ni fa bansa cikin zai sami matsala ba."
     Juyawa nayi gareta cikin kuka nace.
"Allah ni muguwa, gashi nayi kisan kai. Ko koreni ma kawai na tafi."
         Rike hannuna tayi tace.
"Faɗa min gaskiya mi yafaru kika rabu dasu?"
      Girgiza kai nayi cikin kuka nace.
"Idan na faɗa miki korata zakiyi"
      "Eh toh, koda zan koreki sai nayi nazari."
         Tace min.
      A hankali na faɗa mata abinda ya faru, kallona tayi fuskarta a murtuke, tace.
"Ummi Aisha baki kyauta ba, wannan abinda kikayi ba halin musulmin kwarai bane, karki kuma aikata haka. Ya sunan asibitin da suke muje na dubata."
       Zaro ido nayi nace.
"Nifa bani zuwa ko ina kawai zanje niman dangina ne, idan nasamesu zan koma garesu, tsoro nake ji kar ta mutu, kuma nasan Ya Maheer bazai taɓa yafe min ba."
        "Ai ba dake zamu ba, nima zani ganin likitane, dan na wucce Edd na."
             Tausayi tabani na kalli tikeken cikinta, na sake murmushi nace.
"Kuma baya miki nauyi."
          Dariya tayi ta shafa cikin a nutse tace.
"Ba sosai ba, kema wata rana zaki haka ɗauki naki."
   Kunyace ta kamani na rufe fuskana ina dariya.
         Mikewa nayi na tattara kayan abincin da muka ci.

           Mik'ewa tayi dakyar ta biyo bayana, dan ganin ta inda zan kai kwanikan.
        "Ummi Aisha ga kitchen ɗin nan." ta nuna min  dan har na wucce.
         Tana shiga nabi bayanta, na zuba a cikin gurin wankewa. Buɗe musu ruwa nayi ina ɗauraye su sannan na wanke su tass, ta nuna min inda zan kifasu.
           Kayan girki tafitar tare da nuna min abinda zan mata dasu, a hankali na shiga mata yanda tace, amma dake ban iya aikin ba sai da tabi wasu abubuwan.
     "Ummi Aisha! Kakarki ta miki mugun goyo, yanzun kamarki baki iya komi ba. Sai an koya miki, kina gani na a nan degree biyu gare ni ɗaya a fannin girki ɗaya a fannin tattalin arzikin kasa, dan nayi hakane dan na burge mijina, kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Dan yanzun na saye zuciyar mijina, zaki zauna dani sabida ki koyi yanda ake zamantakewar rayuwa ne, sannan zaki koma makaranta. Sai dai ba'a nan ba dan ina tunanin komawa gida zamuyi, sai abinda Dadda yace tukun."
     Kunya ce takamani,  ganin duk inda zanyi da hijab tace min nacire. Dole na cire muka cigaba da aikin har muka kammala abincin rana, tazuba a cikin wasu warms aka saka a basket.
      Tabawa Sarkin gida ya kaiwa Mijinta, inda muka ɓata tace na goge dukda baiwa tazo tace taje ni zan gyara komi. Aikuwa haka na gyara ko nace na ajiye komi da gindinshi.
           Murmushi tayi sannan tace.
"Da aiki a gabanki, muje na duba miki kayan da zaki sauya kafin Annur ya dawo kuje kusayo."
            ****
Koda Ya Maheer ya isa asibitin yasameta a kwance tana kuka, zama yayi a kujeran dake gabanta ya riko hannunta, kwace hannunta tayi tace.
"Wato ta nemi kashe ni, baka damu ba shine katafi kabarni a cikin mugun yanayi na mutu ko nayi rai nice keda asara ba kai ba."
             Tsura mata ido yayi cikin rarrashi yace.
"Toh ba gani ba, ai sai a wucce gurin tunda nazo."
          "Wato bazaka ce min nayi hakuri ba." ta faɗa cikin kuka,
    Galla mata harara yayi yace.
"Karkiyi hakuri don Allah, kinsamu ma nazo ina lallaɓaki da wanne zanji da halin da Yaddiko take cikine koda na ɓatar Yar mutane dake ku mata kullum brain ɗinku a cushe yake da kishi kina zaman jirana, ki nitsu cikin yasamu zama idan kika ɗaga hankalinki toh ki sani kece da asara."
   Yana gama faɗar haka ya fita abinshi.
            Shiru tayi tana mai jin zafinshi gefe guda kuwa farin ciki take, *madalla da ta ɓata Allah yasa kar a sameta."
              ........Daga asibitin gida ya dawo ya sauya kaya yafita nimana ko za'a dace, amma haka ya gama kewayawa cikin gari ko mai kama dani bai samu ba.
      Dawowa yayi ya sami Yaddiko jikin dai dole su dangana da asibiti.
            Kiran Mama yayi suka gaisa, sai yayi shiru.
            "Maheer! akwai matsala ne?."
         Ta tambaye shi a takaice,
         Inda inda ya shiga mata, csn da yaga ta hasala ya fito ya faɗa mata gaskiyar abinda ya faru.
             "Madalla kunyiwa kanku, wato dan bata da galihu kuka ci zarafinta kai da kakarka, ita da aka hantsilota daga sama ba Y'a bace, sannan kai da kanka kake kiranta jaka muguwa, Insha Allah duk inda take tana hannu nagari. Kai da zaka gina zuciyarta da sonka shine ka kara rura wutar kiyayyarka a ranta, ka ajiye wannan maganar ka rasata kenan har abada. Kuma bana maka fatar samunta dan baka san darajar mutum ba, Yarinyar da take cike da haukar balaga, ga kuma mutanen boyen da suƙe bibiyarta shine ka mata wulakanci ka kori Yarinya karama da igiyar aurenka akanta, ina zata? baka tunanin a taɓa mutuncin aurenka ne? Nan ɗin bauchine aka ce maka toh wallahi wani abu ya taɓa Rayuwarta ban yafe maka, kasan xaka wulakantata kasa aka baka aurenta tun bata shiga scndry ba, dan munafunci har da ajiye karatunka kayi kazo ka tare mana dan abaka aurenta, an baka wato kasami abinda kake bukata a gurinta Allah Ubangiji yasa baka lika mata cikinka ba balle tasha azabar rayuwa."
     D'ifff ta kashe kiran ranta na zafi.

       Dafe kanshi yayi hankalinshi inyayi dubu ya tashi sai yanzun ya gano kuskuren da ya tafka na korana, da aurenshi.
        ........
       Koda Annur ya dawo asibiti suka je da Mamie ina gida, sun sami sailuba lafiyarta lau, sai ɗan abinda baza'a rasa ba.
       Gaisheta sukayi. Sannan Mamie taga likita suka dawo gida, nan mamie ta faɗawa Annur ya kaini nasayi kaya.
         Murmushi yayi ya wucce ɗaƙinshi, yayi wanka tare da sauya kayanshi, sannan yafito gurin cin abinci.
   Yana gama ci ya kwankwasa min kofa, fitowa nayi nace.
"Barka da dawowa."
    Jingina yayi tare da lumshe idanunshe idanunshi yace.
"Ummi Aisha! Yawwa idan kin gama zamu iya tafiya mall."
               "Toh" nace mishi,
         Juyawa yayi na fito tare da jan kofar ɗakin.
            Mika mishi card yayi bata kalleshi ba, dan sai ya iya kin karɓa.
        Dauka yayi yace.
"Aunty Mun tafi."
       "Humm" kawai tace mana.
      ........
      Kimanin kwana goma kenan da ɓata na, dan har an sallami Sailuba. Ya Maheer ya koma kamar mahaukaci, dan dole ya haɗa alamarin da Yan sanda nan suma suka gama nasu ba'a same ni ba.

               Karshe a cikin sati uku ya mai da Yaddiko da Sailuba yayi gida shi ya cigaba da aikinshi yana kuma nimana.
                 
              ........ Ranar da na cika wata gudu, ranar aka kai Mamie asibiti cikin dare, Khairat da Mubina sun koma sai ni ɗaya da Ya Annur wanda tafiyarmu tazo ɗaya.
                  Cikin dare suka tafi ban sani ba, ina can ina barci musaman yanzun da nasami Ya Annur ya cire mim kewar wancan masifaffen, Mamie kuma ta cire min na Yaddiko.
                  Bayan nayi sallar asuba na koma na kwanta, can naji hayaniya a gidan. Mikewa nayi na fito sanye nake da doguwar riga sakar behairin, sai hullar da nasaka.
              Kallon babyn nayi cike da mamaki nazo gurinsu nace.
"Har sun zo duniya, yaushe kuka zo? Mamie yaushe kika haifesu."
      Basu da niyyar dariya amma sai da sukayi sabida wautar da nayi, kallon jakadiya nayi yanda take shafe ɗaya babyn da lalle, sai nishi yake. Kamar zanyi kuka sabida kaunar yaran nace.
"Jakadiya don Allah kibishi a hankali, kinga sai nishi yake, haba da wanne zai ji da nishi ko da maka mishi lallen da kike."
     Kallona tayi cike da mamaki yaushe nazo gidan da zan mata isa da gadara, ɗago kaina nayi muka kalli juna gyad'a kanta tayi tace.
"Toh angama ranki shi daɗe."
      A hankali ta cigaba da aikinta tanayi tana kallon Mamie da Dadda wanda ya kasa ya tsare, bayan ta gama na yaron aka ɗauko ɗayar aka warwareta, kallon fuskar yarinyar tayi ta kalle ni.
       "Allah mai yanda Yaso, Fulano kiga wannan Yarinyar sak khadijarki lokacin tana jinjira."
     Sannan ta dire idanunta kaina, murmushi nayi nace.
"Ai mamie tace Sister khadija baka ce, ƙinga kuma wannan fara ce irin Mamie ko Mamie."
   Na kalleta. Gyɗa min kai tayi ina zaune har aka gama musu wanka aka shiryasu tsaf, aka kaisu ɗakin Mamie.
                Tun daga ranar nima na tare a ɗakinta, ko kuka suke nima zama nake na tayasu Dadda kuwa ya zauna yayita dariya wai nafisu son babyns.

          Kwana uku da haihuwar, ina barci a ɗakin Mamie na ɗanne kusada Yaran nayi kanekane zakusha mamakin yanda mamie ta sake min, ainun ni kaina mamaki nake. Kuma bansan mi yasa bs kodan Yaddiko ta shagwaɓa ni ne yasa bana rena abin kuka, dan Ya Annur shima ya fahimci ni ɗin muguwar sangartacciya ce, har masu gidan da ma'aikatansu.
      Cikin barci nake jin busar algaita, nasaba jinshi a bauchi amma na yau dukar zuciyata yake da ruhina, jikina rawa yake a hankali na mike ina jin busar na shiga jikina.
               Dadda ne ya yashigo ɗakin ganin yanda jikina ke ɓari da kerrma yazo yayi maza yarike ni tare da zaunar dani, yana kallon fuskana wanda yake tsatsafo da gumi, ga idanuna a rufe jikina bai fasa rawa ba. Shigowar Mamie tayi turuss tana kallon yanda nake kerrma. Zams tayi suka sani a tsakiya tare da rike hannuna.
           Ana barin busar jikina yabar rawa, kuka nasaka mai mugun ban tausayi nace.
"Wacece Ni......."
     Daga Alkalamin Yar mutan bauchi..........

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now