31

5.4K 740 70
                                    

*YAR GIDAN YADDIKO*

*HAZAƘA WRITER'S ASSO*
Mai_Dambu....
*Wattpad:Mai_Dambu*
*_Shafin nakune Ummyn Yusra Fans grp musaman Ummun Sayeed, Mr Muhamud, Hauwa tanko ga kyautarku nan_*
         '''Zama da masani yafi zama da lusari, wannan jinjinarku ce Mommyn Sayeed nd Noor, tare da Ummu Leenah naji daɗin Muhawaranku musaman yanda kuka fito da ra'ayin Mazahabobi, Akan sakin da Ya Mayye yayi labtawa Kawata Nagode sosai a ciki gaba da gashi'''
   
        _Sarauniyar Yan comments Aysha Aliyu na zumunta wannan shafin tukwaicinki ne ke ɗaya amma dai toh ba'a san maci tuwo ba sai miya ta kare nagode_
Page.31
       Bin bayana yayi da kallo har na shige, sannan ya mai da kanshi ga tv dake falon. Shafa kanshi yayi.
    "Yarona! Yaushe ka shigo sudan?" Aunty Zaituna ta tambayesh.
       Gyara zamanshi yayi cikin nutsuwa yace.
"Ammina! Jiya na shigo, mun sami hutu a gurin aiki dole na gudo gida."
      Masu hidiman gidan ne suƙa shiga jera mishi kayan abinci a gabanshi.
       ....
    Dariya Buhaina take min har da rike cikinta kallon kaina nayi nasake kallo nace.
"Miye kikewa dariya?"
          "Oho toh naga kawai jikinki na rawa ne, daga ganin handsome guy. Prince Izzudeen." ta faɗa min,
        Bansan lokacin da bakina ya suɓuce ba nace mata,
"Ina handsome a gurin, Mr Perfect nd classic,gentleman babu irin Dr Maheer gum...."
             Kuruuu tayi min da ido tana mamakina dan tasha min maganar shi ina balbaleta yau kuma nice mata zan mata Allah ya isa, idan ta kuma kiran sunanshi.
        "My Dear! Kina son mijinki har yanzun mi yasa yayi miki haka." ta tambayeni,
    Haushin da takaici ne ya kamani, na taɓe bakina  tare da ɗaga kafadata nace.
"Oho shi yasani, duk mazan halinsu ɗ'aya dan matuƙar kika shigo da rayuwarsu sune zasu juya miki taki rayuwar upsitdown."
   Ina faɗar haka na cire gown ɗin jikina na ɗaura towel, zan shiga ban d'aki ,Tace.
          "Dear sis, Ina hango miki ranar da zaki faɗa hannun Mr Perfect ɗinki. Dan naga alamun wahala, mace sai uban tsayi babu shif."
         Juyawa cikin masifa, dan nayi imani ni banda jiki sosai sai tsayi amma karya ka kalleni kace ban isa mace ba, dan ina da kirji da k'ugu.
       Sake towel ɗin nayi naje gaban mirror nace.
"Kalleni da kyau, ba dukka bane suke da irin tsarina, na fito cikin kabila biyu Kanuri nd Fulani."
     Jan bam ɗin gashina nayi nace.
"Ko ke da Abbunku yake balarabe, sai dai ki nuna min, hasken fata. Yarinya nasan nan gaba, sai na haɗa crush akaina dan ina jin haka a jikina, Yar kwal uba. Ni matar Mutum ɗ'aya ce bawan da ya bautawa jikin da mai jiki...."
      "Mr Gentleman ba?"
   Tsaki nayi na ɗauki zanina na faɗa banyi.
   Dariya ta bini dashi har da rike cikinta, ba karya Buhaina tana sona da Ya Maheer, tunda na bata labarin da Umma ta fada min, ta daina jin zafinshi, asalima sai ce min take bata tunanin shi yasake ni.

             ........ Sosai Izzudeen ya shigo rayuwata, a hankali na gano wani ɓoyayyen halinshi na niman mata, wani hidima ake a cikin gidan sarautan dan mahaifinshine sarkin sudan, dake anyi dinner da dare  na tashi zan je fitsari na hangoshi da wata cousin sister ɗinshi kamar zasu cinye kansu.
           Komawa inda na fito nayi, haka kawai Ya Maheer ya shiga dawo min dukda yakin da nake da zuciyata amma ina.
            ......Kafin Izzudeen ya koma yayiwa Aunty Zaituna magana, ita kuma da azarɓaɓɓi ta kira Dadda ta faɗa mishi, kai tsaye shi bazai min dole ba idan ina son shu shi knn.
   Koda tayi min magana nace mata ni bana da lokacin soyayya karatu ya kawo ni.
              ****
  Bayan gama wankar sarautar Daddane suka keɓe da sarkin bauchi akan matsalar da ya faru nida Ya Maheer, anan Dadda ke nunawa Sarki Abdullahi Yakubu na uku, cewa.
"Maganar gaskiya nafi sonta da Yaron, wallahi banso ya rabu da ita ba. Dan naji komi a gurin kakar yaron da irin sonda yake mata, sannan abin mamaki shine rashin tuntuɓar mu da iyayenshi basuyi ba, mutumin da ya kwanta jinya sabida itane zai saketa har uku."
       Gyara kishingiɗa Sarkin bauchi yayi tare da murmusawa yace.
"Zan tuntuɓe iyayen yaron muji daga garesu nima dai banso haka ba."

     Haka sukayita tattaunawa har washi gari da sarkin bauchi zai koma sukasake maganar.
         *****
       Lokacin da nabar kofar ɗakin, juyawa Ya Najib yayi ya biyo bayana har na bar asibitin.  Tari yake har da  jini, ta hanci da ta baki.
              A cikin lokaci kalilan ya yanki jiki ya faɗi a gurin, masu aikin shara ne sukayi ihu akazo aka wuce dashi ICU.
             ****
     Koda sarkin Bauchi ya dawo bai nime su Abba ba sai bayan sati guda ya tura musu da sako lokacin Ana kokarin fitar da Ya Najib India, dan nashi matsalar tafi ta Ya Maheer.
         Ummanshi haukacewa ne batayi ba amma alal haƙiƙa tana cikin tashin hankali.
          *****

      A hankali muka fito daga ajinmu zuwa inda za'a ɗaukemu dukkanmu sanye da kayan makaranta dafa kafaɗana Buhaina tayi, tace.
"My Dear! Kinsan wani abu?"
   Girgiza mata kai nayi tare da kallonta.
     "Wallahi ina son Ya Izzudeen, amma shi kuma ke yake so."
          Cike da mamaki na kalleta, sannan nace mata.
"Don Allah da gaske kike ko da wasa?"
          Girgiza kai tayi kwalla ya zubo mata, tace.
"Am not joking."
          "Kin same shi, Yarinya dan ni dai bana sonshi." na faɗa mata kai tsaye.
          Har muka dawo gida shawara muke bawa junanmu, tare da karfafawa kanmu.
                Kiran Wayar Ammi Izzudeen yayi ta mika min.
    Karawa nayi a kunnena nace.
"Aslm"
           Can naji muryanshi a tausashe, yace min.
"Wlsm, Khadija ina ta binki kina min wasa da hankali miye lafiya."

           "Gaskiya baka da laifi asalima, ina ganin ƙoƙarinka ma gurin maƙalewa matar Wani."
     Sai da na faɗi haka ne na dafe bakina sabida yanda matar wanin yayi fitowar bazata,
           "Well! Amma ai ance min kun rabu da wanin ko?"
      "Wannan ba matsalarka bace, sai anjima."
    "Pls karki katse wayata, ina sonki sosai khadija."
       "Ayya sowiee ni kuma ina da wanda zuciyata ta baiwa a jiyan shi, wanda ya sadaukar da rayuwarshi domin ni..."
         "Amma dai kinsan babu aure a tsakaninku, dole sai kinyi wani auren kafin ki koma mishi, indau ni kika aura bazan barki ki fita daga hannuna ba."
           Murmushi nayi wanda bansan lokacin da nayi shi ba. Nace.
"Toh ai bazan ma aureka ba, dan ni Rayuwata da karankaina mallakinshi ce, babu wanda ya isa shiga inda ya gina domin kanshi bye."
  Na katse kiran ina jin haushin kaina, yanda zƴciyata ke min shishigi , tsaki yayita ja yafi sau ɗari.

     Maida mata wayar nayi, nace mun gama hiran, na gudu zuwa ɗakinmu dan karta tambayeni.
    Munafuki ashe bayan kai mata wayar da nayi yasake kiranta kamar zaiyi kuka wai shi fa zai iya mutuwa idan nace bana sonshi nan ya labarta mata abubuwan da muka tattauna.

          D'akin ta shigo tayi min masifa, tunda nace mata tayi hakuri ni bana sonshi dama,

        Taje ta kira Mamie ta faɗa mata, nan naga bubun masifa dan mamie kamar ta antayo ta wayar ta yagalgalani. Domin kawo karshen rigimar nace.
"Wallahi Mamie bana sonshi, Asalima Buhaina ce ke sonshi na rantse miki da Allah."
      Shiru tayi sannan tace.
"Kin tabbatar dagske ita ce ke sonshi."
     Narke mata nayi cikin sakalci nace.
"Eh Mamie."
"Ok kai mata wayar."
    Fita nayi na mika mata wayar, bansan ya suka kare ba karshe dai naga Yayar Dadda fuskarta ya cika da farin ciki.
      Oho can da yawarsu na rabu da ƙaya.
           Bayan kwana biyu naga Buhaina tayi replace ɗina ita ke waya da Izzudeen, nace aƙare lafiya.
             *****
   Lokacin da wakilin sarki yaje gurinsu Abban Ya Maheer ya samu, dan haka ba ɓata lokaci ya bi bayan Ɗ'an aikan.
              Cikin karramawa aka amshi Abban Ya Maheer dan wani farlou na daban aka kaishi, inda ya sami sarkin a can.
             Bayan gaishe gaishe, nan mai martaba yake faɗa mishi abinda ya faru har da copy wasikar da aka kaiyi copy ɗinshi.  A kiɗime Abba ya mike cikin tashin hankali yace.
"Ranka shi daɗe, wallahi wannan ba aikinshi bane asalima yana can kwance. Cikin halin rayuwa da mutuwa Innalillahi... Wannan wacce irin masifa ce haka ga ɗan kanina shima gobe za'a fitar dashi zuwa india."

   Shiru mai martaba yayi yana mamakin wannan alamarin.
            Karshe dai haka Abba yabar fada da takardan sakin dan ya tabbatar.
              ****
   "Najibullah ummanka ce take zaune don Allah karka tafi kabarta mi kake ɓoye mata."
   Inji Umman Ya Najib, abin tausayi. Buɗe fararren idanunshi yayi cikin raunanniyar murya yace.
"Ummi Aisha! Amma nasan bazan taɓa samunta b..."

Tari ne ya kara turnike shi, jini na fita ta hancinshi. Murmushi yayi fuskarshi tayi fayau.......

Karku manta da:Vote nd FollowMai_Dambu

YAR GIDAN YADDIKO🧕Where stories live. Discover now